Connect with us

MATASAN ZAMANI

Tasirin Hanyar Sadarwa Mara Tsari Wajen Yada Labaran karya

Published

on

-Sadarwa Marar Tsari, Ta Na Kasancewa A Gidaje Da kungiyoyi Da Wuraren Addini Da Kasuwanni Da Kuma Sauran Muhallan Zamantakewa Da Rayuwar Al’umma.

Sadarwa wacce ba ta hukuma ba, ko kuma sadarwa marar tsari da ka’ida, (Informal Communications) hanyar sadarwa ce wacce ba ta bin dukkan wata ka’ida da wani tsari na doka. Ta na dogara ne kan masu sarrafa ta kawai.
Sadarwa marar tsari, ta na kasancewa a gidaje da kungiyoyi da wuraren addini da kasuwanni da kuma sauran muhallan zamantakewa da rayuwar al’umma. Sadarwa marar tsari, ta na faruwa ne a yanayin lokutan zamantakewar jama’a da lokacin maganar gulmace-gulmacensu.
Tun daga lokacin da sadarwa marar tsari ta fara bin hanyoyin rashin doka da ka’ida, cikin hanzari ta ke yada duk wani sako ta fannoni daban-daban. Sadarwa marar tsari ta na haddasa karin gishiri da yada jita-jita da labaran karya a cikin kankanin lokaci su zagaya loko da sako ta taba nutsuwa da zaman lafiyar al’umma.
Abubuwan da su ke haddasa yaduwar labaran karya da jita-jita da karin gishiri ya game al’umma ta hanyar sadarwa marar tsari:
Rashin Nutsuwa A Ya Yin Sauraro: Rashin nutsuwa a ya yin sauraron bayani kan sanya mai sauraron bayanin ya zantuttuka ya watsa labaran da ba gaskiya ba ne su yadu a cikin al’umma.
Cukuda Labari Da Ra’ayi Na kashin Kai: A wasu lokutan mai sauraron labari ko wani bayani ya kan karba ya cakuda shi da ra’ayinsa ko manufarsa ta kashin kansa ya yada shi ga al’umma. A wannan yanayi labarai masu cakude da karya da karin gishi su kan yadu cikin kankanin lokaci su game al’umma.
Rashin Doka Da ka’ida: hanyar sadarwa marar tsari, ba ta bin dukkan wani tsarin doka da ka’ida. Wannan dalili ya sanya mai ba da bayani da mai karban bayanin su ke haduwa su yi musayar sakonni a junansu ba tare da wani tunani mai zurfi ba. Wanda hakan ne kuma ya ke kaisu ga gulmace-gulmace da yada jita-jita.

karin Gishiri A Labari: a wasu matsalolin kuma, akan hada gaskiyar labari da karya domin jawo hankalin sauran al’umma. Wannan karin gishiri ya kan boye hakikanin gaskiyar labari sannan kuma jita-jita da karya su yadu.

Hatsaniya: hatsaniya ko rikici a tsakanin mai ba da bayani da mai karban bayanin dalili ne da ke haddasa tattauna bayanan karya ta hanyar sadarwa marar tsari. Saboda rikici ko sabani, bangarorin da ba sa ga maciji da juna su kan maida hankali kan hanyar sadarwa marar tsari su yada karya da bayanai marasa tushe su kalubalanci juna su kara bata dangantakar da ke tsakaninsu.

Amfani Da Kafafen Sadarwa Masu Rauni: idan aka hada da hanya mai tsari, hanyar sadarwa marar tsari ta na da rauni da rashin tsari wanda ke haddasa yaduwar labaran karya.

Rashin Son Sabon Tsari: a wasu lokutan mutane musamman ma ma’aikata ba sa son wani sabon tsari da za a kawo musu kan aikin da su ke yi, a wannan yanayi su kan yada labarai na karya wadanda ba su da tushe balle makama domin kare faruwar sauyin da ake son kawo musu.

Daga wannan bayani, mai karatu zai fahimci cewa hanyar sadarwa marar tsari (Informal Communications) hanya ce mai matukar wahala da hatsari a cikin al’umma.

Advertisement

labarai