Ahmed Muhammad Dan Asabe" />

Tattalin Arziki: Tallafa Wa Kananan ’Yan Kasuwa Zai Taimaka Wa Najeriya – Dr. Umar Muhammed

Rubutun Ajami

An gano cewa tallafa wa kananan yan kasuwa zai taimaka wajen habbakar tattalin arzikin kasa, musammam ma kasa irin Najeriya wacce tana daya daga cikin jerin kasashe masu tasowa.

Shugaban kungiyar yan kasuwan arewa( Arewa Traders Association) reshen jihar Kogi, Alhaji ( Dakta) Umar Muhammed ne ya bayyana hakan a yayin da yake tattaunawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU, a jiya litinin a garin Lokoja.
Alhaji Muhammed wanda har ila yau shine sakataren jin dadin kungiyar ta Arewa Traders Association, reshen Arewa ta tsakiya da suka hada da Kogi, kwara, Benuwe, Nasarawa, Neja,filato da kuma babban birnin tarayya( FCT), yace kanana da kuma matsakaitan yan kasuwa suna taimakawa kowa ce kasa wajen ingantawa da kuma tashin tattalin arzikinta.
Ya ce, kananan yan kasuwa irinsu masu sana’ar sayar da laimu, karas, abarba da sauran kananan sana’oi suna da muhimmiyar gudunmawar da zasu taka wajen habbakar tattalin arzikin kasa, idan har suka samu tallafin daya dace daga gwamnatoci a dukkan matakai.
Sai dai kuma shugaban ya nuna rashin jin dadinsa ganin yadda kungiyar yan kasuwa dake yammacin Najeriya  tayi wa takwararta ta Arewa,wato Arewa Traders Association fintikau saboda, a cewarsa, gwamnatin tarayya tana damawa  da yayan kungiyar,inda yace su kam kungiyar su ta Arewa Traders Association, sun rasa inda matsalar take.
Alhaji Umar Muhammed yace duk da cewa gwamnatin tarayya tana iyakar kokarinta wajen kyautata wa yan kasuwan, amma kuma” Ina kira ga gwamnatin data kara kokari wajen tallafa wa kungiyar mu ta Arewa Traders Association. Har ila yau, a madadin kungiyar Arewa Traders Association, ina kira ga babban bankin Najeriya,( CBN) daya baiwa yayan kungiyar bashi ko rancen kudi domin ganin sun inganta jarinsu”hakan zai taimaka wajen habbakar tattalin arzikin kasa,” inji Shi.
Alhaji Umar Muhammed ya kuma yabawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a bisa kudurinta na farfado da tattalin arziki da kuma ceto tattalin arzikin daga rugujewa, inda har ma ya bukaci yan Najeriya dasu baiwa shugaban cikakken hadin kai a kokarin da yake yi na ceto kasar nan daga halin data tsinci kanta na matsalar tsaro da kuma sauran kalubale dake addabarta.
Haka zalika ya yi kira ga mambobin kungiyar ta Arewa Traders Association dasu kasance masu bin doka da oda da kuma baiwa gwamnati hadin kai, wanda a cewarsa zai taimaka wajen ganin gwamnatin ta kyautata wa kungiyar.
“Zan yi amfani da wannan dama wajen kira mambobin mu ta Arewa Traders dasu zama masu biyayya ga hukuma tare da ganin sun zauna Lafiya. Kada Ku manta, duk inda babu zama lafiya, to babu ci gaba” Inji Alhaji Umar Muhammed

Exit mobile version