Connect with us

MANYAN LABARAI

Tashar ’Yankaba Na Neman Zama Kasuwar Miyagon Kwayoyi A Kano

Published

on

 

Rahotanni daga tashar motar ’Yankaba sun tabbatar da cewa, tashar motar da ke kan titin Hadeja Road a Kano na neman zama wani sansani na cinikin miyagon kwayoyi, domin kuwa yanzu haka masu cinikin kodin da makamantansu sun maida wannan tasha wajen cin karensu babu babbaka. Don haka ne mutanen da ke wannan yanki ke neman hukumomi da su dauki matakai na kawar da wannan matsala ta cinikin miyagun kwayoyi a tashar ta ’Yankaba.

Shugaban tashar motar ta ’Yankaba, Alhaji Iliyasu Ayuba ’Yankaba, ya bayyana damuwarsa a kan yadda wasu matasa marasa kishin al’umma kuma marasa kishin zuci da kasarsu su ke neman gurbata tarbiyar al’umma a yankin. Don haka ya ce, su na neman ganin matasa sun zama nagari a koyaushe, sai ya yi kira a gare su da cewa, yakamata su nemi sana’a tagari, wacce doka ta yarda da ita maimakon tallen miyagun kwayoyi da kuma ta’ammali da su.

Haka kuma kan wannan tabarbarewa da ta samu wasu matasa da ke neman mayar da tashar ’Yankaba kasuwar cinikin miyagun kwayoyi ta sanya shugaban hukumar hana fatauci da shan miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano (NDLEA Kano), Malam Hamza Umar, ya ce, hukumarsa ba za ta bar dillalai da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi su cigaba da wannan danyen aiki na karya doka ba.

Don haka duk inda su ke hukumar NDLEA na daukar mataki a kansu kuma su na maraba da duk wani wanda ya ga irin wannan danyen aiki da idon hukumar bai gano ba, da su kai rahoto gare ta, domin tabbas za ta dauki mataki a ko ina ne.

Ita dai tashar motar ’Yankaba na da kasuwa da ta yi suna wajen sayar da kayan miya da kayan marmari, kamar yadda wakilunmu a Kano ya ruwaito ma na.

 

Advertisement

labarai