Cigaba daga makon jiya
- Tarihin Alhaji Shehu Shagari
An haifi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a shekarar 1925 cikin kauyen Shagari, garin da kakan-kakansa Ahmadu Rufai ya kafa. Sunan mahaifinsa Aliyu, mahaifiyarsa kuwa sunanta Maryamu.
Mahaifin Shehu Shagari ke rike da mukamin Magajin Shagari, watau kamar dagacin kauyen kenan, sai dai Allah Ya yi ma sa rasuwa kafin a haifi Shehu Shagari, wanda hakan ya sa dan uwansa Bello ya cigaba da zamowa Magajin Shagari.
Shagari ya yi karatun Alkur’ani a gida, sannan ya fara fita waje neman ilimin zamani. A shekarar 1931 zuwa ta 1935 ya kammala karatun elementarensa a Yabo, sannan ya tafi midil da ke Sokoto a shekarar 1936, ya kammala a shekarar 1940. Daga nan sai ya tafi kwalejin Kaduna ya yi karatunsa daga shekarar 1941 zuwa shekara ta 1944.
Bayan ya kammala kwalejin Kaduna sai kuma ya samu gurbin karatu a kwalejin horas da malamai ta Zariya, inda ya kammala a shekarar 1952 tare da zamowa malami jiharsa ta Sokoto.
Shehu Shagari ya soma siyasa ne da zamowa akawun jam’iyyar NPC (Northern Progressive Party) reshen jihar ta Sokoto a shekarar 1951, sai kuma a shekarar 1954 a ka zaɓe shi a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar yammacin Sokoto.
A shekarar 1958, Shagari ya zamo akawun majalisar tarayya, amma a shekarar 1959 sai ya bar wa Tafawa Valewa wannan gurbi saboda martabawa. A wannan shekarar kuwa sai a ka nada shi ministan tarayya mai kula da kasuwanci da masana’antu.
Shagari ya rika samun sauye-sauyen hukumomi a matsayinsa na minista tun da a ka karɓi ’yancin kai a shekarar 1960 har lokacin da a ka yi juyin mulki a shekarar 1966. Haka kuma bayan Janar Yakubu Gawon ya zama shugaban kasa, an sake baiwa Shehu Shagari mukamin ministan kasa a shekarar 1970.
Baya da haka, a shekarar 1971-75 a lokacin yakin basasar Nijeriya, Shehu Shagari ya zama ministan kudin Nijeriya. Wannan kujera ce ta ba shi damar ya rike mukamin gwamna na bankin duniya, ya kuma zama daya daga cikin mutane 20 ’yan kwamitin bankin lamuni na duniya, watau IMF.
Shehu Shagari na daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar NPN a shekarar 1978 bayan an kashe Janar Murtala, a lokacin da shugaban kasa na lokacin Janar Obasanjo Olusegun ya bada izinin kafa jam’iyyun siyasa, don mika wa farar hula mulkin kasa.
Haka kuma a shekarar 1979 Shagari ya zama dan takarar shugaban kasa a tutar jam’iyyar tasu, kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana shi a matsayin wanda ya cinye zaɓe a wannan shekara.
Shehu Shagari ya yi shekaru hudu ya na mulkar Nijeriya, sannan ya sake neman takara kuma ya ci a shekarar 1983, to amma jim kadan da zaɓen, sai sojoji su ka yi ma sa juyin mulki a ranar 31 ga watan Disambar 1983, a lokacin da a ka nada Shugaba Muhammadu Buhari shugaban kasar Nijeriya kenan da kakin soja.
Hakika za a jima a na tunawa da Shehu Shagari a matsayinsa na shugaban kasar Nijeriya duba da kokarinsa wajen haɓaka samar da man fetur da inganta masana’antu da samar da Injinan aikin gona a shirinsa na ‘Green Revolution’ da gina titkna da su ka sadar da manyan jihohin kasar, don inganta zirga-zirga gami da samar da gidaje masu saukin kudi a birane da karkarar Nijeriya.
Da rarar kudin man fetur Shagari ya kammala ginin matatar man fetur ta Kaduna a shekarar, sannan ya kammala ma’aikatun sarrafa karafuna na Ajaokuta da wani irinsa a Delta a shekarar 1982.
A shekarar 1983 Shagari ya samar da kamfanin sarrafa alminiyon a Ikot Abasi duk kuwa da talaucin da kasar ke ciki saboda karyewar farashin mai a shekarar 1981.
A lokacin sai ya maida kasar izuwa dogaro da noma ta hanyar bada taki da iri mai kyau a kyauta ga manoma, sannan ya rage kudaden da gwamnatinsa ke kashewa tare da kara samar da kudaden shiga daga jami’an hana fasa kwauri na kasa, watau kwastam.
Sojojin da su ka hamɓarar da gwamnatin Shagari sun zargi gwamnatinsa da rashawa gami da magudi a zaɓen 1983, sannan sun yiwa ‘yan kasa alkawarin fitar da su daga kangin talaucin da su ka shiga biyo bayan karyewar farashin mai a kasuwar duniya
Shehu Shagari ya yi rayuwa mai kyau a iya shekarunsa 92 da haihuwa, ya janye jikinsa daga mafi akasarin lamurorin gwamnati dana siyasa don tsira da mutumcinsa, sannan ya auri mata uku; sune Amina, Aishatu, Hadiza.Allah kuma ya albarkace shi da ‘ya’ya da dama; a cikinsu akwai Captain Muhammad Bala Shagari mai ritaya da Aminu Shehu Shagari.
Alhaji Shehu Shagari, tsohon shugaban Nijeriya, tsohon dan siyasa, Turakin Sokoto, Ochiebuzo na Ogbaland, wato Ezediale na Aboucha, Baba Korede na Ado Ekiti, sannan kuma mai lambar girma ta Grand Commander a tarayyar Nijeriya, watau GCFR.
Da fatan Allah Ya inganta lafiya, Ya sa kuma a gama lafiya. Amin.
- Tarihin Audu Bako
An haifi tsohon gwamnan jihar Kano, Marigayi Audo Bako, a barikin ‘yan sanda na Kaduna cikin shekarar 1924. Mahaifinsa dan sanda ne kuma shi ne Sarkin Sabon Garin Kaduna.
Audu Bako ya yi karatun elemantare a Kaduna, sannan ya tafi Zariya ya yi kwaleji a can. Daga nan ya samu shiga rundunar ‘yan sandan Nijeriya a shekarar 1942.
Da fari Audu Bako ya soma zama malami a kwalejin horas da ‘yan sanda ta Kaduna, sannan a hankali ya rika samun daukaka ta yadda har sai da ya zama mataimakin kwamishina mai kula da yankin Arewa.
An nada Audu Bako a matsayin gwamnan Kano da kakinsa na dan sanda a shekarar 1967 bayan an yi wannan mummunan juyin mulki na shekara ta 1966.
Tun da hawansa sai ya dukufa wajen inganta kananun hukumomi da kuma samar da kyakkyawar hurda tsakanin gwamnati da sarakuna da kuma talakawan nasa duk kuwa da kasancewarshi shugaba da kakin sarki.
Audu Bako ne gwamnan da ya gina kusan daukacin manyan gine-ginen birnin Kano. Misali, shi ne ya gina sakatariyar Audu Bako bakidayanta wadda ko a yanzu ya na da wuya a samu wani mahaluki da zai yi irin wannan gagarumin aiki.
Baya da haka, ya gina kwalejin aikin gona a Dambatta wadda a ka sanyawa sunansa. Haka kuma, Audu Bako ne gwamnan Kano na farko da ya soma yunkurin daukaka darajar ‘ya’ya mata ta hanyar tsara mu su hanyoyin samun ilimin zamani daidai da koyarwar Shehu Usmanu Danfodiyo.
Sannan a zamanin mulkinsa ne a ka soma tsara hanyoyin samun kudin shiga daga baki masu yawon bude ido. A shekarar 1969 Audu Bako ya soma gina madatsar ruwa ta Bagauda, domin samar da ruwan noman rani a Kadawa.
Daga shekarar 1970 zuwa 1973 gwamnatinsa ta gina babban madatsar ruwa ta Tiga bisa burin haɓaka noman rani da yawon bude ido.
A na yiwa Audu Bako lakabi da ‘Uban Noman Kano’ saboda manyan madatsan na ruwa daya gina a fadin jihar Kano.
Audu Bako ya yi ritaya a shekarar 1975 bayan juyin mulkin da ya kawo karshen rasuwar Janar Murtala da a ka shirya wanda bai samu nasara ba, sannan ya soma aikin noma a Sokoto.
A shekarar 190 Allah Ya yiwa Audu Bako rasuwa, kuma har gobe shi abin tunawa ne duba da manyan gine-ginen daya yi a Kano.