Tashin-tashinar Taron Jigon Sayawa: Yadda Aka Farmaki Sarakunan Bauchi Da Dass

Sayawa

 

Daga Khalid Idris Doya,

A tsakanin ranakun 30 da 31 na watan Disamban 2021 ne aka ware domin tunawa da wani dan gwagwarmayar nema wa Sayawa ‘yanci kuma tauraron al’ummar Sayawa, wato Baba Peter Gonto a cikin karamar hukumar Bogoro, sai dai taron bai samu gudanuwa cikin armashi ba kana ya bar baya da kura.

Wakilinmu ya labarto cewa, tun kafin zuwan ranakun taron, wasu kungiyoyin matasan Sayawa da wasu dattawa sun nuna ra’ayin amincewarsu da yin taron bisa hujjar cewa an ware wasu muhimman mutane ba tare da gayyatarsu ba, don haka ne suka shelanta cewa ba za su bari a yi wannan taron ba.

A gefe guda kuma masu shirya taron da suke samun goyon bayan shugaban hukumar kula da asusun tallafa wa manyan makarantu Farfesa Sulaiman Bogoro da gwamnatin Jihar Bauchi suka hakikance kan cewa sai an gudanar da taron.

Kodayake, tun ana sauran kwanaki, aka samu wasu rahotonnin da ke cewa, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara ya aika wa hukumomin tsaro wasikar da ke neman kada su bada damar yin  taron bisa barazanar yamutsi da ka iya tasowa.

Har-ila-yau, wakilinmu ya labarto cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata da aka ware domin yin babban taron tunawa da Gonto, wasu fusatattun matasa sun farmaki tawagar Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, da na Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman, inda suka farfasa masa motar da Sarkin Dass ke ciki da kuma lalata motar wucin gadi na Sarkin Bauchi.

Haka kuma matasan sun tarwatsa wajen taron tare da kona dukkanin kayan da aka ware domin gudanar taron da suka hada da siffiku, kujeru, minbari da sauran muhimman kayan tare da fattatakar wadanda suka halarci wajen taron.

A bisa wannan ne, masarautar Bauchi ta gudanar da wani taron gaggawa a shekaran jiya inda ta dauki matakin yin tir da Allah wadai da harin da aka kai wa Sarakunan biyu tare da kiran gwamnatin tarayya da ta Jihar Bauchi da su gaggauta kafa kwamiti na musamman da za su binciko tare da zakulo wadanda suka kai wa Sarakunan hari a karamar hukumar Bogoro.

Da ya ke karanta wa ‘yan jarida matsayar da masarautar ta cimma, Galadiman Bauchi, Subiyo Ibrahim Sa’idu Jahun, ya misalta wannan lamarin a matsayin aikin rashin hankali, neman tsokana, gami da tada zaune tsare, sai ya nemi gwamnatin tarayya da ta jiha da su kafa kwamiti domin gano wadanda suka fasa wa sarakunan mota.

“Bisa gayyatar da wadanda suka shirya taron suka yi wa sarakunan Bauchi da na Dass domin tunawa da Baba Gonto, wasu bata gari sun tare tawagar Sarakunan inda suka fasa motar Sarkin Dass (Wanda yake ciki) da kuma na Sarkin Bauchi (Wacce take biye da shi a matsyin ta wucin gadi) bisa abin da ya faru, hakan ya jawo sarakunan jiyowa domin guje wa rasa rayuka da dimbin dukiya”.

“Masarautar Bauchi ta yi Allah wadai da wannan harin na dabbanci, neman tsoka, don haka muna kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su kafa kwamiti masu karfi domin gano wadanda suke da alhakin wannan lamarin domin gano ko su waye.”

Masarautar ta ce, Jihar Bauchi na cin gajiyar zaman lafiya da kwanciyar hankali, don haka ba daidai ba ne wasu da basu kishi ko son cigaban jihar su jawo irin wannan lamarin da ka iya haifar da rashin jituwa a tsakanin mazauna.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa, gidajen muhimman mutane 10 tare da kadarorin miliyoyin naira da suka kunshi motoci ne aka kona a yayin wannan rigimar da ta faru sakamakon wannan taron tunawa da Marigayin Baba Peter Gonto a Bogoro.

A sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar ‘yan sanda a Bauchi, SP Ahmed Wakil ya fitar, ya bayyana gidajen wadanda aka kona da suka hada da na Peter Roko, Injiniya Isuwa Galla, Mr. Kura Sang KK, Sarkin Yaki Amos, Mr. Habila Samu Sur, Mr. William Wotni, Mr. Mamaki Ishaya, Sarkin Bogoro Nuhu Tafida, Mr. Luka Maiciki, da na Mr. Gashon Godiya.

SP Ahmed Wakil, ya yi bayanin cewa a sakamakon harin da matasan suka kai ya jawo kona gidaje, farmakan jama’a, rufe wasu manyan hanyoyi da mata da yara suka yi.

Bisa dukkani abubuwan da suka wakana, al’ummar Sayawa (Zaar), sun bai wa gwamnan Bauchi, Sanata Bala Muhammad, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu, da Sarkin Dass hakuri bisa abubuwan da suka faru har suka jawo kai hari wa sarakunan, sun misalta hakan a matsayin abun kaito da takaici.

Shugaban al’ummar Sayawa da suke zaune a kananan hukumomin Bogoro da Tafawa Balewa hadi da sauran wadanda suke zaune a sassa daban-daban na duniya, Injiniya Isuwa Galla, ya ce neman afuwan sarakunan ya zama dole lura da irin barnar da wasu bata gari suka musu tare da baiwa fitaccen mawakin nan Panam Percy Pau hakuri kan kona masa kayan sana’arsa da aka yi a sakamakon wannan taron.

Shugaban, sai ya nemi hukumomin tsaro da su tambayi dan majalisar tarayya, Yakubu Dogara da ya musu bayanin inda ya samu bayanin da suka ce akwai barazanar yatsumi da zai faru muddin aka yi taron, wanda kuma a karshe hakan ya faru.

Isuwa Galla, wanda ke wannan bayanin a taron manema labarai da suka yi a shekaran jiya, ya ce a ranar 24 fa watan Disamban 2021, Hon. Yakubu Dogara ya aike da wasika ga sufeto janar na ‘yan sanda Alkali Baba, inda yake neman hukumomi da su sanya a dage taron bisa barazanar tashin

hankali da ka iya faruwa a sanadiyyar taron.

A cewarsa, babban dan marigayin Baba Peter Goto, a ranar 27 ga watan Disamban shekarar da muka wuce ya aike da wasika ga Gwamnan Bauchi Bala Muhammad da yake neman a amince musu domin gudanar da taron, kana ya ce shugaban karamar hukumar Bogoro da na Tafawa Balewa sun aike da wasika ga kwamishinan ‘yan sandan jihar inda suke tabbatar masa da cewa babu wani barazana don haka ana iya bada izinin yin taron.

“Masu shirya taron da hadin guiwar iyalan mamacin, sun cimma matsayar cewa a yin taron tunawa da Gonto a ranakun 30th da 31st December, 2021, da suka hada da kaddamar da littafi da karrama marigayi Baba Gonto a matsayin tauraro, jigon da ya bar ababen koyi ga Sayawa.

“Sai dai wasu marasa kishi sun yada jita-jitan cewa wai nadin sarauta za a yi a wajen wannan taron wanda hakan ya janyo shakku da fargaba a zukatan jama’a.”

Baba Peter Gonto wada ya mutu a shekarar 2000, ya kasance dan gwagwarmar tabbatar da ‘yancin Sayawa da nema musu cigaba hadi da tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu. Haifaffen dan kauyen Mwari, da aka haifa a shekarar 1882 ya yi rayuwa abun koyi ga su Sayawan wanda suke dakansa a matsayin wani tauraronsu.

Shugaban Zaar, Isuwa Galla sai ya nemi hukumomin tsaro da su tabbatar da zakulo wadanda suka kai wannan harin, sai dai bai tabbatar wa ‘yan jarida ko da wani da aka kashe ba, sai ce hukumomin tsaro ne za su tabbatar da hakan sai dai ya ce a cikin wadanda aka ji wa raunuka da kai wa hari har da dan marigarin wanda masu kai harin suka jikkata da yake amsar kulawar likitoci yanzu haka a Jos.

Dukka a sakamakon wannan, wasu gungun matasa sun yi zanga-zangar neman a tube wa Hon. Yakubu Dogara rawaninsa na Sarautar gargajiya ta Jakadan Bauchi. Matasan masu zanga-zangar a kofar fadar Sarkin Bauchi sun misalta abun da ya faru da Sarkin Bauchi da na Dass a matsayin cin fuska.

 

 

Exit mobile version