Taron JKS Da Jam’Iyyun Kasa Da Kasa Wani Sabon Salo Ne Na Karfafa Cudanya, In Ji Jami’in Sudan

Daga CRI Hausa

Babban sakataren jam’iyyar Umma ta kasar Sudan Al-Wathiq Mohamed Ahmed Al-Birair, ya ce taron tattaunawa tsakanin JKS da jam’iyyu daban daban na sassan duniya, wani sabon mataki ne irin sa na farko, dake da nufin karfafa cudanya tsakanin Sin da sauran kasashen duniya.

Ahmed Al-Birair yana mai cewa jam’iyyar Umma za ta shiga a dama da ita, a taron hadakar jam’iyyun da zai gudana yau Talata ta kafar bidiyo. Daga nan sai ya gabatar da fatan alherinsa ga JKS. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version