Matawallen Bade; tsohon karamin ministan kudi a gwamntin da ta gabata, Dakta Yerima Lawan Ngama, wanda kuma kwararren masanin tattalin arziki ne wanda ya kasance tsohon babban manajan daraktan Bankin ‘Diamond Bank’ da kuma manajan daraktan Bankin ‘First Bank’ a yankin arewa. Tsohon ministan ya ce, har yanzu da sauran rina a kaba dangane da salon tafiyar gwamnatin Muhammadu Buhari kan sha’anin tsarin tattalin arziki, wanda ya ce gurgu ne da tababar kai bantensa. A tattaunawar da ya yi da Muhammad Maitela, a Yobe, ya yi bayanai dangane da gwamnati mai ci ta APC, ga yadda hirar ta kasance:
A Kwanan baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin sake farfado da tattalin arzikin Nijeriya, a matsayin ka na masani, ya kake kallon wannan shirin?
Haka ne, kwanan baya shugaban kasa da mataimakin sa da ministan tsare-tsare sun yi taron kaddamar da kwamitin farfado da tattalin arzikin kasa, mai gajeren zangon daga 2017 zuwa 2020. To, wannan tsari ba wani abu sabo ba ne, an dade ana kaddamar da irin wadannan tsare-tsaren. Akan yi tsari mai dogon zango, sai kuma a dinga tsakurowa shekara uku-uku. Wannan ya faro ne tun lokacin jamhuriya ta farko a lokacin marigayi Abubakar Tafawa Balewa, wanda ake kira da Ruling Plan. To wannan abu da aka yi yana da kyau, kuma abinda yakamata a rinka nuna wa jama’a don su san ana yi, sai dai zai yi tasiri ko ba zai yi ba wannan kuma shi ne bamu sani ba tukun.
To, yallabai ya kuke kallon wannan tsarin, shin kuna ganin kwalliya za ta biya kudin sabulu?
Wato shi tsarin tattalin arzikin kasa da muke dashi, tun daga lokacin Tafawa Balewa zuwa lokacin Gawon zuwa marigayi Janar Murtala har a lokacin Obasanjo na farko. Abu na daya, wato alkiblar gwamnati, saboda idan mutane zasu iya tunawa, har zuwa lokacin Shehu Shagari, Nijeriya tana tafiya kan tsarin tattalin arzikin hadaka (Mided Economy), wato tana hada tsarin gurguzu ne dana jari-hujja. Wani abu wanda yakamata a bar wa yan kasuwa sai ka ga gwamnati ta shiga ciki dumu-dumu; ko yana da kyau ko bai da. Wani abin kuma an bar wa jama’ar kasa masu jari, to wannan hadakar abubuwa biyu to shi ne ainihin alkiblar gwamnati a wancan lokacin.
Amma da Janar Babangida ya zo sai aka bar waccan alkibla, gwamnati ta sa hannu kashe kudi kawai ake a banza kuma kwalliya bata biyan kudin sabulu. To amma lokacin Janar Babangida da aka yi SAP din nan, to abinda ya faru wato an juya alkibla ne; daga hadakar tsarin tattalin arziki zuwa na jari-hujja akan cewa wannan canje-canjen sakin harkokin kasuwanci a hannun yan kasa, inda gwamnati ta fidda hannun ta a
harkokin kasuwanci.
A yayin da kuma lokacin marigayi Janar Abacha aka rungumi wannan alkibla sosai inda aka tattaro duk wadada suke sune yan kasuwar Nijeriya da masu masana’antu da manoma da yan book da kowa-da-kowa aka Rungumi wannan tsarin, aka yi shekara guda cur, kuma aka kawo wani shiri na shekara wajen 15; ka ga wajen 1997 ne aka yi Bision 2010. A wannan tsarin sai aka dauki sabuwar alkibla, wadda aka sa mata suna TINA (There Is Not Alternatibe). An yarda a kan cewa wannan rungumar yan kasuwa a basu duk abinda suke bukata, a rungumi manoma, a basu duk abin da suke bukata, ba wai gwamnati ce za ta share fili ta zauna tace ita da kanta za ta yi noma ba, a’a, dole ne ta taimaki su manoman suyi noma da kan su.
A lokacin da shugaban kasa Obasanjo ya zo sai ya mikar da shi zuwa shekarar 2020. Shima ya yinda marigayi shugaban kasa ‘Yar Aduwa ya zo sai ya dora kan wannan hanyar; har aka zo aka ce Bision 2020 wanda muna so idan mun bi wannan tsarin zamu zama daya daga cikin kasashe 20 da suka fi arziki a duniya.
To, wannan tsaririn shi ne har lokacin shugaba Jonathan, inda kuma aka fadada shi, aka bashi suna ‘Transformation Agendar’. To yanzu kana da shirin ka har zuwa 2020, yanzu ka tsakuro shekara uku a ciki. Abin tambaya, to shi wannan 2017 zuwa 2020 din a cikin wancan tsarin wanda ya kai har 2020 ka dauko shi, ko daga wani guri ka dauko shi? Ka gane, sai aka ce an kirkiro wani sabon abu ne, kuma alkiblar har yau, tun daga lokacin da Buhari ya hau shugaban kasa bamu taba jin cewa shi fa ya rungumi tsarin jari-hujja ba.
Har wala yau kuma su wadanda tattalin arzikin yake a hannun su ba a taba yin taro aka ce shugaban kasa ya kira su gaba daya ba, ya ce ku zo mu hada hannu domin mu gyara tattalin arzikin kasar nan ba. Kuma ko yaya za ka yi, tattalin arzikin Nijeriya, kawai gwamnati bai wuce tana rike da kasha 18 cikin dari ba: 72 yana hannun ‘yan kasa (‘yan kasuwa).
Yadda yake a tsarin gwamnati, kullum dole ne kowanne wata shugaban kasa ya zauna da duk wadanda suke da ruwa da tsaki a sha’anin tattalin arzikin kasa, shi ne ake kira tawagar masana tattalin arziki (Economic’s Tearm). A wannan, taron da na sani ake gudanar wa a lokacin shugaban kasa Jonathan da can baya a zamanin ‘Yar Aduwa da shugaba Obasanjo, in an je irin wannan zaman, su ma’aikatan gwamnati kawai ‘yan kallo ne; shi shugaban kasa yana sauraron wadanda suka zo daga bangaren sha’anin kasuwanci. Za a nemi shawarar masu wakiltar masu masana’antu da cewa ga wannan kudurin, yaya kuka gani? Idan kuma abinda ya shafi noma ne, manoma ne za a tuntuba da shawarar yadda za a yi, idan al’amarin saya da sayarwa ne suma haka. To yanzun ma a rungumo su a zauna dasu, amma ka ga ba a yi, kuma idan ba a yi ba, an riga an rabu da waccan alkibla ta jari-hujja an komo akidar gwamnati ita kadai, ko meye? Saboda haka idan ma baka fahimci bisa kan wacce fuska ko alkiblar ce ka dosa ba, to duk wani kwamitin farfado da tattalin arziki ba zai yi ma’ana ba, balle har kace wannan zai yi tasiri ko ba zai yi tasiri ba.
Saboda haka muna bada shawara kan cewa, don Allah a daina saka siyasa a cikin sha’anin tsarin tattalin arzikin kasa, babu zancen siyasa a irin wannan lamarin. Idan mutumin da zai baka shawarar yadda Nijeriya za ta ci gaba, wannan ake bukata, babu bukatar asa siyasa.
Baya ga wadannan, wacce shawara kake da ita wajen inganta tsarin tattalin arzikin Nijeriya?
Ita maganar tsayuwar tattalin arzikin kasa, akwai abu biyu da na zayyana maka; sune alkibla da akida. Bayan wadannan kuma akwai abu na uku, shi ne rike alkawari. Shi wannan yana nufin kamar sanya yarjejeniya ce tsakanin ka da jama’ar da suka zabe ka. Yanzu ka ga
kamar lokacin da ministan wutar lantarki da ayyuka, Babatunde Fashola ya bayyana cewa ya za a yi a ce ana zaune a kasar nan babu wutar lantarki, ai ya kamata nan da watanni 6 kowa ya samu wutar lantarki. Sai mu ce mun rikeka a kan wannan, kayi muna alkawarin. Yanzu gashi shekaru biyu sun wuce bamu ga komai ba.
A lokacin Jonathan kowanne minista a cikin kowadanne watani 6 sai ya zo ya gaya wa mutane wanne alkawari ya yi kuma wanne ya cimma wanne bai
cika ba. Sannan a wancan lokacin, alkawaran da kowanne ministan ya dauka, kai minista za ka sa hannu shugaban kasa ya sa hannu a rubuce kayi alkawari kuma za ka aiwatar dashi kuma ana bibiyar aikin kowanne minista. Saboda wannan dole gwamnati tayi alkawarin cewa ga abinda take son ta ga ta cimma. Akwai daya daga cikin wani alkawarin da gwamnatin Jonathan take dashi, shi ne kafin shekarar 2016- 2017, Nijeriya za ta daina shigowa da shinkafa; wato zamu noma shinkafar da zai ishemu.
To ka ga wannan burin; duk da ba a kai ga cika shi ba, amma dai an kama hanyar sa, kuma bai kmata ayi wurgi dashi ba, saboda duk wani batun tsara tattalin arzikin kasa noma shi ne kan gaba. To da wannan gwamnatin da ta zo da za ta iya cewa shugaban kasa zai yi mulki zuwa 2019, kuma kafin wannan lokacin Nijeriya za ta iya ciyar da kanta.
Da an yi wannan alkawarin da kowanne talaka ya san alkawarin da shugaban kasa ya yi masa, kuma yana jiran ya ga an cika masa shDomin duk wata hanyar farfado da tattalin arzikin kasa, idan ba a saka shi a cikin saukakan kalmomin harshen da kowa zai iya fahimta ba.
Misali ka daukar wa jama’a alkawarin cewa Nijeriya za ta iya ciyar da kanta nan da 2019, ka ga kowa ya san me aka fuskanta. Amma yanzu da za a tambayeka wadanne alkawari ne wannan gwamnati tayi wa jama’ar kasar nan, wanda kuma ta kama hanyar cikawa? Duk da na san an ce za a ciyar da ‘yan makaranta abinci, amma bamu gani ba. An ce za a ba mutane kudi, ko yaya ne? wanda a karshe ma ya ce ba shi ne ya yi wadannan alkawurran , wai jam’iyya ce ta yi. An ce za a mayar da darajar naira dai dai da ta dala. Yanzu kuma halin da ake ciki akwai tazarar daruruwan kilomitoci tsakanin dala da naira (Dariya). Shi zancen tattalin arzikin kasa, dole kowa yasan inda aka dosa. Ai rakiya ne, yanzu ban san inda ka nufa ya za a yi in raka ka?
Amma in ka gaya wa mutun ga inda za ka sai ya zo ku tafi, dama duk wani tallafi zai iya baka. Mu yanzu muna son gwamnati ta maida tsare-tsaren fasalta tattalin arziki ta maida su kan alkawurra, cikin yare ko kalmomin da kowa zai fahimta.
A lokacin Obasanjo, bayan an tattaro masa sakamakon kwamitocin, sai ya maida su alkawari daya inda ya ce kafin ya sauka daga mulki zai samar biloniyoyi guda 30, ka ga burin sa shi ne ya taimaki yan Nijeriya tattalin arzikin su ya bunkasa. Ka ga da ya gama shekarun sa 8, a kididdiga an gano Obasanjo ya samar da gaggan manyan yan kasuwa da suka mallaki biliyoyin dala har mutum 15, wadannan yanzu haka kowa yana cin gajiyar su a kasar nan. Irin su Alhaji Aliko Dangotte, Alhaji Abdussamad Sheikh Isyaka Rabi’u.
Sannan da a ce ka kirkiro karamar hukuma ko jiha daya gara ka samar da hamshakin dan kasuwa guda daya, saboda akwai jihohi da yawa wadanda tun da aka kirkiro su ba a ga ci gaban komai tattare dasu ba, kamar jihata ta Yobe ba abinda aka yi a kasa. Kalli yadda Abdussamad Isyaka Rabi’u, abubuwan da ya yi wa jama’ar Nijeriya, ta hanyar kamfanonin sa da yawan jama’ar da ya dauka. Mun yarda an ce an bube kamfanoni, to a koma can kasa wajen manoma mana, yanzu ace ana son a san wane manomin yake noma buhun shinkafan miliyan daya. A duba a gani, akwai ko babu, sai dai ko Olam, shi kuma kamfani ne na Indi, amma cikin yan Nijeriya ban ga mai noma buhu shinkafa miliyan daya ba. To ayi alkawarin cewa za a taimaki manyan manoma, wanda kafin Buhari ya gama zangon mulkin sa na farko za a kirkiro manoma masu noma buhu miliyan daya su 50.
Idan an yi wannan zamu iya ciyar da kan mu kenan. A maida shi alkawari, a ce kowacce jiha ayi kokarin kirkiro manomi daya wanda zai iya noma buhu miliyan 1- ana iya samar dasu a cikin jihohi 36.