Rukayyat Sadauki" />

Tasirin Kafafen Sadarwa Na Zamani Ga Rayuwar Matasa Da Al’umma (I)

Sabbin Kafafen Sadarwa Na Zamani (Social Media) Sun Zame Mana Jiki A Rayuwarmu Ta Yau Da Kullum, Har Ma Sun Zame Mana Kamar Misalin Mashayi Da Kayan Shaye-Shaye In Dai Bai Sha Ba To Babu Nutsuwa Da Zaman Lafiya A Wannan Lokaci.

  A wannan zamani da mu ke ciki, sabbin kafafen sadarwa na zamani da ake kira (Social Media) sun zame mana jiki a rayuwarmu ta yau da kullum. Har ma ya kasance jama’a ba su cika kallonka a matsayin wayayye wanda ya san mai ya ke yi ba idan  har ya kasance ba ka amfani da daya daga cikin shafukan sadarwar na zamani. A wannan zamani ya kasance kowane rukuni na mutane su na amfani da (Social Media), tun daga kan maza har zuwa mata, tun daga yara har matasa da attajirai da ‘yan siyasa da malamai da sarakuna da ‘yan kasuwa da sauran sassan jama’a. Kowa kasance ya na amfani da (Social Media), har ma da kamfanoni duk sun kasance su na amfani da (Social Media) wajen tallata hajojinsu ga al’ummar Duniya.

Akwai dimbin shafukan sadarwa na zamani wadanda su ka hada da; Facebook, Twitter, Snapcht, Instgram, WhatsApp, da sauransu. Sannan kuma shafuka ne masu saurin isar da sako da yaduwa a duniya gaba daya. Akwai abubuwa da dama wadanda (Social Media) ta haifar a cikin al’umma, amma akan wannan rubutu nawa na yau, ni Rukayyat Sadauki zan yi bayani ne kan yadda (Social Media) ta yi tasiri a rayuwar matasa, ma’ana ta yaya (Social Media) ta taba rayuwar matasa?

A yayin amsa wannan tambaya, za mu kalli abun ne ta bangarori guda biyu, wato bangaren amfani da kuma bangaren rashin amfanin (Social Media) a kan rayuwar matasa. Da farko dai akwai bukatar mu fahimci cewa (Social Media) ta rage girman duniya ta hada ta wuri guda ta zama wani dan karamin gari wanda ake kira (Global Billage), ko kuma a ce duniya a tafin hannunka. A yau matasa suna haduwa da tattaunawa da al’umma daga bangarori daban-daban na duniya ta hanyar bude maballin shafukan sadarwa na zamani kawai.

Ta hanyar wannan mu’amala, matasa su na musayar ra’ayi da tafka muhawara a junansu, sannan kuma su na samun bayanai da labarai da kuma samun dumbin damammaki daban-daban. Dadi da kari, (Social Media) ta ba wa matasa damar yin sabbin abokai da kuma samun damar dawo da tsahuwar abotarsu. Ta hanyar (Social Media) matasa kan gano tsaffin abokansu wadanda a baya su ka yi gwagwarmayar karatu tare ta hanyar ganin sunayensu ko sunayen makarantar da su ka yi.

A dai wannan fannin mu’amula, (Social Media) ta na sahun gaba ga kamfanoni da masu saye da sayarwa inda su ke bude shafuka na musamman domin tallata abubuwan da su ke sayarwa ko kuma su Biya matasa wadanda su ka yi suna su tallata musu hajojin nasu su kuma su Biya ladan tallatar da su ka yi musu. Sannan (Social Media) ta na ba wa matasa damar hada kai da zama jakadu kan harkokin kasuwanci da ayyukan jama’a.

Haka zalika, (Social Media) ta na samarwa matasa kudi ta hanyar (Blogging) da ayyukan watsa labarai da harkokin tallace-tallace da sauran ayyukan fasaha. Dimbin matasa masu hazaka da basira su na tara dumbin mabiya su tallata hajojinsu su kuma rarraba a sauran zaurukan shafukan tare da daukar nauyin abubuwan da su ke yadawa domin fata da son ganin ya yadu a duk Duniya.

Sannan kuma (Social Media), wurare ne da matasa su ke amfani da shi wajen bayyana ra’ayinsu da sanar da duniya tunaninsu cikin sauki ba tare da wata shakka ko fargaba ba a kan farashi mai rahusa. Ma’ana hanya ce ta sadarwa cikin sauki abin da ta ke bukata shi ne Netwok din da zai ba ka damar shiga ta yadda za ka yi magana ka aike wa duniya sakon da ka ke son a sani. Haka zalika (Social Media) ta ba da dama ta yadda a sanadiyyarta za ka iya yin aiki a ko’ina ka ke a fadin Duniya. Sannan kungiyoyi daban-daban kan bude zauruka a shafukan sadarwa na zamani su kuma gudanar da tattaunawarsu kai tsaye (Online).

Ta fuskar rashin amfani ko illolin (Social Media) kuwa, akwai matsalar rashin wani tsari ko ka’ida da sanya ido ko wasu dokoki da ya zama wajibi a bi su a duniya. Duba da yadda matasa kan dauki hotuna da bidiyo na wasu hadarurruka ko fyade ko tarzoma da tashin hankali ko kisan kai ko batsa da barna da wani yamutsi su baza a shafukan sadarwa na zamani wadanda kuma su ke haifar da matsalolin kwakwalwa idan suka yawaita tare kuma da sanya fargaba da rudani a zukatan al’umma su rika tunanin cewar duk duniya babu inda ake zaune lafiya. A kullum abin da zai rika zuwa cikin tunanin jama’a shi ne duk duniya ba lafiya, alhalin kuwa a rayuwa ta zahiri kaso 90% cikin dari na duniya lafiya lau ake. Amma a sanadiyar yada hotuna da bidiyo da bayanan tashin hankali da matasa suke yi a (Social Media) sai fargaba da shakku ya mamaye zukatan al’umma.

Exit mobile version