Connect with us

MAKALAR YAU

Tasirin Furuci

Published

on

Furuci na da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam, irin rawar da ya ya ke takawa ga zukata da ruhi babu wani abu da ke makamancinsa.
Akwai wani farfesa wanda ya kai kololuwa a ilmi, wata rana ya ziyarci kasar Japan, inda ya hadu da wani masani daga shugabannin addini.
Shugaban addinin ya yi maraba da zuwan farfesan, sai ya gayyace shi shan shayi. Lokacin da shugaban addinin ke kokarin harhada shayi, sai Farfesan ya fara zayyano kwalayen da ya samu a makaranta, da kololuwar iliminshi. Shugaban addinin ya na saurare bai tanka ba, ya yi ta zuba shayi a kofi, har kofin ya cika ya fara zuba kasa. Sai Farfesan ya yi ihu ya ce, “kai wannan wanne irin shugaba ne, ba ka ga kofin ya cika ba ne?”.
Sai shugaban addinin ya ce; “kamar yadda wannan kofin ya cika, idan a ka ci gaba da zuba mai shayi an yi barna kenan, dole sai ya zama ba komi a ciki kafin ya dibi sabon abu.”
Darasin da na ke son a fahimta shi ne cikin furuci wannan shugaban addini ya mayarwa da Farfesan martani. Saboda ya yi ta fadin bajintarshi a fannoni daban daban, sannan kuma a lokaci guda ya zo wurin shugaban addini don karin wani ilmin da bai sani ba. Kun ga kenan Farfesa na bukatar ya gane cewa sai ya cire girman kai, ko kuma tunanin shi wani ne, kafin ya fahimci abun da a ke so ya fahimta.
Fatan baki ne ke furuci wanda kuma kunnuwa ke saurare, don haka ya na da kyau mu san menene ma kalmar furuci?. Amsa; Ba komi ba ne face sauti da ke daukan hankali. Misali idan na ambaci kalmar ‘Doki’, abun da zai zo kwakwalwar mutum shi ne hoton wani dabba swanda aka fi sani da suna doki. Amma ga wanda ba ya jin hausa sai dai kawai ya ji karan fitar iska daga bakina, sannan kuma zai ga motsin bakin amma kwakwalwarshi ba za ta fahimci dabba ake nufi ba. Mafi muhimmanci a furuci shi ne mu fara kokarin fahimtar ma’anar kalma tukunna, sannan mu san me ta ke nufi.
Furuci na daga cikin abubuwa masu hadari ga rayuwar dan Adam. Idan ba ka fahimci me mutum ke son fadi ba, ka yi ma furucinshi bahaguwar fassara nan da nan tsirarun kalmomi za su haifar da mummunan hargitsi.
Matakin farko da ya kamata mu dauka wurin kaucewa rashin fahimta shi ne kar mu yiwa furuci bahagon fahimta, na biyu, kar ka rika yiwa furucin mutane fassarar son rai wanda ba shi su ke nufi ba. Mutumin da ke cikin damuwa (yana neman rigima) zai fassara furucin mutane ba yadda ya dace ba, wanda hakan ba za ta kasance ba da a ce ya na cikin nishadI ne da kwanciyar hankali. Ya na da kyau mu gane, ba zai yiwu ka iya shiga cikin zuciyar mutum ka fahimci hakIkanin abun da ya ke tunani ba, haka nan kar ka yi tsammanin wani zai iya cinkar tunanin da ka ke yi a zuciyarka. Da kanka za ka sarrafa yanayin fahimtarka ga furucin mutane.
Da yawan rikice rikice na afkuwa ne sakamakon rashin fahimtarmu ga furucin mai furuci. Idan da za mu tsaya akan fahimtar cewa furuci fa ba komi ba ne face wani abu wanda ke nuni da ra’ayin wanda ya yi shi da al’amura sun zo cikin saukI.
Da kowanne mutum zai yi tsammanin cewa furucinshi na da ma’ana guda 100, kuma kowa fahimtarsa daban da na wani dangane da furucin lallai da an rika yin taka tsantsan kafin budar baki a yi magana.
Ga mutumin da ya ke kurma babu illar da furuci zai yi mai. Saboda furuci sam babu samuwarshi a rayuwar kurame. Domin ba za su iya karantar motsin labba ba. Kun ga kenan, mutum ne ya ke tarbiyyantar da kanshi muhimmancin furuci wanda a wurin wasu ‘yan adam din (kurame) sam ma babu shi. Kamar da za a jefa dutse ya fado saman kan mutum ba, ka ga kowanne mutum idan aka jefe shi da dutse sai ya ji saukanshi a jikinshi. Tasirin furuci ya dogara ne ga mai saurare, ba mai furtawa ko kalmar da a ka furta ba.
Furuci shi ne muhimmin kafar sadarwa a tsakaninmu. Furuci na da ikon sanya mu farin ciki ko bakin ciki, mu zamo mamugunta ko masu tausayi. Ka dan natsu ka yi tunanin yadda a ka yi wani abu (furuci) wanda ba a ganinshi ko a iya taba shi ya ke da matukar tasiri akanmu?.
Furuci tilo bai da wani karfin iko, ba komi bane face iska da ke fitowa daga bakin mai magana. Har sai yayin da furucin ya je ga kwakwalwar mai saurare sai ya samu daraja da karfin iko.
Da wani zai ajiye wuka a saman teburi, sai ka kI daukan wukan, tabbas ba yadda za a yi wukan ta yi ma ka illa. Amma idan ka dauki wukan sai ka bugawa zuciyarka, wanene abun zargi?. Haka furuci ya ke.
Don kawai wani ya nishadantu ya zo ya yi ta feso soki burutsun shi, idan har ka san bai kai ka tanka mi shi ba, mafi muhimmanci shi ne ka rabu da shi ya yi ta fitar da iska daga bakinshi, idan bakin ya gaji da motsi da kanshi zai daina ba don Allah ba. Da ma burinshi shi ne ya bata ma rai.
Kar ka yarda haka nan da rana tsaka, wani ya zo ya yi furucin da zai debe ma farin ciki daga rayuwa. Da zaran ka lura hakan zai faru, ka tuna cewa fa baki ne yayi motsi sai iska ta fito, ba wai lafiyar jikinka a ka taba ba ko tabo a ka yiwa halittarka. Hausawa sun ce sai bango ya tsage kadangare ke iya hawa. Mu hadu mako mai zuwa.
Advertisement

labarai