Daga Idris Umar Zariya
A cikin makon da ya gabata ne fitacciyar kungiyar nan ta matasa da take fafutukar kawo cigaban al’ummar garin Tafa, wacce ake kira TYDA, wato ‘Tafa Youth Debelopment Association’ ta gudanar da taro kuma taron ya yi armashi.
Wakilin LEADERSHIP A YAU na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka sami halartar taron kuma ya samo tsarabar a wajen taron.
Taron an gudanar da shine a filin makaranta firamar dake cikin garin Tafa a karamar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Manyan mutane ne suka sami damar halattar taro da suka hada da limamai da sarakuna da yan siyasa da yan kasuwa da shuwagabannin kungiyoyi masu zaman Kansu dake ciki da wajen Garin Tafan.
Bayan an bude taro da addu’a ne sai shugaban kungiyar Comrade Idris ya gabatar da jawabin bude daro da karbar many an baki da makasudin gaoyyatar jama’ar a takaice.
Bayan Comrade Idris shugaban kungiyar yayi wa dubban jama’ar da suka sami zuwa taron barka da zuwansu wajen taron ne ya fadidi dalilin shirya taro yace yadda za a baiwa matasa gudummawa a bangare matsalar shaye-shaye a Garin Tafa yace bisa hakane kungiyar ta gaiyato bangarori daban-daban da zasu iya taka rawa a wajen bayar da shawara.
Banyan jawabin shugabanne kungiyarne sai aka baiwa baki damar tofa albarkacin bakinsu akan hanyar da za a magance matsalar lalacewar matasa maza da mata a Garin Tafa.
Alhaji Abdul-Kareem Suleman shine Yariman Jere yana daga cikin manyan baki shima ya gabatar da jawabisa mai tsawon gaske tare da ma’ana ga rayuwar matasa.
Yariman Jeren yayi kira ne da bubban murya akan matasa da suji tsoron Allah su kauracewa shan duk wani abu da zai rinka gusar masu da hankali yace, mafi yawan lafika ba a aikatasu face sai hankali ya gushe a bangare guda kuma yayi kira ne ga iyaye da su rinks Jan yaransu a jika yace hakan ne zai sanya su gane halin da yaransu yake ciki dan daukar mataki mataki mai ma’ana.
Karshe Jariman ya Ja hankalin gwnati dasu yi iya yinsu wajen samawa matasa hanyar da zasu koyi sana’ar hannu da zai cire masu gangen kayan wani balle har su dauka ba tare da izinin mai Shiba.
Kuma ya jinjinawa kungiyar bisa namijin kokarin da sukeyi dare da rana don haka nema yayi alkawarin baiwa kungiyar tallafi don gudanar da wasu aiyuka nasu yayi fatan Allah ya maida Kowa gida lafiya.
Shima wakilin JNI liman Abuakar Tafa shima ya farane da mika godiya ga Allah da ya bashi damar halattar wannan taro kuma ya janyo ayoyi daga cikin lattafin Allah da hadisai akan kyautata tarbiyar mutane yace yin hakan jihadine bubba don haka ne yace a shirye suke don baiwa kungiyar goyan baya kuma yayi fatan yadda aka fara lafiya Allah yasa a tashi lafiya.
Shima takwaransa daga CAN Rabaran Dauda Jarumi shima ya goyi bayan magana sanya tsoron Allah a dukkan aiyuka yace haka shine hanyar tsira a gobe kiyama.
Shima mataimakin kwamishinan yan Sanda na shiyar Tafa malam Umar Faruk, shiko yaja hankalin masu shan kwayar ne har da masu sayarwa dasu tattara inasu-inasu su bar Garin Tafa kafin aiki ya kawo kansu.
Karshe ya yabawa kungiyar matasa bisa hangen nesansu na shirya irin wannan taro yayi fatan Alheri ga jama’ar da suka sami halattar taron.
Garkuwan Garin Tafa Muhammad Ndama tsohon DPO mai ritaya na Garin Tafa shima kira yayi akan duk wani mai sanya kaki da yaji tsoron Allah a yayin da yake gudanar da aikinsa yace hakan shi zai sanya Allah ya tsareshi daga dukkan sheri yace da ikon Allah zasu bayar da hadin kai wajen kare rayuwar mutanen garin Tafa.
Honorabul Nuhu Gora shine dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kagarko shiko ya gabatar da jawabine mai tsaro wadda ya shafi yabo ga dukkan jama’ar da suka gabatar da kasidu kuma ya amsa dukkan tabbayoyin da suka fito daga bakin mahallta taron da suka shafeshi kai tsaye musamman al’amuran siyasa karamar hukumar hukumarsa tare da daukan alkawarin kawo gyara a duk inda aka sami tseko.
Shima shugan karamar hukumar kakarko honorabul honorabul Audu Rabo shima yaji Dadin yadda matasa suka shirya taron kuma tuni yayi alkawarin bayar da goyan baya ga matasa wajen kawar da duk wata matsalar dake damun matasa a soyasance ya kuma yi fatan Allah ya koma da Kowa gida lafiya.
Alhaji Ibrahim Musa Dan kwairo na daya daga cikin Yan kasuwan dake kishin garin Tafa ta bangaren samawa matasa abin yi
Da yake jawabin sa wajen taron ya farane da mika godiya ga Allah uban Gigi madaukakin sarki kana yayi jinjina ga kungiyan matasar garin Tafa bisa himma da kishi da suke nunawa a kowani lokaci
Alhaji Ibrahimi ya baiyyana matasan a matsayin masu kishin gari Tafa yace hakan ake so .
Da kuma yake bayar da shawara ga matasan Sai yace wajibine matashi ya nemi sana’ar yi komin kan-kan tarta domin hakane zaisa zuciyarsa ta tsaya waje guda ba tare da Sanya zuciyarsa ga abin da ba nashiba.
Bisa haka ne a halin yanzu ya siyawa matasan Baro kusan guda 3000 don su rinka turawa suna samun taro da sisi don su rufawa kansu asiri ba saisunje sun taba kayan waniba kuma sukan ajemin kadan daga cikin abinda suka samune a duk wata.
Alhaji Ibrahim ya kara da cewa yanzu haka akwai shago na dinki Wanda ya bude domin kawai samawa matasa abin yi don kaucewa zaman banza.
Karshe ne Alhaji Ibrahimi yayi alkawarin baiwa matasa guraben aiki a kamfanoninsa da an kammala aikin su da yardar Allah ya kuma bayar da taimako mai tsoka ga kungiyan don ci gabanta.
Shugaban kungiyar Comrede a lokacin da yake zantawa da manema labari yayin kammala taron ya baiyyana makasudin gudanar da wanna taron da yayi tasiri ga jamakar garin Tafa ciki da wajenta.
Shugaban yace wannan taro an shirya shine bisa dalilai guda uku,na farko shine kungiyar cigaban garin Tafa ta hango wasu kalubale da matasa ke fuskanta a bangaren lalacewar tarbiya.
Na biyu kungiyar ci gaban garin Tafa ta hango wasu hanyoyi da za a iya mfani dasu wajen taimakawa wasu marasa karfi wajen Neman karatu ko sana’ar hannu da zasu iya rike kansu da kansu maimakon yawon banza da shaye-shayi a cikin gari.
Sai na Uku baiwa masu hannu da shuni dama don bayar da gudummawarsu don cigaban kungiyar.
Karshene shugaban ya baiyyana nasarori da kungiyar take samu lokaci bayan lokaci harya bayar da misali da Kansas yace yanzu ya kusan hada digirnsa na Uku a jami’a karkashin shawarwarin da wannan kungiyar take baiwa matasa.
Ya baiyyana zagi da tsegumi a matsayin kalubare da suke fuskanta a gurin masu amfana da rashin tarbiya a garin nasu,amma yace hakan bazai sasu su dena kira akan gyaran tarbiyaba.
Alhaji sama’ila Adamu Barwan Kano shine Uban taro kuma shi yayi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.