Cigaba daga makon jiya
Farfesa McGill ya karewa Maryama kallo da nufin ko zai fahimci wani sirri da ke tattare da ita kafin su fara tattaunawa. Ya lura da cewa kamannunta sun sha ban-ban da na Hausawa , kuma ga alama daga Maghreb take watau Arewacin sahara.
Suka fara tattaunawa da ita akan harkokin yau da kullum har a wayance suka sullube suka far hirar tarihi da hasashe-hasashen asalin Hausawa. Ga alama maryama sam ba ta da wat sha’awa akan tarihi kwata-kwata. Bayan kamar kusan mintoci arba’in suna magana ba su fahimci komai ba, sai Dr. Usman ya ce mata `Ni kuwa ina da wani abu da nake so in nuna maki, kila zai tuna maki da wani abu’’
“Me nene?’ ta tambaya
`wani hotonki ne’’
`Hotona kuma?’
`Kwarai kuwa. Kin gane shi’ ya mika mata.
Ta karba ta dubi hoton. Da alama ta fahimci wani abu daga yadda fuskarta ke karantar hoton. To amma kafin su fahimci wani abu daga labarin fuskarta sai suka ji ta ce “Ankh en Maat”
Sai kawai Maryama ta bace. Sama ko kasa babu maryama babu alamarta.
Duka wadanda ke tare da ita a lokacin sai suka yi tsit kamar ruwa ya ci su. Tsit, kake ji.
Abu kamar wasa suka fara nema, Dr. Salim na ta kwala mata kira har yana mata ba a yana cewa “ba na son irin wannan wasan”. Shiru suka karade gidan ciki da waje babu Maryama babu alamarta.
Abu kamar almara, har gari ya waye ba a Maryama ba. Hoton nata fa? Shima ba a ganshi ba.
Kwana daya, kwana biyu, kwana uku, abu shiru. Mako guda, mako biyu, shiru. Abu har ya kai wata guda cur.
Hankalin Dr. Salim ya dabaibaye har ta kai ya daina zuwa aiki. Ya yi iyaka kokarinsa domin ya gano ko akwai wani bayani a kimiyance da zai iya samu akan dalilin bacewar matarsa ya kasa. Karshe dai ya yarda da shawarar Alhaji Musa cewa a koma ga Allah a yi ta rokonSa.
21-3-`99
Maris 9, 1995
JAMI’AR BADUN
Farfesa Wai-Andah ya yi shiru yana nazarin bayanin da Dr. Usman da Salim suka yi masa. Can sai ya gyada kai da nuna alamar ya tuna wani abu. Take ya tashi ya dauko wata mujalla daga jerin Mujallun dake kan kantar ofishinsa wadda ke cike makil da littattafai da Mujallun ilmi. Ya bude ta ya soma karantawa.
Farfesa Wai-Andah fitaccen masani ne akan ilmin Kufai a Nijeriya. Can sai ya yi murmushi ya dube su ya ce `Da alama wannan matsala take tana da hanyar warwarewa sai dai ina kyautata zaton cewa sai kun je Masar. Farkon watan Janairu an hako makarar wani makusancin Fir’auna Akhanaten, sai dai abin mamaki ba bu gawarsa a ciki kuma an rubuta cewa `wannan sako ne daga tsohon zamani zuwa sabon zamani domin a ceci tsohon zamani-zama cikin gaskiya’. Dr. Sabik Al-Mansour wanda ya rubuta wannan makala ya yi hasashen cewa akwai wani abun al’ajabi babba da yake tattare da wannan makara kuma ya ce yana ci gaba da bincike. Amma karin bayanin da ya yi ya nuna cewa abin yana da dangantaka da tafiyar ruhi ne wanda Misrawan Dauri ke kira ANKH. Kuma kila warware matsalar ta hada da tafiyar ruhi.’
Dr. Salim kwata-kwata bai san inda aka dosa ba. Bayanin da Farfesa Wai-Andah ya yi ya kara harba tunaninsa, amma Dr. Usman ya fahimci inda aka dosa.
`Muna saurare Farfesa, yanzu wa ce shawara za ka ba mu?’
`Shawara mafi sauki shine lallai ne ku tafi Cairo. Dr. Al-Mansour abokina ne, zan baku takarda ku kai masa kila shi da yake fanninsa ne sosai zai fi fahimtar wannan surkullen ya kuma bada shawara mafi dacewa.’
`Mun gode Farfesa’ inji Dr. Salim.
Suka karbi takardar suka kama hanyar komawa Kano. A kan hanyar su Dr. Usman ya sake karanta makalar Dr. Al-Mansour sannan ya kara fahimtar inda aka dosa. Ya yi wa Dr. Salim karin bayani `Su Misrawan Dauri sun yi imani da cewa ruhin mutum wanda suke kira ankh shine mutum, kuma za a iya sarrafa gangar jikin mutum ta hanyar sarrafa ruhinsa. To a lokutan matsi, ana iya matsar da ruhin mutum zuwa wani zamani domin a cece shi.’
`Ni ban gane wannan dogon turancin ba. Ka gaya mani me ya faru da Maryama?’
`Ai bayanin ne nake kokarin yi maka. Abin da Dr. Al-Mansour ke hassahe shine wani ko wata za ta yi tafiya cikin zamunna’
`Me kake nufi da haka?’
`Abinda ake nufi dai a takaice shine Maryama ba `yar wannan zamanin ba ce kuma ta koma zamanin da ta fito watau zamanin Fir’aunonin Masar’
`Kana nufin cewa a halin yanzu ta koma wani zamani na dabam kenan?’
`Haka dai hasashen ke karfafawa’
`Any scientific edplanation?’
`Simply, time trabel ne kawai’
Dr. Salim ya gyada kai ya yi shiru. Kwarai ya san wannan ra’ayi na kimiyya wanda ya amince da cewa mutum zai iya tafiya daga wani zamani zuwa wani zamani. To amma a wancan ra’ayin ai ance sai in mutum zai iya tafiya a gudun haske watau kilomita dubu dari uku a kowace dakika. To ita Maryama bacewa ta yi a gaban idanunsu. Shi ba zai iya bada wani bayani na kimiyya akan bacewar matarsa ba. Ga alama ya fara karaya akan cewa dole ne komai ne ya samu bayani a kimiyance.
`Ba za mu fahimci al’amarin sosai ba har sai mun ga Dr. Al-Mansour’ inji Dr. Usman.
Maris 27, 1995
ALKAHIRA: OFISHIN DR. AL-MANSOUR, JAMI’AR AL AZHAR.
Dr. Al-Mansour ya kara saurarar bayanan da su Dr. Salim suka yi cikin natsuwa da cikakkiyar sha’awar bayanin nasu. Da ma sun rubuto masa a rubuce kafin zuwansu. Ya kuma gabatar da wani bincike kafin su zo.
`Yanzu za mu je mu sadu da kwararren malami a kan zamanin Fir’auna Akhanaten watau Farfesa Weeks. Mun tattauna da shi da kuma sauran kwarrarru akan addini da al’ada ta Misrawan Dauri. Ba za mu ce muku kai tsaye ga bayani ba kila sai nan da sati biyu, kafn sannan mun tabbbatar da sakamakon bincikenmu. Amma ko menene amsar su to za ta zama babban labari a duniya’ Dr. Al-Mansour ya bayyanawa su Dr. Salim.
Su Dr. Salim suka ci-gaba da zagayawa suna kallon ababben tarihi da Tsohuwar Masar ta bari. Sun je Thebes da Karnak da Abu Simbel da Abydos da Dahshur da Sakkara da sauran tsofaffin biranen Misrawa. Sun ga Dalar Misrawa wadda ta basu mamaki matuka. Sun ga gine-ginensu na mabauta da mutum-mutumin manyan Sarakuna. Sun ga Zaki mai kan mutum watau Sphind. Masar ta burgesu kwarai da gaske. Alkahira watau Cairo, sun je Gidajen Adana Kayan Tarihi sun ga gawawwakin Fir’aunoni irin su Snefru da SetiI da Khufu da Amentohep II, da Fir’auniya Hapsetsut da kuma RemesessII watau Fir’aunan annabi Musa Alayhis Salam. Wani abu da ya kara burgesu shine dukiyar Fir’auna Tutankhamun (Fir’auna mai kan gwal).
`Usman ka lura da yadda wadannan mutane suka adana kayan tarihinsu?’
`Sosai kuwa , abin gwanin ban sha’awa’ Dr. Usman ya amsa.
`To mu me yasa a Kano ba ma damuwa da adana kayan tarihinmu? Ka duba badala ka gani duk ta zube. A wasu wuraren ma haketa ake yi ana yin gini. Sam ba mu damu da tarihi ba’ Dr. Salim ya ce.
Afirilu 8, 1995
DAKIN BINCIKE, SASHEN NAZARIN TSOHUWAR MASAR JAMI’AR AL AZHAR.
A cikin wannan daki na bincike akwai kwarrarrun masana guda goma. Kowane hukuma ne mai zaman kansa a wani bangare da ya shafi Tsohuwar Masar. Akwai mai daukar hoton bidiyo da kuma kyamara karama. Sai kuma Dr. Usman da Dr. Salim.
Farfesa Andrew Harschell ya mike tsaye ya yi gajeren bayani a idan yake jaddada cewa `Yau rana ce da zamu yi abin tarihi. Wannan shine karo na farko a tarihin Nazarin Tsohuwar Masar da yau za ta yi hulda da jiya. Mun yi nazarce-nazarce akan Fir’aunoni da hanyoyin rayuwa da kuma addinin Misrawan Dauri. A yau za mu jaraba kwarewarmu wurin tafiyar da ankh din abokinmu Dr. Salim zuwa zamanin Fir’auna Akhanaten domin ya ceci sabon sauyin da yake kokarin kawowa.’’
Ya kara bayanai sannan aka nemi Dr. Al-Mansour da ya gabatar da ainihin gundarin maganar. Ya tashi ya fara bayani `Kowa ya sani cewa a tsakanin shekara 1352 zuwa 1336 kafin zuwan Annabi Isa Alaihis salam Fir’auna Akhanaten ya yi mulki. Da sunansa Amenhotep IB lokacin da ya zama Fir’auna a 1352BC ya yi tawaye ga Babban Ubangijin da Misrawan Dauri watau Amun. Ya yi yekuwar samar da sabon addini a karkashin sabon Ubangiji mai suna ATEN. Ya ce Aten shi kadai za a bautawa kuma ba shi da abokin tarayya. To a dai-dai lokacin da yake kokarin kafa tushen wannan sabon addinin nasa, sai manyan malaman mabautar Thebes suka tayar da kayar baya domin a wannan sabon addinin na Akhanaten su ba su da ta cewa. Saboda haka ne suka shirya makarkashiyar rusha addinin tun daga tushe.’ Ya ci gaba `Sun fahimci cewa, ba za su ci nasara ba har sai sun layyar mutum. Mutumin kuma dole ya zama mace kuma `yar babban malamin Aten. To shine abin ya fada kan Maryama. Da iyayenta suka fahimta suka kuma ga cewa a lokacin ba za su iya kareta ba, sai suka turo ankh dinta wani zamani da nufin ta samu mai ceton ta. Saboda haka ne su kum manyan malaman Amun suka turo ruhin wani ya zo ya koma da ita. Makasudin samar da hasashen Birnin Surame kenan.
Saboda haka, idan Dr. Salim ya amince zai yi tafiya cikin zamunna, watau za a tura ruhinsa wancan zamanin domin ya je ya ceto ta. Don in har bai yi haka ba to malam Amun za su yi nasarar rusa addinin Aten daga tushe wannan kuma zai sauya tarihi baki daya. A halin yanzu tana hannunsu, nan da makwanni biyu za su yi layyarta ga Amun.’ Dr. Al-Mansour ya zauna.
Cigaba a makon gobe in sha Allahu.