Tarihin Masallacin Agadez A Jumhuriyyar Nijer Mai Ban Al’ajabi

Agadez

Bisa bayanan kakanin kakanni ana iya kiyasin cewa Masallacin ya kai shekaru 700 zuwa 800. Masallacin dadadden wuri ne sosai wanda ke hade da tarihin Abzine

Sallar Juma’a A Masallacin Agadez

Masallacin Juma’a na Agadez, tun kafa Agadez aka yi shi, ya fadi aka sake zuwa aka gina shi, bayan da ya fadi ne aka dauko wani Mallami mai suna Zakariya. Sarkin Agadez na wancan lokacin, ya neme shi ya ce cikin amanar Allah ya zo ya yi mishi Masallaci na Juma’a, kasancewar dama can shi ya yi na Timbuktu da na Gao.

Mallam Zakariya ya amince ya gina Masallacin amma bisa sharadin cewa za’a tara mutane su kawo sadaka saboda Allah ba tare da an matsa masu ba. Haka kuwa aka yi mutane suka taru suka ba da sadaka. Wannan waliyin ya dauki lokacinsa ya gina wannan masallaci. Ya ce duk wanda ya ga faduwar wannan masallaci zai ga tashin alkiyama

Yadda Aka Gina Masallacin

Wasu suna rade-radin cewa daga an tashi da safe sai a ga ana cigaba da gina Masallaci, ba’a sanin ainihin yadda ake yi, amma Muhammed Bilal wani masanin tarihi, ya ce wannan zance ne kawai na mutane, shi dai wannan bawan Allah ya sa an kawo sadaka duka, lokacin da ake aikin, akwai sanhuna wadanda ake zuba laka ana badawa, sa’an nan da fodannai da ake daurawa duniya duk bata san da irin wannan ba, har Ubangiji Allah ya sa aka yi shi. To sai dai ya ce ba zai iya ba da tabbacin cewa daga gari ya waye ake ganin mutane na gini ba shi dai jagoran ginin abun da ya ce kawai shi ne wanda ya ga faduwar ginin, zai ga tashin Kiyama.

Tsarin ginin Masallacin

Kakanni wadanda suka ga mulkin akalla sarakuna bakwai a wancan lokacin, suka ba da wannan bayanan, inda suka ce akwai matattakala wacca ake hawanta a yi kiran Sallah kafin Liman ya zo.

A karkashinta kuma akwai wata rijiya wacce bakin mambari ne wanda aka aza wani abu, yadda kafin a kare Liman yana iya zama.

Duk wadannan an yi su ne bisa tsari na da wanda ba kowa ba ne zai iya fayyacewa. A wancan lokacin ne ma aka yi wani aljani da ya rika hawa matattakalar yana kashe mutane, sai Ladanai 40 su mutu a yini guda kafin a yi Sallar Juma’a. Lokacin bayin Allah ne da dama suka taru suka rika addu’a, har Allah ya basu iko, a wani hawa da dayansu ya yi yana kira sai ya tsage cikin aljanin, aka ce jinin ya zubo kan wani gurbi wanda aka rufe shi a ciki har ya zamana ana iya zama a kai. Mutane sun kuma sami tarihin wannan aljani a gidajen da ake koyar da karatu ko kuma samun abinci da kuma gidajen sarauta.

Shekarun Masallacin

Wasu na cewa Masallacin na da shekaru 700 zuwa 800. Dadadden wuri ne saboda Abzin ta dade dukka. An yi abubuwan tarihi kamar nadin sarauta duk a gaban idon abzin. Saboda tarihi ya nuna cewa cikin sarautar abzine Shehu Dan Fodio ya yi sarautar Sokoto, daga sarautar Sokoto aka yi ta Kano. Shi Shehu Usmanu Mujadaddi da farko sai da ya je kasar Abzine inda akwai kanin mahaifiyarsa Malam Muhammad Sambo shi ya fara koya masa karatu, amma daga baya, akwai wani Malami mai suna Jibril, wanda ya cigaba da yi masa karatu. Wannan Masallaci kafin zuwan manyan naurorin sadarwa shi ne akan yi amfani da shi wajen kwatance, tamkar tambari ne na kasar Abzine.

Mawallafa: Tilla Amadu/ Pinaɗo Abdu. Edita: Usman Shehu Usman.

Exit mobile version