CRI Hausa">

Tattalin Arzikin Jihar Xinjiang Ya Samu Tagomashi A Shekarar 2020 Duk Da Tasirin COVID-19

Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta arewa maso yammacin kasar Sin, ta samu ci gaban tattalin arziki fiye da yadda aka yi tsamani a shekarar 2020, duk da tasirin annobar COVID-19.
Bisa la’akari da ci gaban da take samu cikin shekarun da suka gabata, kwanciyar hankali da farin cikin al’ummar jihar na karuwa, inda mazauna yankunan karkara ke daga cikin wadanda suka fi cin gajiya.
Bisa rahoton aikin gwmanatin jihar da aka gabatarwa taron majalisar wakilan jama’ar yankin na shekara-shekara da aka fara jiya, tattalin arzikin jihar ya fadada da kaso 3.4 a bara, wanda ya karu da maki kaso 1.1 fiye da ci gaban GDPn kasar.
An samu ci gaban tattalin arzikin ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ingantuwar kwanciyar hankali a yankin.
Da yake gabatar da rahoton, shugaban gwamnatin yankin, Shorat Zakir, ya ce yanzu ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, ba tare da aukuwar ayyukan ta’addanci da suka yi ta gudana a fadin yankin cikin shekaru 4 da suka gabata ba.
Ya kara da cewa, jihar za ta ci gaba da himmantuwa wajen yaki da ta’addanci da wanzar da zaman lafiya ta hanyar daukar matakai masu inganci bisa doka. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Exit mobile version