Abdulrazak Yahuza Jere" />

Taron NIS Ya Ayyana Bunkasa Amfani Da Fasahar Zamani A Ayyukan Hukumar

An kammala babban taron shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Qasa na shekarar 2019 a Benin, Babban Birnin Jihar Edo na tsawon kwana hudu inda aka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi inganta ayyukan hukumar da kuma tabbatar da dorewar nasarorin da hukumar ke samu bisa gyaran fuskar da take aiwatarwa.
Sanarwar manema labaru da hukumar ta fitar a karshen taron a karshen mako, ta bayyana cewa hukumar ta sha damarar ci gaba da ayyukanta cikin kwazo domin inganta tsaron kasa da karfafa matakan bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin kasa da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba ta hanyar janyo hankulan masu zuba jari daga waje, da masu yawon bude ido, da masu kirkirar fasahohi da kuma kwararowar baki masu fikira zuwa cikin kasa.
Taron ya kuma bayyana cewa NIS ta yi alkawarin yin dukkan wani abu mai yiwuwa wajen kare mutunci da kimar kasar nan tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana cikin ayyukanta kamar yadda yake kunshe a manufofin gwamnatin tarayya na yaki da cin hanci da rasawa.
Wazakali, taron ya cimma matsayar cewa bisa tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi na saukaka yanayin hada-hadar kasuwanci, NIS za ta ci gaba da lalubo hanyoyin amfani da kayan fasaha na zamani wajen tsaurara tsaron iyakokin kasa, da nuna kwarewa ta fuskar ba da izinin shiga kasa (biza), da bayar da fasfon tafiye-tafiyen kasashen waje da sauran takardu makamanta, domin rage cunkoson mu’amala da kuma samun biyan bukatar abokan hulda a kan lokaci.
Wakazalika, hukumar ta ce za ta ci gaba da karfafa horas da jami’anta manya da kanana domin inganta kwazonsu na aiki, da ilimi, da nuna kwarewa ta zamani wajen kula da al’amuran bakin da ke shigowa cikin kasa, da kara kyautata wa jami’an hukumar ciki har da kara yawan hakkokin fansho ga wandanda suka yi ritaya domin karfafa gwiwar yin aiki tukuru a tsakanin jami’an.
Bugu da kari, taron ya cimma matsayar cewa hukumar za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da hukumomin da suka dace da sauran masu ruwa da tsaki domin samun goyon bayan da take bukata ta fuskar cimma kudororin da ta sanya a gaba.
Haka nan, taron ya yanke shawarar cewa a kokarin da NIS ke yi wajen samun nasarar dukkan gyaran fuskar da take yi, hukumar za ta kara matsa wa gwamnatin tarayya lamba a kan ta kara yawan kudin da take ba ta, musamman ma gwamnatin ta rika sahale mata wani kaso daga cikin kudaden shiga da take samarwa.

Bisa wadannan muhimman batutuwa da taron ya bijiro da su, hukumar ta NIS ta yi amannar cewa daukan kwararan matakai na ci gaba da kwarya-kwaryar gyaran fuska domin magance kalubalen da ake fuskanta wajen zamanantar da aikin shige da fice, ya zama wajibi don samun nasarar cin gajiyar ayyukan hukumar kamar yadda ya kamata.
Hukumar ta kuma ce za ta kara mayar da hankali wajen amfani da kayan kimiyya da fasaha na zamani a aikace-aikacenta, da yin kawancen aiki da ma’aikatu da hukumomin da suka dace na cikin gida da waje, da inganta kwazon aikin jami’anta ta kyautata hulda da masu ruwa da tsaki domin samun nasarar sauke nauyin da aka dora mata.
Daga bisani, sanarwar bayan taron ta ce hukumar ta NIS tana mika godiya ta musamman ga Shugaban Qasa Muhammadu Buhari, da Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola, bisa goyon bayan da suke bai wa hukumar wajen samun nasarar gyaran fuskar da take yi a aikace-aikacenta.
Haka nan, ta yi godiya ga Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki bisa karamcin da ya nuna wa hukumar wajen karbar bakuncin babban taron nata na shekarar 2019, kana ta jinjina wa daukacin al’ummar jihar bisa karar da suka nuna mata har a ka samu nasarar gudanar da taron.

Exit mobile version