Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Kafuwar Daular Zazzau (4)

by
4 years ago
in ADABI
7 min read
Tarihin Kafuwar Daular Zazzau (2)
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Cigaba daga makon jiya

 

Yadda Jihadin Fulani Ya Kasan Ce A Daular Zazzau

Labarai Masu Nasaba

Yadda Aka Fitar Da Sakamakon Gasar Rubutun  Hikaya, Na Diyan Gobir

Ta Hanyar Karance-karance Mutum Yakan Zama Marubuci, In ji Fatima Muktar Gombe

Saɓanin jihadin fulani daya auku a kano wajajen shekara ta 1803-1804, jihadi a daular Zazzau bai auku ba a sai a wajajen shekara ta 1808.

Dalilin haka shi ne karbar kiran limamin yakin Jihadi, watau shehu Usmanu dan fodio da sarkin daular Zazzau Isyaku Jatau yayi a zamanin rayuwar sa.

Sarki Jatau ya aikewa shehu Usmanu sakon mubaya’ar sa a lokacin da Shehun yayi hijira zuwa Gudu. Haka kuma ya aikewa malamai masu yakin jihadi a kano bukatar aiko malami gareshi wanda zai koyar dasu addini, inda akace jakadun sarkin sun hadu da malaman jihadin kano a gundumar Karaye, har kuma suka aike da Mallam Dan Zabuwa da wasu mutane gareshi.

Daga baya mallam Danzabuwa ya fada ga malaman jihadi cewar sanda ya riski fadar Zazzau, ya taras da Sarki Jatau abisa karagar mulki, sanye akansa rawani ne na mabiya sunni da Shehu Usmanu ya kawo sabanin rawanin haɓe da sarakunan hausawa ke sanyawa kafin zuwan Shehu.

Sai dai wannan abu ya tayar da kura a Zazzau.

Mutane da yawa basu ji dadin yadda sarki Jatau ya bijirewa al’adun daya gada ba ya koma kan abinda shehu yazo dashi. Haka kuma yadda yasa aka rushe wurin bautar Iskokai tare da maishesu Masallatai yayiwa mutanen Zazzau ciwo, ciki harda manyan fadawa masu fada aji ga Sarki.

Akan haka akace wasu kusoshi a daular irinsu Magajiya, da Iya da Shebagu, da Wagu suka rinka hada kan mutane domin yiwa sarkin bore ko kuma a tilasta masa komawa tsohuwar al’ada, amma sarkin sam yaki biye musu.

Ana haka sai sarkin ya gushe, masu zaben sarki suka hadu akan dora dansa Makau amma bisa sharadai guda uku.

Na daya akace masa dole ya karya duk wata yarjejeniya da mahaifinsa Jatau yayi da Tubake, watau musulmai mabiya koyarwar shehu Usmanu dan fodio.

Na biyu dole ya hukunta wadanda suka dora sarki Jatau bisa wannan tafarki na bijerewa abinda kaka da kakanninsu sukeyi a Zazzau musamman limamin Kona da Limamin Juma.

Na uku dole ya rushe masallatai da Sarki Jatau yayi, ya maishesu wurin bautar Iskokai kamar yadda suke a baya.

Ai kuwa da hawan sarki Makau mulkin Zazzau, abinda ya soma kokarin cikawa kenan.

Akan haka yasa aka rushe masallatai har dana Jumu’a, aka maishesu wuraren bautar Iskokai.

Sannan yasa aka kama Liman Mallam Muhammadu Lawal aka daure a fadan-fadan, daga baya aka kashe shi. Shikuwa daya limanin Mallam Hamidu mai Jan Rago sai ya gudu ya tsira da ransa.

ADVERTISEMENT

Koda labarun Wadannan abubuwa suka riski Shehu Usmanu, sai ya hada tawagar mabiyansa karkashin Mallam Musa ya turo su Zazzau domin suyi yakin jihadi anan..

A cikin wadanda zasu taimaka masa akwai Mallam Yamusa, da Mallam Abdulkarim, da Mallam Abdulsalam wadanda dukkansu sai da sukayi sarautar Zazzau bayan sun samu nasarar karbe iko da ita.

Sai kuma malamai irinsu Mallam Usmanu Sabulu bahaushen kano wanda ya zamo Katukan Zazzau, da Dokaji bafullatani da akayiwa sarautar Galadima, da Mallam Hamma bahaushen kano da akayiwa Dallatun Zazzau, da Mallam Gabdo bafullatanin ‘Yandoto daya zamo limamin Zazzau na farko bayan Jigadi.

Sauran kuma mutane ne mabiya shehu Usmanu da suka fito daga wurare daban-daban, misalin Tofa, Yandoto, Borno, Katsinawa, Barnawa, Dan Dorori, Yeskwa, Joli, Gadidi, Bebeji da Zariya.

Sai dai tun kafin isowarsu har labari ya iske sarki Makau. Don haka ya tara dakaru masu dumbin yawa, ya aike da wasu kimanin dubu ashirin Hunkuyi domin tarar masu jihadi da dai-daitasu.

Ai kuwa dai, an gwabza fada da Masu jihadi a garuruwan Hunkuyi da Kudan har kuma an kusa cin galaba akansu, amma cikin ikon Allah sai suka samu taimako daga wasu sarakunan mulki na yankunan.

Mutum na farko daya basu taimako shine dagacin Kauyen Durum, wanda ya kuɓutar dadu daga dakarun Makau.

Na biyu kuma shine sarkin Fawan Likoro daya labarta musu yawan adadin dakarun dake gabansu a Hunkuyi. Don Haka sai suka yanke shawarar kauracewa yakin fito na fito, suka sulale ta Kudaru suka shige birnin Zariya ta kofar Bai ba tare da kowa ya sani ba.

Wasu sunce Sarki Makau da mabiyansa na cikin gudanar da Sallar Idi masu jihadi suka karbe iko da Zariya, amma saboda hujjar kiyayyar Sarki Makau ga musulunci, wasu suka ce sam ba haka bane, yana bayan gari da dakaru yana sauraron yaji yadda ta kaya tsakanin dakarunsa da masu jihadi sai labari ya riske shi cewar masu jihadi sun karbe ikon garinsa cikin ruwan sanyi.

Wannan abu sai ya tsorata rundunar dashi kansa.

A ka ce sai Sarki Makau yayi kudu tare da wasu tsirarun dakaru da basu wuce dubu uku ba, ya sauka a garin Kajuru inda dan uwansa mai suna Albarka ke shugabanci.

Daga nan sai sarki Makau yabar Kajuru ya tafi Abuja inda ya kafa mulki acan. An ce kuma shine dalilin da har yanzu ake kiran sarkin Suleja da Sarkin Zazzau din Suleja.

Shi kuwa Albarka sai ya taho Zariya tare da dan wani malami mai suna Abduljalil dake karantaswa a Kajuru, sukayi mubuya’a ga Mallam Musa, aka kuma karbe su da martabawa.

An ce shine Aka baiwa Albarka gida a kusa da Fada, kuma daga gareshi Sunan Unguwar Albarkawa ya fkto.

Shi kuma Ibrahim Tsoho aka bashi gida kusa da gidan wasu masu kakaki, kuma daga nan sunan unguwar Kakaki ya fito.

Mallam Musa kuwa shine ya zama sarkin Zazzau na farko bayan jihadi. Kuma yayi mulki ne a gidansa dake Unguwar Kwarbai, bayan fadar Zazzau ba tare da ya shiga gidan sarautar Bakwa ba saboda tsoron kada ya sauka daga tafarkin Sunna zuwa aikata abinda sarakunan Habe suke aikatawa.

Kunji yadda Jihadin Fulani a Zazzau ya kaya.

Zuwan Turawa Zariya

Kashi na daya

Daga Sadik Tukur Gwarzo

Tun gabannin mamayar Turawa ga daular Zazzau, an samu cewa karfin daular ya ragu nesa da yadda ta kasAn ce a baya sabili da wasu dalilai.

Da fari dai, akwai rikicin cikin gida daya mamaye kabilun fulani da suka jagoranci karbe ikon Zazzau a zamanin Jihadi saboda neman mukami.

An ce tun zamanin Sarki na farko aka soma wannan sabanin tsakanin Jagora kuma sarkin Zazzau na farko Mallam Musa da wani Ja’e shugaban kabilar fulani Yesgwamawa, amma sai aka bashi sarautar Kajuru aka zauna lafiya.

Daga baya sai rikicin ya sake kamari bayan rasuwar Sarkin Zazzau Usman Yero, a wajajen shekara ta 1897 kenan.

Hakan ya samu ne ta yadda kabilu hudu na fulani da aka sani da mulkin Zazzau suka nuna bukatarsu ga mulkin, kabilun sune Mallawa, Katsinawa da Barnawa.

A cikin masu neman mulkin akwai dan marigayi Sarki Yero mai suna Madaki Kwasau, sai Mallam Lawan dan tsohon Madaki da kuma wani daga cikin ‘ya’yan tsohon sarkin Zazzau Mallam Sambo.

Babban abinda kuma ya samar da sabani a lokacin shine yadda Galadima ya tsaya kai da fata cewar wani kurma kuma Makaho mainsuna Mallam Muhammd ya kamata a baiwa sarauta. Mutane sunce hakan nada nasaba da kokarinsa na dora wanda ba zai iya katabus ba a mulki ta yadda zai rinka juya shi.

Ganin karfin ikonsa ya sa wadancan kabilu na fulani suka dunkule tare da goyawa Madaki kwasau baya domin ya zama sarki. Akan haka suka nemi gudunmuwar Sarkin Kano Aliyu Babba, da kuma rundunar ‘yan bindiga da mahaifin Madaki Kwasau ya kafa a zamanin rayuwarsa, shikuwa Galadima sai ya nemi goyon baya daga Sokoto.

 

Za mu cigaba a mako mai zuwa in sha Allahu.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Osinbajo Da Malamai ’Yan Siyasa Abu Daya Ne –Malam Ibrahim Khalil

Next Post

A Na Zargi ’Yan Bangar Kungiyar Garu Da Kashe Matashi A Bauchi

Labarai Masu Nasaba

Rubutun

Yadda Aka Fitar Da Sakamakon Gasar Rubutun  Hikaya, Na Diyan Gobir

by Mukhtar Yakubu
2 months ago
0

...

Marubuci

Ta Hanyar Karance-karance Mutum Yakan Zama Marubuci, In ji Fatima Muktar Gombe

by
2 months ago
0

...

Muluuk

Labarin Asadulmuluuk (17)

by
3 months ago
0

...

Muluuk

Labarin Asadulmuluuk (15)

by
4 months ago
0

...

Next Post
A Na Zargi ’Yan Bangar Kungiyar Garu Da Kashe Matashi A Bauchi

A Na Zargi ’Yan Bangar Kungiyar Garu Da Kashe Matashi A Bauchi

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: