Abubakar Abba" />

Tattalin Arziki: Cibiyar Bajekoli Ta Legas Ta Tsara Wa Gwamnatin Tarayya Ajanda

Cibiyar baje kolin kasuwanci ds masana’antu ta jihar Legas LCCI, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya data mayar da hankali akan yin amfani da kaya masu inganci da kuma samar da kyawawan tssre-tsare don dorewa da kuma ciyar da tattalin arzikin kasar nan.

Cibiyar ta kuma jaddada cewar, zaiyi wuya a dinga samun zuba jari a tattalin arzinkn kasar nan, yanayin na yanzu da kudin ruwa na banki ya kai sama da kashi 25 bisa dari a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki kasa.

A cikin ajandar cibiyar mai shafuka biyar ta raba kafa akan fannin tattalin arzikin Nijeriya da Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf ya rattabawa hannu ya kuma fitar a jihar Legas a satin da ya gabata, cibiyar ta LCCI ta yi nuni da cewar, kudin ruwan na bankuna da a yanzu ake kara rubanya su, zasu iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzinin kasar nan.

Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf yaci gaba da cewa, tsaurin da aka samu na yanayin musayar kudaden kasar waje, bazai wani taimaka wajen ciyar ds tattalin arzikkn kasar nan gaba ba.

A cewar Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf ya hakan ya kawai janyo samar da damammaki ne na cin hanci da rashawa ds kuma dakile damar shigowar zuba jari a cikin kasar nan.

Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf na cibiyar ta LCCI ya kara da cewa, tsarin tara haraji yana bukatar a sake sabunta shi yadda zaiyi daidai da tattalin arzikin kasar nan, musamman don kuma a ragewa masu son zuba jari a fannin tattalin arzikin nauyin tsadar karbar haraji, inda hakan yake karewa akan masu sayen kayan da masana’antun suka sarrafa.

Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf ya LCCI ya yi nuni d cewa, yin amfani da bankuna a matsayin ajent da Hukumar tara haraji ta kasa FIRS, yana da rikitarwa, sanya damuwa, matsi kuma bai yiwa masu zuba jari dadi.

Ya yi nuni da cewar, karbar haraji bai kamata gwamnati ta mayar dashi tamkar hanya daya ta samar da kudin shigar ta ba.

Da ya ke yin tsokaci akan tsare-tsaren kasuwanci, Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf ya yi nuni da cewar, akwai bukatar da a mayar da hankali akan masa’antun cikin gida yadda hakan zai kara masu kwarin gwaiwa wajen yin gasa a tsakanin ta sarrafa kayan cikin gida da kuma amfanin tattalin arzikin kasar nan.

A cewar Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf yace, har yanzu akawai damarmaki da dama da ba’a yin amfani dasu a fannin mai da da iskar gas, ma’aikatun sarrafa takin zamani.

A karshe Darakta Janar na cibiyar Muda Yusuf yace, “ Muna da bukatar mu kawo karshen lamarin ganin cewar, masu fitar da man fetur ds kuma masu fitar dashi don sarrafawa.

Exit mobile version