Abba Ibrahim Wada" />

Tarihin Wasanni A Nigeriya Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

Tun lokacin da Nigeria ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960 kawo yanzu ta taka rawar gani a fannin wasanni da dama, ta kuma ci karo da cikas iri-iri kuma Najeria ta haskaka a wasanni da dama da suka hada da kwallon kafa da damben boksin da kwallon kwando da na tennis da wasannin nakasassu a nahiyar Afirka da duniya tun kafin samun ‘yancin kai a shekarar 1960.

Hakan ya sa ta yi kawaye da abokan hamayya da suke gwabzawa a duk lokacin da wasa ya hada su, sannan ta samar da zakakuren ‘yan wasa da suka yi suna kuma suka wakilce ta a fanni da dama da wasunsu ma suka samu aikin yi.

Kwallon kafa – Tawagar Najeriya da ake kira Super Eagles ta dauki kofin nahiyar Afirka guda uku kawo yanzu, ta kuma je wasannin karo da dama domin Super Eagles ta ci kofin nahiyar Afirka a karon farko a shekarar 1980 sannan ta ci na biyu a 1994 da kuma 2013 da ta lashe na uku jumulla kuma  gasar kofin nahiyar Afirka sau 18 Najeriya ta halarci wasannin.

Tun farko ana kiran tawagar ta Najeriya da sunan Green Eagles wadda ta fara zuwa gasar nahiyar Afirka a shekarar 1963 shekara uku da samun ‘yancin kai sannan kuma Super Eagles ta saka kaimi a wasanninta inda ta je gasar cin kofin duniya karo shida, bayan da ta fara halarta a shekarar 1998, kuma wanda ta fi taka rawar gani shi ne na 1994 wanda ta kai zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

A wasannin matasa Najeria ta taka rawar gani inda tawagar Golden Eaglets ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 ta ci kofin duniya karo biyar a shekarar 1985 da 1993 da 2007 da 2013 da kuma 2015 har ila yau tawagar ta ci kofin Afirka karo biyu a 2001 da kuma 2007, ta kuma zo ta hudu a 2019.

Ita kuwa tawagar matasa ‘yan shekara 23 da ake kira Dream Team ita ce ta farko daga Afirka da ta ci lambar zinare a fagen kwallon kafa a wasannin Olympics saboda tawagar ce ta yi nasarar samun lambar zinare a shekarar 1996 da aka yi a birnin Atlanta na kasar Amurka, sannan ta yi ta biyu a wasannin da aka yi a shekarar 2008 a birnin Beijing na kasar China.

Tawagar kwallon kafa ta mata kuwa ta Nigeria, Super Falcons ta lashe kofin Afirka sau 11 daga gasanni 13 da aka yi haka kuma Falcons din ta je gasar cin kofin duniya sau takwas, kuma na farko da ta fara zuwa shi ne a shekarar 1991, wanda ta fi yin abin kirki shine a shekarar 1999 wanda ta kai wasan dab da na kusa dana karshe (kuarter finals).

Ko a kwallon rairayi – Najeriya ta taka rawar gani, inda ta lashe gasar Afirka a shekarar 2007 da kuma 2009, sannan ta yi ta biyu a 2006 da kuma 2011, ta kuma yi ta uku a 2015 sannan ta yi ta hudu a 2013.

Kwallon guragu da aka yanke musu kafa ta duniya  kuwa tawagar Najeriya ta ‘yan wasan ta je gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Medico a shekarar 2018, bayan karo uku da ta kasa zuwa saboda karancin kudi kuma dan wasa Goodluck Obieze shi ne ya yi wa Najeriya kyaftin  sai dai kungiyoyin kwallon kafa na Nigeria ba su yi abin azo a gani ba a gasar Zakarun Afirka.

Ita kuwa Shooting Stars Sports Club ta garin Ibadan 3SC ita ce ta fara lashe wa Najeriya African Cup Winners Cup a 1976, bayan da ta yi nasara a kan Tonnerre Yahounde da ci 4-2 gida da waje.

Shekara 16 tsakani kungiyar ta ci CAF Cup, bayan da ta doke Billa SC ta Uganda 2-0 gida da waje, shekara daya tsakani Enugu Rangers ita ma ta ci CAF Cup bayan da ta yi nasara a kan Canon Yaounde da ci 5-2 gida da waje.

Daga nan ne sai da Najeriya ta yi shekara 38 kafin ta lashe kofin Zakarun Afirka wato CAF Champions League, inda Enyimba International ta lashe a shekarar 2003 da kuma 2004 a jere.

Tun daga nan, kungiyoyin kwallon kafar Nageriya ba su sake taka rawar gani a wasannin ba, inda a bana ma aka fara cire Kano Pillars sai Enyimba ma ta yi ban kwana da gasar ta koma Confederations Cup, ya yin da Enugu Rangers ta kai bantenta.

Sai dai wasan kwallon kafa a Najeriya ya ci karo da cikas a fanni da dama har da rigimar shugabancin NFF da aka yi ta yi har Fifa ta ce za ta dakatar da kasar kuma sannan ‘yan wasa a karo da dama sun yi zanga zanga kan kin biyansu hakkin wasa.

A ‘yan shekaru, Najeriya ba ta taka rawar gani a wasannin tsalle-tsalle da guje-guje na duniya ba, duk da kokarin da take yi a gasar Afirka idan aka kwatanta da kwazon da take yi a All Africa Games da sauran wasannin Afirka.

Wasannin Olympic – Najeria ta fara zuwa wasannin Olympic a shekarar 1952 bangaren tsalle-tsalle da guje-guje, haka kuma ta halarci gasar duniya ta The IAAF, inda ta yi bajinta a kakar 1989 zuwa 1999.

A kakar wasannin 1998, Gloria Alozie a tseren mita 100 da tsallen shinge da Falilat Ogunkoya a tseren mita 400 suka daga martabar Najeriya haka ma a shekarar 1999 Charity Opara da Falilat Ogunkoya suka kare a mataki na daya da na biyu a tseren mita 400, tun daga nan kuma shiru kake ji.

A wasan matasa na nahiyar Afirka, Najeriya ta lashe gasa ta 12 da aka yi a birnin Addis Ababa, Ethiopia, inda ta ci lambar yabo ta zinare 12 da Azurfa takwas da tagulla 7 hakan yana nufin wasan tsalle-tsalle da guge-guje wannan fanni Najeria ta yi fice wajen taka rawar gani da ‘yan wasanta ke gogayya da na Afirka da duniya.

Shekarar 1996 da 2000 ita ce Najeriya ba za ta manta da ita ba a wasannin tsalle tsalle da ta yi a Olympics domin ‘yan Najeriya Sunday Bada da Jude Monye da Clement Chukwu da kuma Enefiok Udo Obong sun taka rawar gani a 2000 inda suka lashe lambar zinare, shekara 12 tsakanin suka ci zinare, bayan da aka samu daya daga ‘yan tseren Amurka da laifin shan abubuwan kara kuzari duk da sune suka lashe tseren.

Wani wasan da Nigeria ta taka rawar gani shi ne wadanda aka yi a Atlanta a shekarar 1996, inda Chioma Ajunwa ta yi tsallen da ta lashe zinare tun farko da ya kai nisan mita 7.12 kuma har yanzu ba’a samu wadda tayi abinda tayi ba a wancan lokacin.

Wasan kwallon tebur – Wasan kwallon tebur ya kai Najeriya mataki da dama, bayan da ta zama ta daya a Afirka, kuma tun samun ‘yancin kai a shekarar 1960 ‘yan wasan kasar maza da mata ke yin abin kirki a nahiyar da ma duniya.

‘Yan wasa kamar Atanda Musa da Segun Toriola da Sule Olaleye da Kazeem Nosiru da Monday Merountoun da kuma na kwanan nan Aruna Kuadri sun ci wa kasar lambobin yabo a Afirka da duniya.

A kakar wasa ta  1998 zuwa 2008 Segun Toriola ya rike mataki na daya a Afirka a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon tebur, haka shi ma Aruna Kuadri bai bai wa kasarsa kunya ba, bayan an zabe shi tauraron dan wasa a shekarar 2017.

A bangaren wasannin mata Bose Kaffo da Biola Odumosu da kuma Funke Oshonaike sun bi sahun bajintar da maza suke yi, inda su uku suka lashe lambobin yabo a wasannin nahiyar Afirka da ya hada da All African Games da na Commonwealth Games.

Exit mobile version