Tattalin Arziki: Masana Sun Ja Hankalin Gwamnati Kan Gargadin Babban Bankin Nijeriya

A kwanan baya ne babban bankin asa CBN ya gargadi gwamnatin tarayya akan yuwar gwamnatin zata sake jefa kasar nan a cikin matsin tattalin arzikin kasa da gwamnatin a kwana baya ta yi shelar cewar ta fice daga ciki.

Wani Farfesa a kasuwanci kuma shugaban sasshen banki da hada-hadar kudi dake jami’ar jihar Nasarawa Uche Uwaleke ya sanar da hakan a hirar sa Majiyarmu, inda yace, bai kamata gwamnatin ta yi buris ea gargadin ba.

A cikin watan Satumbar 2018 ne kwamitin tsarin kudi (MPC) ya sknar da hakan a wata ganawa da ya gudanar, inda yace, saukar da tattalin arzikin ksar ya yi a cikin shekaru biyu da suka yana zama barazana ga aukuwa sake komawa cikin matsin tattalin arzikin.

A lokacin da yake karanta sakamakon ganwara gwamnan CBN  Mista Godwin Emefiele yace, kwamtin ya nuna damuwasa akan fitar da kasar nan ta yi daga matsin tattalin arzikin kasa amma akwai barazana dake janyo yin tafiyar hawainiya da kai kashi 1.95 da kuma kashi 1.5 a farkon zangon shekara dakuma zangon shekara ta biyu ta  2018.

Kwamtin ya bayyana cewar, tafiyar hawainiyar ta farao ne daga fannin mai da kuma sauran fannin tattalin arzikin kasa. Da ya ke kuma tsokaci akan lamarin, Farfesa Uwaleke yace, mun shiga wannan sarkakiyar a baya kuma gargadin da CBN ya yi ya kamata ya zamowa gwamnatin darasi.

A cikin yan watannin da suka wuce ne bayan da Nijeriya ta fice daga matsain tattalin arzikin kasar a tsakiyar 2017 ta yi kokarin yin bankwana da matsin na tattalin arzikin kasa musamman a lokacin da farashin mai ya farfado.

Asusun ajiya na kasar waje na gwamnatin tarayya ya koma daidai, hauhawan farashin kaya ya sauka, indakuma kasuwar shinku ta Nijeriya ta kai matsayi na uku a 2017.

Ya yi nunda cewar amma a yau, alkalumar sun munana ganin cewar tattalin arzikin kasar ya koma kashi 2.11 zangon shekara ta hudu a 2017 zuwa kashi 1.95 a farkon shekarar 2018 inda ya kuma kara sauka zuwa kashi 1.5 bisa dari a farkon shekarar 2018.

Har ila yau, fannin aikin noma shi ma ya fada a cikin wani mummunan yanayi a shekarun da suka wuce hara lokacin da kasar ta fada a cikin matsain tattalin arzzikin kasa, inda ta iya karuwa zuwa kashi 1.19 bisa dari a farkon shekarar 2018.

Exit mobile version