Ibrahim Ibrahim" />

Taron Gwamnonin Arewa: Ba Girin Girin Ba Dai Ta Yi Mai, In Ji Matasa

Taron Gwamnonin Arewa

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa 19, karkashin jagorancin Alhaji Nastura Ashir Shereef, sun bayyana taron da kungiyar Gwamnonin Arewa suka gudanar tare da Sarakunan Arewa kwanan nan a Kaduna, a matsayin wani zama da ya yi hannun riga da muradun jama’ar yankin Arewa.

 

Matasan sun bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da suka kira wanda ya gudana a Gidan tarihi na Arewa House dake Garin Kaduna.

 

Matasan sun bayyana cewa babban abin mamaki ne da takaici a taron Gwamnonin Arewa, inda gaba daya basu yi magana akan matsalar da ke addabar yankin ba, musamman na tabarbarewar tsaro da garkuwa da mutane, sai kawai suka bige da surutu akan maganar Zanga-Zangar Endsars da batun Soshiyal Midiya.

 

A cewarsu, “Irin wadannan halaye da Gwamnonin Arewa suke nunawa shi ne ya ke sanyawa ake wulakanta ‘yan Arewa musanman a kudancin kasar nan, ake daukar ‘yan Arewa a matsayin wawaye marasa alkibla”.

 

Gammayyar kungiyoyin Matasan na Arewa sun kalubalanci Gwamnonin na Arewa da yin koyi da Gwamnan Jihar Ribas Wike, wanda ya fito fili ya la’anci kungiyar Tsagerun Inyamurai IPOP, ya shelanta haramta ayyukan su gaba daya a Jihar Ribas.

 

Kungiyoyin Matasan na Arewa, sun bayyana cewa, har yanzu Gwamnonin yankin Arewar basu kamo hanyar shawo kan matsalar tsaron dake addaban yankin ba, musamman idan akayi la’akari da yadda kawunan Gwamnonin ya rarrrabu wajen dabarun dakile ‘yan ta’addan. Saboda a cewarsu, misali, da zarar Gwamnan Jihar katsina ya sami nasarar korar ‘yan ta’addan daga jiharsa, sai su koma Jihar Sokoto, idan na Sokoto ya sami nasarar korar su, sai su koma Jihar Zamfara. Saboda babu wani matakin hadin kai da Gwamnonin suka dauka a tsakaninsu.

 

Daga karshe matasan na Arewa sun shawarci Gwamnonin Arewa da cewa lokaci ya yi da zasu mayar da hankulansu waje daya domin gyaran matsalolin da ke addabar yankinsu, wajen ganin su hada kawunan su wuri guda domin kai wa ga nasarar da ake nema.  A cewarsu.

Exit mobile version