Taron Tunawa Da Cikar Rimi Shekara 10 Da Rasuwa Zai Sha Bamban

Guda daga cikin makusanta kuma masoyi na hakika ga Maragayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi (Limamin Canji), Alhaji Sani Abdullahi Kwalli, wanda ya assasa fara aiwatar da addu’a tare da bikin tunawa da Marigayin, Dakta Abubakar Rimi a duk shekara, wanda kuma shi ne aka nada a matsayin Babban Sakatare na wannan addu’ar tunawa da Limamin Canjin, ya bayyana cewa, bikin tunawa da tsohon Gwamnan Farar Hula a Kano kuma tsohon Ministan Sadarwa a Nijeriya, zai sha bam-bam da wanda aka sha gudanarwa a baya, wanda a ka fara yi tun a shekarar 2011, kamar dai yadda ya bayyana a wata ganawarsa da ya yi da mane ma labarai a Kano, ranar Larabar da ta gabata.

Kwalli ya kara da cewa, Dakta Abubakar Rimi wanda ya kafa Gidan Jaridar TRIUMPH da Gidan Telabijin na ARTB da Hukumar Yada Ilimin Manya  (AGENCY FOR MASS EDUCATION) da Hukmar NARDA da kuma kirkirar ranar Ma’aikata, wacce a halin yanzu ta zama ta kasa baki-daya.

Har ila yau, a cewar tasa akwai batun kai hasken  wutar lantarki Kananan Hukumomin Jihar Kano da Jigawa, a lokacin suna matsayin jiha guda. Kazalika, kasancewar garuruwa uku ne kacal ke da hasken wutar lantarki a Kano da Jigawa, sai da Limamin Canji ya kai wannan haske na wutar ta lantarki lungu da sako na fadin Kano da jigawa, ya kuma tafi tare da ‘yan hamayyar Gwamnatin tasa, wadanda suka cancanta yake da kuma yakinin cewa za su bayar da gudunmawa wajen gina Kano, ba tare da nuna wani banbanci na siyasa ba, da sauran ayyuka a fannin lafiya, ilimi, noma, kasuwanci da kuma gyara al’adun a’lummar Kano ta hanyar ba da umarni ga Ma’aikatan Asibiti mata su yi irin shigar da ta dace da al’adunsu da kuma addininsu, sabanin shiga irin wacce suka gada daga wurin Turawan Mulkin Mallaka, tare da hana koyar da Ilimin Kiristanci A Kano da sauran wasu ayyukan da ba za su iya lissafuwa ba, in ji Kwalli.

“Wadannan abubuwa ne suka sanya ake yin wannan taron addu’a duk shekara da kuma ta yau da kullum da ake yi Marigayin da iyayanmu da kuma sauran al`umma wandda suka riga mu zuwa gidan gaskiya. Sannan, ake yin taro da kuma bikin karanto ayyukan alhairi wadanda Marigayi Abubakar Rimi ya yi a cikin shekaru uku rak, domin na baya su ji su kuma yi koyi da shi.”

Daga nan ne, sai kuma Alhaji Sani Kwallin ya bayyana cewa, wannan taron addu’a da aka saba yi, ko shakka babu zai sha bam-bam da na baya, domin kuwa za a gayyato manya-manyan masana daga Jami’o’i da sauran makusantansa da kuma `yan  Jaridun da suka samu damar zantawa da shi a lokacin da yana raye, domin sake fitowa da cikakken tarihinsa da kuma ayyukan alhairan da ya shuka, musamman a bangaren gwamnati da kuma siyasa.

Har wa yau, wannan taron addu’a da za a yi shi ne na cika shekaru 10 cif da rasuwar Marigayin, wanda ya yi mulki a Jamiyyar PRP daga shekarar 1979 zuwa 1981, inda ya baiwa Marigayi  Alhaji Audu  Dawakin Tofa wannan mulki, domin neman zango na biyu a matsayinsa na jagoran yan Santsi  masu ra`ayin tallafawa talaka da kin yadda da rashin gaskiya.

A karshe kuma Sani Kwalli, ya bayyana farin cikinsa da irin nasarorin da suka samu a wadannan shekaru na tarurrukan addu`o’in Marigayin Rimi, duk da irin kalubalen da suka samu na rashin fahimta ga wasu, amma yanzu gashi ana kokarin yin koyi da su. Sannan a cewar tasa, wannan taro na kowa da kowa ne da kuma Gwamnatin Jihar Kano da ma ta Tarayya baki-daya.

Exit mobile version