Jamila Umar Tanko" />

Taron Rana Marubuta Hausa Ta Duniya: Bashir Tofa Da Farfesoshi Malumfashi, Dangambo, Muktar Sun Jagoranci Rana Ta Biyu

Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya Rana ta biyu 17 Ga Maris, 2018 an fara shi da misalin karfe 9:00 na safe a dakin taro na tsohon gidan gwamnatin jihar Katsina.

Furofesa Ibrahim Malumfashi ya yi jawabi a kan rubutun zube, inda ya yi kira ga marubuta masu rubutun zube da su dinga yin bincike sosai kafin su yi rubutu.

Mawaka daban-daban sun cashe, sannan a ka kira tsohon dan takarar shugaban kasa a Jamhuriya ta Uku, Alhaji Bashir Usman Tofa, inda shi ma marubuci ne, wanda Alhaji Ibrahim Kurawa, ya wakilta.

Tofa ya ce, kididdiga ta nuna cewa, Hausawa sun kai adadi miliyan 150 a duniya. Don haka ya wajaba marubuta su inganta rubutu.

Mai jawabi na gaba shi ne, Mai Martaba Sarkin Katsina, wanda Dagacin Katsina ya wakilta, inda yayi godiya kan yadda a ka zabi Katsina a ka gudanar da taro gami da fatan alkhairi.

Farfesa Isa Muktar shi ma ya yi bayani a kan salon rubutu, ya na mai cewa, salo ya na da muhimmanci, kuma ya na da nau’i daban-daban. Don haka marubuta su dinga rubutu da daidatacciyar Hausa.

Farfesa Dangambo kuma ya yi bayani a kan marubuta su fahimci muhimmancin salo su dinga daukar salo mai jan hankali ta yadda ba zai ginshi  masu karatu ba.

 

Exit mobile version