Tarihin Wasu Shugabanni Da Su Ka Tallafa Don Cigaban Arewacin Nijeriya

Daga Sadik Tukur Gwarzo, RN 08060869978

…………………………….

Cigaba daga makon jiya

 

  1. Tarihin Sir Kashim Ibrahim

An haifi Marigayi Sir Kashim Ibrahim a Kauyen Gargar na gundumar Yerwa, wanda a lokacin Shi ne babban birnin Maiduguri kafin a koma Borno.

Ya soma karatun addinin sa a gida kafin daga baya mahaifinsa Ibrahim Lakanmi ya shigar dashi makarantar Borno probincial a shekarar 1922.

Bayan shekaru uku, sai kuma ya samu gurbin karatu a kwalejin horas da dalibai ta Katsina inda ya samu takardar shaidar malunta a shekarar 1929.

Daga nan sai ya soma aiki a makarantar middle ta Borno a wannan shekara, a hankali ya na samun girma da karbuwa a wurin jama’a, har zuwa lokacin data kai a ka ba shi lakabin Shatiman Borno a shekarar 1933. Aka soma kiransa da Shattima Kashim.

Ya soma siyasa ne a shekarar 1951-52, sanda aka zabe shi a matsayin wakili na majalisar Arewa, daga nan kuma aka tura shi wakilci izuwa majalisar kasa daga Arewa.

Ya zama wannan wakili babu jimawa sai kuma akayi masa nadi izuwa Ministan walwala, sannan ya koma ministan Ilimi daga baya.

A shekarar 1956, aka yi masa mukamin Wazirin Borno, haka kuma ya samu zamowa Gwamnan Arewa dan Arewa na farko a shekarar 1962 kuma yana rike da wannan mukamin akayi juyin mulkin ranar 16 ga watan janairu na shekarar 1966 wanda Major Janar Aguiyi Ironsi ya zama shugaban kasar tarayyar Nijeriya.

A lokacin da akayi juyin mulki aka kashe manyan mutane daga Arewacin Nijeriya, sai aka garkame Sir Kashim Ibrahim a kurkuku, amma daga bisani aka sake shi, ya koma gidansa a maiduguri, ya sadaukar da mafi yawan gidan ga makaranta, sannan bai tsira da komai ba sai kudi kadan da gidansa da mota daya ta hawa, kuma tun daga nan bai sake komawa harkar siyasa ba.

Sir Kashim Ibrahim ya rike matsayin Chancellor na Unibersity of Ibadan daga 1966 zuwa 1977, haka kuma ya sake zama chancellor na Unibersity of Lagos daga 1977 zuwa 1984.

Kafin rasuwarsa a ranar 25 ga watan yulin 1990 sai daya shigar da gwamnatin tarayya kara saboda ta hanashi Fanshonsa na Gwamnan Arewa domin ya samu abin tabawa, kuma ya zamo abin so da alfahari ga kowa saboda gaskiyarsa da kiyayewa daga satar kudin jama’a tayadda aka rinka sakawa jarirai sunansa.

Haka kuma marubuci neshi, tunda ya wallafa littattafai biyu a zamanin rayuwarsa masu suna ‘Teachers guide to Arithmetic’ na daya zuwa na hudu da harshen kanuri. Da kuma ‘Kanuri reader for elementary school’.

A karshe, rayuwarsa abar koyi ce ga dukkan matasa saboda yadda ya sadaukantar da kansa ga gina Arewa da kuma irin nasarar daya samu a rayuwa.

Wannan ne takaitaccen tarihin Sir Kashim, Wazirin Borno, OON, Order of British Empire, LLD’s.

Da fatan Allah ya ji kansa. Amin.

 

  1. Tarihin Hassan Usman Katsina

An haifi marigayi Hassan Usman Katsina a birnin Katsina a shekarar 1933. Shi dane na uku ga marigayi Sarkin Katsina Usmanu Nagoggo dan Muhammadu Dikko.

Ya soma makarantar elementare a garin Kankia, sannan yayi makarantar Midil a birnin katsina. Inda daga nan ne ya samu damar shiga kwalejin Barewa da ke Zaria.

Bayan ya kammalata kuma ya shiga Makarantar Nijeriyan school of Arts and Sciences da ke nan Zaria, sannan ya shiga aikin soja a shekarar 1956.

Marigayi Hassan Katsina ya shiga aikin soja cikin nasara, duba da yadda ya rinka samun daukaka akai-akai da kuruciyarsa da kuma damarmakin karo karatu, a cikin haka yayi karatu a makarantun the Royal officer training school Ghana, the Mons Officer Cadet School da the Royal Military Academy Sandhurst inda akace anan abota ta hadu tsakanin sa da Iliya Bisalla.

Ya zama laftanal kanal a shekarar 1966, wanda daga nan akayi masa mukamin Gwamnan Arewacin Nijeriya a shekarar 1966 bayan hambarar da Gwamnatin Su Ahmadu Bello Sardaunan sokoto. Don haka Shi ne gwamnan Arewa na biyu dan Arewa bayan Sir Kashim Ibrahim.

Zamowarsa Gwamna a wannan lokaci wayau ne nasu Major Chukuma Kaduna wadanda akace sune suka kashe su Tafawa ‘Balewa, domin samun karbuwa daga ‘Yan Arewa bayan sun karbi mulkin kasa.

Don haka sai sukaga cewa Kasancewar Hassan Katsina dan Sarauta ne, bashi mulki zai sanya aminci a zukatan sarakuna da talakawan Arewa.

Watanni goma sha shidda da soma mulkinsa sai akayi jahohin Arewa, inda aka fitar da Jihar Kano, Kaduna, Arewa ta tsakiya da Arewa ta Kudu, a wancan lokacin sai aka karawa Hassan Usman girma a aikinsa na Soja

An nada shi mukamin Army chief of staff daga shekarar 1968 zuwa 1971 sannan ya samu dadin girma daga shugaban kasa na lokacin Gen. Yakubu Gowon bayan hambarar da Major Aguiy Ironsi kenan izuwa mukamin ‘Deputy Chief of staff supreme military headkuarters’.

Haka kuma yana da mukamin Major-General aka nada shi Federal commissioner of establishment na tsawon shekaru biyu sannan da kansa ya ajiye aiki watanni biyu bayan kisan Janar Murtala Muhammad a wani juyin mulkin da baiyi nasara ba, zamanin Olusegun Obasanjo kenan ke kan mulki da kakin soja, a ranar 29th na yulin 1975.

Tun daga nan kuma ya dawo gidansa na Kaduna da zama, kuma bai sake karbar wani mukamin gwamnati ba duk kuwa da tayin da shugabanni suka rinka yi masa, sai dai ya bada gudunmuwa wajen kafa jam’iyyun Siyasa.

Kafin rasuwarsa a ranar 24 ga watan yulin 1995, shi shahararren dan wasan Polo ne, kuma ya rike sarautar Chiroman Katsina har zuwa mutuwarsa.

Haka kuma, tun kafin rasuwarsa wasu mutane suka rinka jefa masa zarge-zarge na laifukan soji. Misali, wasu Inyamurai na ganin ya tsanesu kuma dasa hannunsa akayi musu kisan kare dangi a Arewa a zamanin yakin Basasar kasa, wasu kuma na kokarin shafa masa bakin fentin cewa dashi aka kashe Sardauna.

Sai dai a zahiri, duk manyan Abokansa sun karyata haka, bisa hujjar cewa ADC dinsa ma Inyamuri ne, kuma bashi da hannun kitsawa su sardauna juyin mulki, an dauko Shi ne kurum domin a nemi soyayyar ‘yan Arewa bayan juyin mulki.

An ce tun bayan shekarar 1993, ba’a sake ganin Marigayi Janar sani Abacha tare da Janar Ibrahim Babangida a wuri daya a wani taro ba sai lokacin mutuwar Marigayi Hassan Usman Katsina, inda mutane da yawa suka hadu bisa jimamin rashinsa.

Kuma an sanyawa wurare da dama sunansa a yankin Arewa domin tunawa dashi, mksali shune Hassan Usman Polytechnic.

Da fatan Allah ya ji kansa Amin.

 

Exit mobile version