Connect with us

KASASHEN WAJE

Taron Birnin Tehran Kan Makkomar Idlib Ya Tashi Baram-baram

Published

on

Taron da shugabannin kasashen Rasha, Iran da kuma Turkiyya suka gudanar jiya juma’a domin fayyace makomar yankin Idlib wanda shi ne tungar karshe ta ‘yan tawayen Syria ya tashi baram-baram ba tare da cimma wata matsaya ba.
Da farko dai shugaba Racep Erdogan na Turkiyya ya bukaci Syria da kawayenta su amince da wani shirin tsagaita wuta domin kaucewa kai farmakin karshe a kan ‘yan tawaye da ke yankin, to sai dai shugaba Bladimir Putin ya ce ba ta yadda za a amince da wani shirin tsagaita wuta domin kuma ba wakilan ‘yan tawaye a taron na jiya.
Manzon musamman na MMD a game da rikicin Syria Staffan de Mistura, ya gabatar da wani shiri da ya tanadi janyewar ‘yan ta’adda da ke da nasaba da kungiyar Alka’ida daga manyan birane da kuma yankunan fararen hula a lardin na Idlib, domin ganin cewa Syria da kawayenta ba su kaddamar da farmaki a kansu ba.

Advertisement

labarai