Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Tattalin Arzikin Yanar Gizo Na Ingiza Karuwar Tattalin Arzikin Sin

Published

on

Nie Mingxue, mai jigilar kayayyaki ne a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake yammacin kasar Sin, yana aikin jigilar kayayyaki da sauri ga mutane cikin birninsa, wadanda suka yi oda ta yanar gizo. A ko wace wata, yana iya samun kudin shiga kimanin RMB yuan dubu 10. Cikin birane sama da 200 a kasar Sin, akwai masu jigilar kayayyaki wadanda ke isar da kayayyaki zuwa hannun masu sayayya cikin sa’a guda daya kawai sama da dubu dari 9, kuma kashi 1 bisa 3 daga cikinsu, sun fito ne daga wurare masu fama da talauci.

Wannan daya ne daga cikin gudummawar da bunkasuwar tattalin arzikin yanar gizo ta bayar. Cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, tattalin arzikin yanar gizo yana ci gaba da bunkasuwa, lamarin da ya haifar da guraben ayyukan yi da yawa.
Cibiyar nazarin harkokin sadarwa ta kasar Sin ta fidda takardar bayanin bunkasuwar tattalin arzikin yanar gizo na kasar Sin wadda ta nuna cewa, cikin shekarar 2019, tattalin arzikin yanar gizo ya ba da gudummawar kaso 67.7% na karuwar ma’aunin tattalin arzikin GDP, lamarin da ya sa, ya kasance babban karfin raya tattalin arzikin Sin bai daya.
A halin yanzu, tattalin arzikin yanar gizo yana canja hanyoyin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin bisa fannoni daban daban, kamar kere-kere, da ayyukan gona, da sufuri, da ba da ilmi, da ba da jinya da dai sauransu, lamarin da ya inganta bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin.
Kaza lika, tattalin arzikin yanar gizo yana bunkasuwa da sauri a kasar Sin sakamakon manyan kasuwannin da ake da su a kasar. Kuma bunkasuwar fasahar 5G, da fasahar kididdiga da sauransu, sun ba da babban goyon baya ga harkokin raya tattalin arzikin yanar gizo. A sa’i daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da manufofi da dama domin raya tattalin arzikin yanar gizo.
A nan gaba kuma, tattalin arzikin yanar gizo zai ci gaba da kasance babban karfin raya tattalin arzikin kasar Sin, kuma fasahohin kasar Sin za su ba da gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya, wanda ke fama da illolin da annobar cutar COVID-19 ke haifar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Advertisement

labarai