Khalid Idris Doya" />

Tarihin Rayuwa Da Al’adun kabilar Rabari

A wannan mako  mun sami nasarar kewayawa, mu ka kuma kutsa cikin duniya, filin namu zai sadaku da Al’ummar “Rabari” da ke kasar “Gujarant” ta cikin yankin Indiya.

Al’ummar ‘Ribari’ sun kasance makiyaya ma’ana masu kiwon dabbobi daga wani bangare zuwa wani bangare na yankin kasar domin nema wa dabbobinsu abinci, basu da takamaiman wajen zama guda daya kasancewar su dai ba mazauna waje daya ba ne,su na kiwon dabbobi kamar shanu, tumakai, awaki, rakuma da dai sauran dabbobin gida da aka san su.
Abu mafi ban mamaki ga wannan al’umma shi ne da a ce yau an wayi gari wata dabba daga cikin dabbobinsu ya kwana da yunwa, gara ace daya daga cikinsu bil adama ya kwashe sati guda ba tare da ya sanya koda kwayar hatsi a bakinsa ba.
‘Tirkashi !’ Tabbas wannan dabi’a ta su abar dubawa ce, su kan bawa dabbobinsu kulawa fiye da da bil’adama. Babban tashin hankali ne a gare su ace dabba tana jin yunwa.

Al’ada
A wasu lokutan akan iya hangar mutanen ‘Rabari’ tafe da shanunsu su na kora su a kan tituna tare da iyalansu wadanda su ke sanye da tufafi irin na su na gargajiya.
Mata daga cikinsu su na hura wutar itace ya ruru sosai domin su yi amfani da shi wajen girki,su na debo ruwa domin yin amfani sannan daga bisani kuma su kan tattare dukkan kayayyakinsu su dora a kan rakuma, akasarinsu za ka gansu sanye da sutturunsu ma su kyau, wanda yawanci ya kan kasance ‘siket’, mayafai masu kyalli,kayan ado na kawa wadanda su ka kasance masu kara da daukar hankali.
Mazaje daga cikinsu sun kasance masu dan duhu, dogaye ne  bugu da kari kyawawa ne matuka.
Mafi ban burgewa da sha’awa daga wadannan mutane shi ne ,su dai suna yin tufafi, tukwane, kayan kwalliya, da dai sauran kayayyakin amfaninsu na gida da kansu ba tare da sun ce lallai sai wani ya yi sannan su samu ko su saya ba, ma’ana mutane ne masu kirkira kuma su kera ababen amfani da kuma bukatunsu na yau da kullum.
Matansu su na a sahun mata masu ado na bajinta,su kan sanya maka- makan zobba a hancinsu, jibga-jibgan ababen wuya, sannan kuma ga dirka- dirkan kayan ado na kawata hannaye kamar su:  zobe, awarwaro, sarkar hannu.
Matansu su na sanya tufafi wadanda kalolinsu ke da hasken gaske, akasari su kan yi amfani da kaya masu haske wanda ya sanya har ake iya banbance matan “Rabari” daga cikin sauran mata.
Matan aure daga cikinsu su na amfani ne da kayan ado farare misali: farin awarwaro wanda ake sanya shi tun daga tsintsiyar hannu har zuwa kafada, ‘yan mata kuwa su ma ba a barsu a baya ba domin kuwa su ma su kan yi nasu kwalliyar iya bakin gwargwado, su na amfani da zoben kafa, sarkar kafa, yankunne, zoben hanci da kuma sakar hannu.
Akwai abin daukar hankali dangane da wadannan mutane,wannan abu ya kasance wani nau’in zane da a kan yi musu a jiki wanda kuma baya fita(tattoo) akan yi musu zanen abubuwa kamar dangin: maciji, kunama da sauransu. Wannan zane ana yi musu shi a wurare kamar fuska, hannaye, kafafu.

Auratayya
Al’ummar “Rabari” su na aure ne ta sigar hada aurarraki masu tarin yawa sannan sai ayi hidimar biki a lokaci daya, ma’ana a tare za’a tara auren mutane daban-daban sannan sai a gudanar da shi a wani lokaci da su ke kira da”Janmashtani”.
Janmashtani: lokaci ne da ake bikin murnar zagayowar shekarar haihuwar Abin bautarsu na ‘hindu’ mai su na “krishna”.
A lokacin gudanar da wannan biki akan sakaye amare ta hanyar rufe mu su jiki tun daga fuska har kafafuwansu ,sai kuma a kama wani bangare na jikin tufafin nasu a daure a jikin tufafin mijin da kowacce za ta aura, wanda kuma su ma sanye su ke da maka-makan huluna ta al’ada kamar dai rawani.

Abinci
Cimar al’umar dai ta kasance kakkaurar madara ce mai zakin gaske, ita wannan madara akan sarrafata ne ta hanyar dafawa a kan wuta mai karancin zafi, sannan kuma sai a bar ta akan wuta ta yi ta dahuwa,  zata dauki lokaci mai tsawo ta na dahuwa sannu cikin hankali zata yi kauri kuma sai kalar ta ta koma ruwan hoda.

Addini
Al’ummar ‘Rabari’ sun kasance masu bautar abin bautar ” hindu” wanda suke yiwa lakabi da “Krisha”.

Exit mobile version