Abubakar Abba" />

An Tarwatsa Gungun ’Yan Fashi Da Kwararren Likita Ke Jagoranta A Abuja

Rundunar ‘yan sanda dake Birnin Tarayyar Abuja sun tarwatsa gungun ‘yan fashi da makamai wadanda aka yi zargin wani likita da da kuma wani mai asibitin   Bital Care dake anguwar Kubwa, a cikin garin mai suna Dakta Ola Jimade ne ke jagorantar gungun na ‘yan fashin.

An ruwaito cewar an ‘yan sandan sun cafke mutane biyar daga cikin wadanda ake zargin inda kuma shi Jimade ya arce.

Wadanda aka cafke a  sune, Sunday Okhomode, da aka fi sani Sunny-Momoh dan shekara 30 da Meshak James dan shekara 23 da wani mai sana’ar yin fenti   Amusu Koku dan shekara 28 da  Kunle Obajemi dan shekara 49 shima mai sana’ar yin fenti da Suleiman Isa dan shekara 26 mai sana’ar yin kira.

Kwamishinan ya sanar da hakan ne a lokacin da ya yi baje kolin wadanda ake zargin a ranar Talatar data gabata a Abuja.

Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja Sadik Bello ya bayyana cewar an cafko ‘yan fashin ne bayan da aka kawo rundunar rahoto bayan sunyi fashi a wani gida dake anguwar Maitama, a cikin watan Nuwambar shekarar da ta gabata.

Acewar sa, an samu mota kirar BMW D6 SUB da gwalagwalai da sauran kaya masu tsada na miliyoyin naira a gun wadanda ake zargin.

Bello yaci gaba da cewa, an cafko wadanda ake zargin ne sakamakon rahoton da riski rundunar, inda jami’an ‘yan sanda masu yakar ‘yan fashi da makamai suka bazama, suka samu kuma cafko mutum biyar daga cikin wadanda ake zargin tare da kwato mota kirar SUB.

Kwamishinan ya kara da cewa, “ a lokacin da aka gudanar da bincike, an gano motoci guda biyar wadanda tuni an wadanda ake zargin, sun canza masu fenti kuma daga cikin motocin, guda hudu masu su sunzo sun nuna motocin su ne da ‘yan fashi suka kwace a garin na Abuja.

Ya bayyana cewar,“ an kuma samu wadanda ake zargin da da kananan bindigogi da kwabsar albarusai guda takwas da tsumman rufe fuska da aka boye su a ofishin Dakta Ola Solomon Jimade, a lokacin da aka je bincike.

Bello ya bayyana cewar, ” ana ci gabada gudanar da bincike don gano sauran motocin da kuma cafko sauran da ake zargi.”

Yace, “duk wanda ya san inda Ola Jimade yake wanda akece ya fito ne daga yankin Yagba ta yamma a cikin jihar Kogi, ya gaggauta sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa, don a cafko shi.

Daya daga cikin masu yin fenti da ake zargi mai suna Koku, ya shedawa manema labarai  cewa Jimade ne yazo gunsa ya kuma sashi ya yiwa motar kirar BMW SUB fenti a cikin watan  Disambar shekarar  2017, kuma Jimade ya kara kawo masa wata motar a cikin watan Janairu wannan shekarar, inda ya biya shi kudi naira 60,000.

Shima dayan mai sana’ar ta fenti  Obajinmi, ya shedawa manema labarai cewar, “ya kware wajen sana’ar canza fentin motoci da canza lambar injinonin mota da gaban mota, ya kara da cewar, ya hadu da Daktan ne a shekarar data gabata.“

Ya yi ikirarin cewar “Daktan ya same ni yace inyi masa sitikar mota, amma ni ban san motar sata za’a sanyawa ba.”

Shi kuwa Isa ya amince da sayen gwalagwalan na sata daga gun Jimade akan naira miliyan 1.7.

A wata sabuwa kuwa, ‘yan sanda sunce sun cafko wani mai suna Destiny Abang dan shekara 32 da ya fito daga yankin Boka dake yammacin jihar Cross Riber, a lokacin da yake kokarin satar mota a anguwar Garki ta 8 dake Abuja.

Acewar kwamishinan ‘yan sandan a lokacin da aka gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewar ya saci motocin ya kaisu yankin Boki a cikin jihar Cross Riber, wadanda dukkan su ya sayar dasu.

A binciken da aka gudanar, an samu nasarar gano motoci guda sha uku da mota kirar Mazda 323 mai kala  bulu da jar mota kirar Bolkswagen Golf 3 da Mazda 323 mai kalar toka da Toyota mai kalar toka.

Bello yace, an kuma samu mota kirar Highlander mai kalar toka da Mazda 323 ma kalar ja da Toyota Corolla mai kalar bula da sauran motoci.

 

Exit mobile version