Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Shiga Matakin Da Zai Bunkasa- Ministan Kimiyya

Ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya ya shiga matakin da zai bunkasa, domin a cewarsa yanzu Nijeriya ta fito da hanyoyin kirkire-kirkire da tsare-tsaren dogaro da kai, sabanin yadda a da Nijeriya ta dogara da a yi mata komai.

Onu ya bayyana hakan ne a wani taron wakoki da ba da kyautuka na 2019 da ‘Caleb Group of Schools and University,’ ta shirya.

Onu ya kara da cewa; tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba ta hanyar yin dogaro da kai tare da tabbatar da cewa Nijeriya ba ta dogara kacokaf da wadansu ba sai dai hanyar bunkasa ilimin kere-kere. “wannan yana da muhimmanci kuma yana da bukatar ga ci gaban kasarnan.” In ji shi.

A cewarsa irin wadannan matakan kasar China suka dauka, inda  a watan Disambar da ya gabata suka gudanar da taron murnar cika shekara 40 wajen daukar irin wannan tsarin kwaskwarimar. Har wala yau ya ce irin matakin da Koriya ta Kudu da Singrapore da sauran su suka dauka ke nan.

 

Exit mobile version