CRI Hausa" />

Tattalin Arzikin Sin Ya Jurewa Tasirin Cutar Numfashi Ta COVID-19

Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta fitar da wasu alkaluma a ranar Alhamis, wadanda suka nuna yadda cutar numfashi ta COVID-19, ta yi matukar tasiri ga tattalin arzikin kasar na watannin Janairu da Fabarairu. To sai dai kuma a halin yanzu, an kai ga kusan dakile yaduwar annobar, kana yanayin kandagarki, da na shawo kan cutar na kara kyautata.

Alkaluman sun nuna cewa, an cimma nasarar kare al’amuran rayuwar al’ummar Sinawa, kana yanayin zamantakewar al’ummar kasar na cikin daidaito, yayin da ginshikan makomar tattalin arzikin kasar na dogon lokaci ke kan matsayin su ba tare da canzawa ba.
A daya bangaren kuma, hukumar ta jaddada cewa, a mataki na gaba, za a aiwatar da matakan bunkasa kandagarki da na shawo kan cutar, da bunkasa tattalin arziki, da raya zamantakewar al’ummar kasar cikin managarcin tsari, da takaita hasarar da cutar ta haifar, da dawo da yanayin tattalin arziki da zamantakewa yadda aka saba, tare da bunkasa ci gaban sa cikin yanayi mai inganci. (Mai Fassarawa: Saminu AlHassan)

Exit mobile version