Tashar Freedom Na Dutse Ta Yi Jimamin Mutuwar Ma’aikacinta

Gidan rediyon Freedoom da ke Dutse a jihar Jigawa ta rasa daya daga cikin ma’aikacinta mai suna Malam Abdulkarim Darmanawa. Ya rasu ne a ranar Laraba 12 ga watan Yuni sakamakon gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita. Kamar yadda shugaban gidan rediyon Malam Bashir Atuwa ya tabbatar.

A wata sanarwa da Alhaji Bashir Isma’il, shugaban sashen kudi da gudanarwa na rediyon ya fitar, ya bayyana cewa; gidan rediyon ta rasa zakakuri kuma jajirtaccen dan jarida. Inda suka tabbatar da cewa; ba za su taba mantawa da mutuwarsa ba domin sun kadu da rasuwarsa. Kuma gidan rediyon ba za su manta da irin gudummawar da ya bai wa gidan ba wajen ganin ci gaban tashar.

Ya ce; hatta al’umma sun yi rashin Darmanawa, ya ce musamman masu sauraren shirinsa na Hausa kamar irin ‘Barka Da Hantsi’ ‘Good morning Jigawa’, ‘Yau da Gobe’, da ‘Hasken Makaranta’.

Majiyar labarinmu ya labarto cewa; lokacin da ya isa gidan rediyon Freedom din a ranar Asabar ya tarar da dimbin jama’a da suka zo domin mika ta’aziyyarsu.

Gidan rediyon Freedom da ke dutse, babban hedikwatar rediyon yana garin Kano ne.

Exit mobile version