Makon jiya Akwai daga tarihin Zazzau labarin wannan takobin mai suna Zazzau, wadda wasu ke kallon daga sunan ta aka sanyawa daular suna. Akwai masu kallon cewa asalin takobin ta sarki Gunguma ce wadda ya yaki abokan gaba da ita, don haka aka ajiyeta a masarautar bayan rasuwarsa ta yadda kowanne sarki yazo sai yasha alwashi da ita. Haka kuma babu takamaimen lokacin da sarkin Gunguma ya soma sarautar Zazzau da kuma adadin shekarun da ya yi dashi da sarakunan nan goma sha shidda da suka gabace. Watakila hakan ta faru kasan cewar Zazzau bata da tsohon ajiyayyen rubutaccen tarihi misalin irin na masarautar kano. To amma duk da haka, an hakikAn ce rayuwar sarakunan ta wanzu ne sama da karni na goma sha daya, zuwa kasa da karni na goma sha biyar. Haka kuma Leo Africanus ya ruwaito cewar a wajajen shekara ta 5012 miladiyya daular Songhai ta kasar Mali da Sarki Muhammadu Askiya na daya ke jagoranta ta kwace ikon daular Zariya. Watakila a lokacin sarki Muhammadu Abu (sarki na goma sha takwas) ne ke sarauta, ko kuma tana iya yiwuwa Muhammadu Abu ya hau sarauta ne da sahalewar torankawan Mali wadanda suka kawo musulunci Zazzau tunda a jerin sunayen sarakunan nasa ne yafara da Muhammadu. Daga nan sai wani abu da akaji akan sarkin Zariya na 22 Bakwa Turunku. An ce shi ne mahaifin Sarauniya Amina, da ‘yar uwarta Khadija mai lakabin Zariya wanda ya taso da cibiyar daular Zazzau daga wani wuri zuwa wani. Khadija ce akace ta kafa wani dan kauye mai suna Zariya, wanda yanzu ya bunkasa har cibiyar daular Zazzau ke ciki. Ita kuwa Amina an fi cewa ita sarauniya ce wadda sunan ta ya shahara a kasar hausa duk kuwa da kasAn cewar babu sunanta a jerin sarakunan Zazzau da aka bayar. Wasu na ganin abubuwa biyu ne suka sanya haka. Na farko akace bata zauna a Zazzau tayi mulki ba a sanda ta zamo shugaba, sai kawai ta fita cinye garuruwa da fadada girman daularta. Abu na biyu kuwa shine wanda ake kallon Amina a matsayin sarauniya, kuma shugabar mayaka wadda ba itace lamba daya mai fada aji a Zazzau ba. An samu cewar a Zazzau ana kiran ‘yar sarki da suna Sarauniya, mahaifiyar sarki kuma da suna Iya. An ce wadannan mataye biyu nada fada aji da matukar tasiri a masarautar Zazzau Don haka wasu ke hasashen Amina a sarauniya kurum take, watau diya ga sarki Bakwa Turunku, kuma danuwanta shine wanda ya zama sarki bayan rasuwar Mahaifinsu, ita kuwa sai taci gaba da zamowarta sarauniya, wadda ta fita kasashe yaki na tsawon shekaru har kuma ta mutu acan ba tare da tayi aure ba. Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya karyata wadanda ke cewar ba’a taɓa yin wata mace mai suna Amina a Zariya ba a littafinsa ‘Infakul Maisur’ inda yace a zamaninta ta cinye garuruwan dake makwabtaka da Zariya musamman na Nufawa dana Kwararrafawa. Kuma suna biyanta Jizya. Harma sarkin Nufe ya taɓa aika mata da bayi Arba’in da kuma goro dubu goma. Yace kumu Amina tayi sharafi tsawon shekaru 34. Amma abu mai gaskata wanzuwar Amina shine wani kufai da ake samu a garuruwan da taci ko ta sauka wanda ake kira da suna ‘ganuwar Amina’. Wanda kuma har yanzu akwai ɓurɓushinsa a garuruwa da yawa cikin kasar hausa dana makwabta. Kari akan kasashen da akace Amina taci galabar yaki akai baya da kasashen Nufawa dana Kwararrafawa, akwai kasar Gwari, kasar kano, kasar katsina, da kasashen yankin Nasarawa. Tarihin Kafuwar Daular Zazzau Kashi na shidda Sauran sarakunan da akace sunyi sarautar Zazzau da shekarun mulkinsu sune kamar haka:- (koda yake akwai saɓanin shekaru daga masu ruwaitowa) Ibrahim 1539-1560 Karama 1566-1576 Kofa 1576-1578 Bako I 1578-1581 Aliyu I 1581-1587 Ismailu 1587-1568 Musa 1598-1599 Gabi 1598-1601 Hamza 1601-1602 Abdaku 1602-1610 Burewa 1610-1613 Aliyu II 1613-1640 Makama Rabo 1640-1641 Ibrahim Basuka 1641-1654 Bako II 1654-1657 Sukwana 1657-1658 Aliyu III 1658-1665 Ibrahim Dan Aliyu 1665-1668 Mamman Abu 1668-1686 Sune 1686-1686 Bako dan Musa 1696-1701 Isiyaku dan Gabi 1701-1703 Burema Ashakuka 1703-1704 Bako dan Sukwana 1704-1715 Muhammadu dan Gunguma 1715-1726 Uban Bawa 1726-1733 Muhammadu Gabi 1733-1734 Abu muhanad Gani 1735 Gabir dan Ashakuka 1734-1737 Makama Abu 1737-1737 Bawo 1737-1757 Yunusa 1759-1767 Yakubu 1765-1764 Aliyu IB 1767-1773 Cikkoku 1773-1779 58.Muhammad Maigamo1779-1782 Jatau (isiyaku) 1782-1802 Makau 1802-1804 Sarakunan Zazzau na Fulani Bayan Jihadin Shehu Usmanu dan fodio:- Sarkin Zazzau Malam Musa 1804-1821 Sarkin Zazzau Malam Yamusa 1821-1834 Sarkin Zazzau Malam Abdulkarimu 1834-1846 Sarkin Zazzau Malam Hammada ( kwana hamsin da uku ya yi) Sarkin Zazzau Malam Mahamman Sani 1846-1853 Sarkin Zazzau malam sidi ( shima wata ya yi yana mulki). Sarkin Zazzau Malam Abdulsalam 1853-1863 Sarkin Zazzau Malam Abdullahi 1863-1873 Sarkin Zazzau Malam Abubakar 1873-1876 Sarkin Zazzau Malam sambo 1881-1890 Sarkin Zazzau Malam Yero 1890-1897 Sarkin Zazzau Malam Kwasau 1897-1903 Sarkin Zazzau Malam Alu dan Sidi 1903-1920 Sarkin Zazzau Malam Dalhatu 1920-1924 Sarkin Zazzau Malam Ibrahim 1924-1936 Sarkin Zazzau Malam Jafa’ru 1937-1959 Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu 1959-1975 Sarkin Zazzau Alhaji shehu idris 1975 zuwa yanzu. Fadar Zazzau Ana kiran gidan sarkin Zazzau da suna ‘gidan Bakwa’, kuma yana nan a unguwar da ake kira kofar fada dake tsakanin Madarkachi da Fadamar Bono. A nan ne kusan duk sarakunan da suka hau karagar mulkin daular suke zama. An ce tun zamanin Sarki Bakwa Turunku aka gina shi, a wajajen 5036 miladiyya kenan, don haka ma ake kiran gidan da sunan sa. Wasu suka ce wani maharbi ne ya bada shawarar ayi gidan anan bisa dalilai na tsaro. Da fari, yace wajen kan tudu ne, zai baiwa jagoran gari damar kallon duk abubuwan dake faruwa a Kufena, Turunku, Hange da sauran unguwannin cikin ganuwa. Sannan wajen yafi kusa da tsakiyar gari inda da zarar an buga kugen taruwar jama’a, mutane zasu runtomu da gaggawa. Wannan fada an gina ta da turɓaya ne, kuma an kasa ta gida hudu. Akwai Fada inda sarki ke zama da fadawa ayi fadanci. Akwai sashen da sarki ke kwanciya. Akwai cikin gida sashen da iyalan sarki suke. Sai kuma tsohuwar gida inda barorin sarki suke. Amma a karni na goma sha takwas, An ce sanannan maginin nan mai suna Muhammadu Durungu, Babban Gwani ya sake sabunta gidan tare da gina masa sabbin dakuna na kasaita. Haka kuma bayan jihadin fulani, sarki na farko watau Mallam Musa bai shiga gidan ba bisa tsoron kada ya zama mai aikata irin abinda hausawan haɓe ke aikatawa kafin jihadi, don haka ya yi mulkin Zazzau daga gidansa dake unguwar kwarbai. Wanda ya biyo bayansa Mallam yamusa shima bai dhiga gidan Bakwa ba bisa wancan tsoro, sai ya yi mulki a gidansa dake Unguwar kaura. Daga nan sai Mal Abdulkarim da yazo, shi kuma ya shiga gidan Bakwa ya yi sarauta, kuma a lokacinsa akace magini Muhammadu Durungu ya yi wa fadar gyara na musamman. Amma bayan mutuwar sarkin sai wanda ya gajeshi mai suna Hammade yaki shiga fadar, ya yi kwanaki yana mulki ya rasu, sarakunan kabilar fulani Bare-bari suka biyo bayansa, suma sai sukayi mulkinsu a Unguwar kaura. Abdulsalam ya yi nasa mulkin a gidansa dake Unguwar Bishar. Mal Abdullahi ya yi mulki a kofar Doka. Mal Abubakar ya yi mulki ba tare daya shiga gidan ba. Wanda a ka ce ya komowa gidan shine Mal Sambo, kuma tun daga kansa har yanzu sarakunan Zazzau na shiga domin yin sarauta.