Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Masarautar Bakori Jihar Katsina

by
3 years ago
in TARIHI
3 min read
Tarihin Masarautar Bakori Jihar Katsina
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Kasar Makama tana da tarihi mai yawa, bayan jihadin Shehu Danfodio kusan duk Kudancin Katsina ta koma karkashin galadiman Katsina hakimin Malumfashi, bayan zuwan Turawan mulkin mallaka aka kawo sababbin sauye-sauye a mulkin kauyuka kuma aka raba masarautar galadima domin kirkiro sababbin hakimai ciki har da Maska.

A shekara ta 1915 aka kirkro masarautar Makama a yankin nan mai arzikin noma na Danja Tandama wannan ya biyo bayan yunkurin inganta shugabanci a karkara tare da samar da haraji mai yawa.

Farko wanda aka fara nadawa a matsayin Makaman Danja shi ne Iya Labaran Nadabo. Shi Iya Labaran makusanci ne ga sarkin Katsina Muhammad dikko. Kafin wannan nadin shi ne Sarkin fadar sarkin Katsina, kuma ya taba rike Makurda Bambanmi da Kafarda a Kankiya a matsayin dagaci. Domin saukaka shugabanci Iya Lbaran ya mayar da fadarsa ta mulki daga Danja zuwa Bakori a shekara ta 1931, Kasancewar Bakori na da babbar hanya.

Labarai Masu Nasaba

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

Bayan da Allah ya karbi ran Iya Labaran a 1952, an nada dansa mai suna Mu’utasim Ibrahim wanada aka fi sani da Iya Iro wanda ya yi murabus a 1955, aka kuma nada dan uwansa mai suna Ibrahim Nadabo a matsayin sabon hakimin Bakori, sannan kuma aka mayar musu da sunan sarautarsu ta Makama wadda a da aka kai masa. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba akiransa da Iya sai dai Makama. Haka kuma, yanzu haka hakimin Mashi ne ake amsa sunan Iya.

kafin nadinsa Makama Alhaji Idris Nadabo, ya rike sarautar sarkin fawan Katsina hakimin Kankara, kasancewar ita ma wannan sarautar sun gajeta. Tarihi ya tabbata cewa Makama Idi shugaba ne adali kuma mai kishin addini wanda hakan ne ya jawo masa kauna da kuma soyayyar talakawansa.

Allah ya karbi ran Makama Idi ranar 11 ga watan Fabarairu, 1980. An nada dansa mai suna Alhaji tukur Idris a matsayin wanda ya gaje shi. An fitar da Tsiga da Danja daga cikin masarautar Makama, aka yi musu hakimai.

ADVERTISEMENT

A shekarar 1992, aka nada alhaji Sule Idris Nadabo a matsayin Jarman Katsina, kuma hakimin Tsiga na farko, kafin daga bisani a dawo das hi Bakori a matsayin sabon Makaman Katsina IB sakamakon murabus da Makama Tukur ya yi a shera ta 1955.

Allah ya karbi ran Makama a shekara ta 2007, mutanen garin Bakori sun nuna alhininsu na rashin wannan jajirtaccen shugaba, mai kishin al’ummarsa(Allah ya gafarta masa).

A ranar 22 ga watan Maris 2007, aka nada Alhaji Idris Sule Idris a matsayin Makaman Katsina na biyar. An haifi maigirma Alhaji Idris Sule Idris a ranar 25 ga watan Oktoba, 1967. Kafin nadisa ya yi karatun addinin Musulinci, sannan kuma ya fara karatunsa na boko a makarantar firamare ta Sambo da ke Funtuwa a shekara ta 1979. Dagan an sai ya samu shiga Gobernment College Katsina, ya kammala a shekara ta 1984 zuwa 1900. Bayan ya kammala sai ya shiga makarantar College of Administration da ke Funtuwa a shekara ta 1990 inda ya yi Clerical Officer (Gen) Certificate. Maigirma Alhaji Idris sule Idris  bai tsaya nan ba sai ya wuce Hassan Usman Katsina Polytechnics a shekara ta 1999, inda ya yi karatun Difuloma a Finance, sannan ya koma don yi babbar Difuloma a kan Accounting a shekara ta 2005.

Aikace-aikacen da Maigirma Makaman Katsina Idris Sule Idris ya yi:=

Makaman Katsina ya fara aiki da karamar hukumar Bakori a shekara ta 1990 a matsayin Clerical  Officer bayan ya I shekara daya sai ya koma hukumar tara kudin shiga ta jihar Katsina  a matsayin jami’in karbar haraji a shekarata 1994.

Maigirma Alhaji Idris Sule Idris ya yi aiki da hukumar tara kudi ta kasa a ofishinta da ke Katsina har zuwa shekara ta 2001 wanda daga nan aka mayar da shi Gusau a matsayin kashiya har zuwa shekara ta 2004, sannan kuma aka sake dawo da shi Katina har zuwa lokacin da ya gaji mahaifinsa Makama a ranar 22 Maris, 2007.

A cikin shekara goma da maigirma Idris sule Idris Makaman Katsina Hakimin Bakori ya yi bisa karagar mulki, ya samu muhimman nasarori kuma kasar  Bakori ta samu gagarumin ci gaba wanda hakan ked a dangantaka da kyakkyawan shugabancin da ta samu.

A cikin shekara goman da ya yi an samu cikakken zaman lafiya a kasar Bakori, kuma hakan na da nasaba da tabbatar da adalci ga kowa wannan kuma ta sa kullum maigirma hakimi yana tare da jama’arsa su ma suna tare da shi.

Sannin cewa al’ummar wannan kasa maigirma Hakikimi zai yi musu adalci a dukkan koken da suka kawo, ya sa ma fi yawan matsalolin da ke tasowa tsakanin al’umma sukan garzayo fada su kawo kokensu wanda cikin ikon Allah da kwarewar mulki Hakimi kan daidaita tsakani maimakon a je ofishin ‘yan sanda ko kuma kotu, sai a samu masalaha da fahimtar juna, wanda hakan ke kaea kaefafa zumunci a tsakanin al’umma.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Dalilan Da Suke Sa Wasu ‘Yan Mata Ke Rasa Mijin Aure Da Wuri

Next Post

Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Iraki Ta Kazanta

Labarai Masu Nasaba

Masarautar Nupe

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

by
8 months ago
0

...

Hausa/Fulani

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

by
9 months ago
0

...

Coomassie

Tarihin Tsohon Sifeta Janar Na ‘Yan Sanda Ibrahim Coomassie

by
10 months ago
0

...

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

by
11 months ago
0

...

Next Post

Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Iraki Ta Kazanta

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: