12:30 na rana; 6 ga watan Janairu, 2200
Na kalli uwargidana, na ce,
don Allah mare ni,”
Ta daga hannu, ta zuba mini mari amma, na shanye kamar dan wasan rastalin ‘wrestling.’
“Ai ko a mafarki ma za ka iya sawa a mare ka,” na fada a zuciyata. Sai na sake kallonta, na ce,
“cije ni.”
Sai Amarya, mai yawan son barkwanci wadda, daman dariyar shan marin da na yi take ta yi abinta, ta yi farat ta ce,
ni ce zan mare ka.”
Mhm! Daman in ka ga Amarya tana yi wa yaron da ya yi laifi dariya, to, zai yi kuka kenan, in tana hada rai kuma to, zai sha nasiha kenan.
“Ka da ki kuskura, ba ke na sa ba.”
Uwargida ta galla min cizo. “Ya isa! Ya isa!!” na fada yayin da na ji cizon har tsakar ka. Amarya ta ci gabayar da dariya har da faduwa.
A shekarar 2012 lokacin da na karanta labarin, Tattaki Cikin Zamunna na cika da shakku tare da kallon abin bai fice wani abu ba sai almara. Ya za a yi a ce wai kana cikin wani zamanin ka shiga wani? Ko mamaki ban yarda na yi ba saboda, ban yarda da abin ba, sai ga shi ni ma daga zamanina na tattako cikin wani zamanin har na ketaro cikin wata duniyar. Ilimi ba kara ba ne.
Haka dai a farkon zuwana duniyar Mars din na yi ta ganin al’amarin kamar a mafarki saboda kasa gaskatawa da zuciya daya. Har sai da na fara tuno da tatsuniyoyin Hausawa na abubuwan da muka san ba sa faruwa dole sai a tatsuniyar. Can kuma sai na tuna ko a tatsuniyar an tabbatar da yiyuwarsu, amma a kunnen mai sauraro: Mun sha jin akuya tana cin nama, kare yana cin ciyawa, cinya tana magana. Lalle hakan na iya faruwa tunda halin nan da nake ciki ya faru.
Ba mamaki ba ma, na so a ce akwai kalmar da ta fi mamaki da ita zan ce na yi. Wai yau ni ne –har da iyalaina a duniyar Mars, a sabuwar Najeriya, a sabuwar Kano da aka kafa. Na ci gaba da ta’ajibi, ina tambayar kaina:
“A wata duniyar amma, ba tare da mun mutu ba?” Amma kuma, duk wannan aikin ‘Rabbil izzati-Alimulghayb’ ya kamata a yi wa godiya da yabo, shi kuma Farfesa, ya kamata a jinjina masa saboda kago kumbon ‘Bayeropollo’ da ya yi wa Najeriya. Bayeropollo, rocket ne wato kumbon zuwa sararin Subhana da duniyoyinsu –mafi tsananin sauri kuma, babba da aka taba yi a duniya. Kwararrun injiniyoyin Jami’ar Bayero ta Kano ne suka kera shi wanda Jami’ar Gwamnatin tarayya ta babban birnin Dutse ta dauki nauyi. Kumbon, ya lillinka kumbon kasar Iran, tsohon ya yi, sau da yawa a juriya da gudu da girma,ba a ma maganar Apollon kasar Amurka wanda muke kallonsa ‘aikin mutanen da’. Kumbonmu na Bayeropollo yakan dauki mutane dubu a lokaci guda ya kai su wata duniyar ya dawo abinsa. Yakan ci kilomita dubu-hamsin a rabin dakika daya, hakan, ne ya sa salansarsa shudiyar wuta take fitarwa maimakon jar wuta da tsofaffin kumbunan Amurka da Iran suke fitarwa. Shi ya sa, in ya gifta, shudiyar wutar za ka ga ni wal! Kamar walkiya, sai ka ga ya 6ace, saboda tsananin gudunsa. A dalilin wannan saurin ya sa har yanzu ba a samu kyamarar da za ta dauki hotonsa ba –in dai ba kafin a harba shi ba za ta dauka ba.
Duk da yake likkafata ta ci gaba yanzu har a duniyar Mars na tsinci kaina, ya kamata ku san cewa, ko a al’umar Hausawa, ni ne mutum na biyu da ya taba zuwa duniyar Wata bayan marigayi Alhaji Dk. Mamman Shata. Shi ya sa, bayan ya dawo, ya yi wakar Kumbo Aholo.
Ko shakka babu, kafin zuwanmu duniyar Mars, duniyar wata aka fara harba kumbon Bayeropollo dauke da mu amma, saboda yakin da muka tarar ana gwabzawa tsakanin ‘yan Alka’ida da kasar Amurka, sai muka bar musu ita muka dawo Mars din. In zan ba ku labari, ashe zuki-ta-malle shugabannin Amurka suka sharara lokacin da suka ce sun kashe Usama dan Ladin. Kuma an gano kawai siyasar duniya ce da irin ta kasarsu don su yaudari mutanensu su ci zabe. Wato, tun sanda suka rasa Usaman a Afghanistan da Pakistan, tunda, daman kasarsa ta haihuwa, Saudiyya, ta kore shi, ta kwace takardar shi ta dan kasa, sai ya ce, “tunda kun hana min matsugunni a duniyar doron kasa ta asali wacce ake cewa, ardh’ da Larabci ko ‘earth’ kamar yadda na ji Amurkawan suna fada da Turanci, bari in koma ‘kamar.’ Sai na rika mamakin irin yadda a Larabci da Turanci kalmomin suke kama, amma, watakila sabo da asalinsu ‘yan’uwa ne su, ina jin.
In takaice muku labari, ashe ‘robot’ wato mutum-mutumin roba mai siffar Usama suka kera, suka yi masa magudanan jini irin na mutum wato, blood circulation canals mai gudana da jinin dan akuya, suka je suka harbe shi, suka ce, sun kashe Usama. Yanzu haka, Usama yana raye cikin koshin lafiya a matsayin shugaban kasar Sa’udiyya-aththaniyah da ke duniyar wata:
Bayan tarewar su Usama doron duniyar watan ne sai ‘yan kungiyar tasa ta Alka’ida suka rika kwaso hazikai masu zalaka da basira da tunani irin na ban mamaki daga kasashe daban-daban daga duniyar ‘ard’ har suka gina kasar Sa’udiyya-aththaniyah ma’ana, Kasar Saudiyya ta Biyu. Suka gina kasar da tsananin tsarin tsaron da ya shallake na Pentagon din Amurka. Duk wannan ta faru cikin nasara bayan sun tokare mahangar Amurka daga hango yankin sabuwar kasarsu har sai da ta kai ga sun gama shiryawa tsaf don kai wa cibiyar tsaron Amurka ta Pentagon harin bala’i da masifa na kwab-daya sai kawai tsautsayi ya sa wani hazikin Ba’amurke, Paul Williams, ya gano an tokare mahangarsu daga hango wani bangaren duniyar wata. Kan haka ne, suka tura wasu hatsabiban hazikai da suka fi ji da su, Craig Anderson da Donald Brown, wadanda har yau ba su dawo ba bayan kame su da kasar Sa’udiyya-aththaniyah ta yi da laifin leken asiri amma, don jaraba sai da suka samu damar aika wa Amurka halin da suke ciki tare da wasu muhimman bayanai a takalminsu ta zirin iska mai nisan zango wato ‘Supreme Bluetooth’ mai iya shiga duk inda haske da ruwa da iska za su iya shiga. Wannan shi ne musabbabin barkewar yakin nasu wanda, yanzu haka Amurkan ce take shan kashi har ma suna tunanin gara su mika-wuya. A to, duniya juyi-juyi.
Ina kai ku a wannan labarin ta’ajibi na sararin Subhana. Ko a lokacin da na yi shakkun ba mu labarin Tattaki Cikin Zamunna din da aka yi, da na tuna ai labarin ya kare da ‘Ikon Allah’ ne bayan da ma’abocin ilimi, Dk. Salim ya ki yarda amma, sai gas hi abin yi wa shakkun nasa ya afku a kansa da maidakinsa. Da farko Dk. Salim ya yi tunanin sai ya gane komai amma, karshe dole ya mika wa Allah ikonSa. Ina jin ni ma shakkun da na yi ne aka nuna min ishara da wannan zamanin da duniyoyin da na shigo. Kodayake, ko ni ma da nake da kukumi, bayan shakku sun dabaibaye kwakwalwata har sun mata tarnaki, tana neman bugawa saboda na kasa gano yiyuwar hakan, sai na tuna da kissar Isra’iliyyat din nan da wani limami yake shakku a kan, ya za a yi a ce da wanda ya mutu a farkon duniya da wanda ya mutu a karshenta, tsawon kwanciyar kabarinsu zai zama daya ne kafin a tashi Kiyama.’ Ga shi, shi limami ne mai yawan nawa wato, yawan jinkiri. Ran nan ya dauko buta, ya zauna zai yi alwala sai ya tsunduma cikin shakkun daidaiton kwanciyar kabarin nan. A take, ba a mafarki ba sai ya ji kamar wata irin iska-iska guguwa-guguwa ta dauke shi, sai ya gan shi a wani yanki duniya daban, kuma ya samu kansa ya zama mace. Haka ya ci gabayar da rayuwa a matsayin mace har ta kai ga wani namiji ya aure shi; suka yi haife-haife; ya yi shekaru da yawa har ya tsufa tukuf a matsayin tsohuwa. Ran nan wannan mutumi yana zaune yana tunani da al’ajabin abin da ya faru a kansa ya koma jinsin mace, sai kawai irin wannan iska-iska ta sake daukansa sai ya gan shi a in da yake, ya komo namiji a in da yake a zaune da butar alwalarsa a gabansa, har ga mamu da suka saba binsa sun zo yin sallah kuma suna cewa,
“yau malam ya fito da wuri.”
Wani abin mamaki a sabuwar duniyar nan shi ne irin yadda muka koma yin magana da sabon harshen Hausa ‘New Hausa’, shi kuma Farfesa yake magana da babbar Hausa,‘adbanced Hausa’. Au, na ce fa na dena mamaki da Ikon Allah don ban isa na gane komai ba, hakan kuma shi yake tabbatar da Allah kadai ne Ya bar wa kanSa dukkan sani, kuma ya yi mana iyakar namu sanin. Kuma ba wanda ya isa ya haura iyakar sanin.
Sau tari nakan yi tafakkuri a kan, ko me ya sa mutane musamman Turawa suke tunanin sai sun gano komai? Amma ga shi ba sayin tunanin akalla kamar yadda suka shallake wasu mutanen da baiwar ilimi da ilhama irin ta mamaki har su iya kera abubuwan da wasu ba za su taba gane yadda su Turawan suka yi su ba sai dai kawai su dai suna karba suna yin amfani da su kawai, kamar irin su waya, da yadda ake tura wa wata kasar sakonnin iska na ‘birus’ cikin na’ura mai kwakwalwarsu, tun daga wata kasar mai nisan gaske kawai, don a bata musu bayanan makaman ‘nuclear’ na kare-dangi, ko aiken jirgi mai layar zana ko jirgin dab a shi da direba to, ai haka ne Shi ma ‘Khaliku’ da Ya shallake su da ratar da ba iyakar da ba za su gane yadda wasu abubuwanSa suke aiki ba. Domin Ya riga Ya iyakance musu in da ba za su haura ba. Dama Turawa su hutar da kansu, ba sai sun bari ta kai ga kasa fahimtar wasu lammuran Ubangijin ba ko yiyuwar wani abu ba sai su shiga yanke shawarar karyata wanzuwarSa kawai. Bayan ita kanta gazawarsu tana tabbatar da wanzuwar Mahalicci. Mu yanzu masu karamin ilimi da ilhamar, in misali muka kasa gane yadda waya take aiki ko yadda ake jirgi ya tashi, sai mu ce babu su?
Lalle shi farfesanmu da na taba jin labarin ta’ajibi a wurinsa ba shi da gurbatar tunani, shi ya sa a karshen labarinsa ya dangana mu da Ikon Allah. Masana da yawa sun bata saboda, tunannin sai sun gane tare da binciko abin da Allah Ya bar wa kanSa sani. Sai ka ga mutum daga ‘professor’ (shehun sani) ya koma pro-faithless (shehun bata). Lalle shi Furofesanmu professor ne na sani.