Tattalin Azrkin Sin Ya Karu A Rubu’in Farko Na Bana

Daga CRI Hausa

Alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin, sun fadada da kaso 18.3 a rubu’in farko na bana, wanda ya nuna sun farfado daga koma bayan da suka fuskanta shekara 1 da ta gabata .
Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar sun nuna cewa, raguwar kaso 6.8 da aka samu a rubu’i na farko na 2020, lokacin da al’amura suka tsaya a kasar domin dakile yaduwar annobar COVID-19, ya share fagen farfadowar ta bana. Tagomashin da bangaren fitar da kayayyaki ya samu a watan Maris, inda ya karu da sama da kaso 30, bisa la’akari da farfadowar tattalin arzikin duniya, misali ne na ci gaban da tattalin arzikin ya samu a baya-bayan nan.
Alkaluman GDPn sun fado ne tsakanin kiyasin da aka yi, inda ya haura hasashen kaso 17.9 da cibiyar nazari ta Nikkei ta yi, da kuma kaso 18 na cibiyar Macquarie, sai dai kuma bai kai hasashen kaso 19 da Reuters ya yi ba.
Farfadowar tattalin arzikin kasar Sin na da nasaba da karuwar fitar da kayyaki wanda ya ci gajiyar farfadowar tattalin arzikin duniya da kokarin da ake na riga kafin COVID-19 a duniya da kuma karuwar sayen kayayyaki a cikin gida. (Fa’iza Mustapha)

Exit mobile version