Hauwa Shu’aibu Gaya" />

Tasirin Kunya

Kunya dabi’a ce mai kyau da a ke bukatar kowane mutum; Namiji ko mace, babba ko yaro, su siffantu da ita, domin dabi’a ce da ta kan hana mai ita aikata abubuwa marasa kyau ko munanan aikin da za su sa a daina ganin mutumcin mutum. A takaice dai kunya babu abinda ta ke haifarwa face alkhairi ga mai ita.

Wannan dabi’a ta samu karbuwa ta bangarori biyu manya, wato bangaren al’ada da kuma bangaren addinin Musulunci, inda dukkan bangarorin kewa kunya kallon al’amari mai Kyau.
Hakika kunya na da matukar muhimmanci wajen gudanar da al’amuran rayuwa musamman a wajen mace kasancewar ta jigo wajen bada tarbiyya, sau tari akan danganta ita kunyar gaba ɗayanta da siffofin mata, hakan yasa wasu lokutan idan namiji kunyarsa ta yi yawa ka ji a na “sai ka ce mace”?
To, tunda haka ne ya na da kyau kwarai ko wace mace ta siffatu da wannan dabi’a mai Kyau da muhimmanci kasancewar ita kunya na taimakawa wajen tabbatar da tarbiyya da nutsuwar mutum musamman ita mace.
Tabbas ko ba a fada ba kunya na kara wa mace kyau ta kuma sai mata mutunci a idon mutane, sannan ta kan zamo kariya a gare ta. Abin nufi da kariya a nan shi ne; duk macen da ta ke da kunya, to za ka samu maganarta akwai tsafta a cikinta, za ka same ta da tsare mutunci da kuma gudun aikata abinda za a yi Allah wadai da ita, sannan ta kan yi kokari wajen kin kula wanda zai kawo ma ta matsala a cikin al’amuranta, za ka same ta da nutsuwa da bin al’amura sannu-sannu da kuma kawaici, wanda kusan duk mai kunya ba a raba shi da shi.
Duk wani abu in a ka hada shi da kunya, to ta kan kara wa abin inganci da kyau. Hakan ta sa ko wajen neman auren mace idan ta kasance mai kunya sai ta kara martaba da kima a idon mai neman auren, abokai da danginsa.
Rashin kunya a wajen mace na da illa kwarai, domin ta kan haifar mata da matsaloli masu tarin yawa, domin kunya wata alama ce da ke nuna cewa mace na da kyakkyawar tarbiyya inda rashin ta ke nuna cewa akwai karancin tarbiyya a tare da ita.
To, ya matsayin kunya ya ke a yanzu, msamman a kangaren mata?
Hakikanin gaskiya ko ba a fada ba abu ne da ya ke a bayyane a halin yanzu akwai karancin kunya a tsakanin mutane, musamman matasa, ba ga mazan ba baga matan ba da su a ka fi so su siffatu da wannan dabi’a.
Kadan daga cikin matsalolin da watsi da dabi’ar kunya kan haifar:
Rashin biyayya: muddin idan a ka samu mutum da karancin kunya ko ma ya rasa ta gabadaya, to zai yi wahala ya yi biyayya yadda kamata wajen na gaba da shi, kusan wannan kalubale ne da ya addabi jama’a rashin ganin girman na gaba gare ka.
Lalacewar Tarbiyya: karancin kunya ko rashinta kan taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar tarbiyya, musamman a wajen mace. Mata kusan sun matan cewa kunya wata sifface da a ke son ko wacce mace ta kasance tana da ita, yanzu kusan a iya cewa an yi watsi ko an ajiye kunyar a gefe guda da sunan wayewa.
Ba a ce kar mace ta waye ba; wayewa na da nata hurumin da amfanin domin shi ita rashin wayewar zai sa ka zama ko ki zama kidahuma. Amma me? Ki bi wayewar ta hanyar da ba za ta gurbatar mi ki da rayuwa ko kawar mi ki da wasu halaye da dabi’unki masu kyau da daraja ba. Yi kokari ki tsinci abubuwa masu kyau da wayewar ta zo da shi ki inganta rayuwar ki, kar ki bari wayewar ta bi da ke a duk yadda ta ke so ko kuma duk yadda ta zo.
Ya na da kyau mu gane muhimmanci kunya, mu kuma guji aikata abubuwa na rashin kunya. Ita kunya kamar sinadari ce, domin babu wani abu da za a hada shi da ita ya ki armashi.
Ko laifi mutum ke aikatawa ya ke kuma kunyar bayyana shi, to a na kyautata ma sa zaton daina wannan laifin, saboda ya na kunyar bayyana shi fiye da wanda ba ya kunyar bayyana wani abu mara kyau da ya ke yi.
Wannan shi zai tabbatar ma na da cewa kunya muhimmiyar al’amari ce duba da yadda ta kan ba wa mutum kima tare da daga darajarsa cikin mutane.

Exit mobile version