Tattaunawa Akai-Akai Za Ta Samar Da Fahimtar Juna Tsakanin Sin Da Amurka

Daga CRI HAUSA,

Da safiyar yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta kafar bidiyo da takwaransa na Amurka Joe Biden.

Tattaunawar da ta kasance irinta ta farko tun bayan da shugaban Amurka ya hau karagar mulki a watan Junairu, duk da cewa shugabannin biyu, sun tattauna har sau biyu ta wayar tarho.

Dangantakar Amurka da Sin, na cikin wani irin yanayi na ba yabo babu fallasa, biyo bayan irin katsalandan da takalar da Amurkar ke yi wa kasar Sin, kuma ganin cewa su ne kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya, irin wannan dangantaka ba za ta haifar da wani alfanu ga duniya kamar yadda ake muradi ba.

Sai dai, irin wannan tattaunawa, idan aka ci gaba da gudanar da ita lokaci zuwa lokaci, za ta yi matukar taimakawa wajen fahimtar juna da amfanawa kasashen har ma da sauran sassan duniya dake ganinsu a matsayin abun koyi.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, ya kamata Amurka da Sin, su tafiyar da harkokinsu na cikin gida da kansu, da sauke nauyin dake wuyansu a harkokin da suka shafi kasa da kasa kamar na sauyin yanayi da annobar COVID-19. Kowa dai ya san irin kokarin da kasar Sin ke yi a harkokin da suka shafi duniya, musamman ga ’yan uwanta kasashe masu tasowa. An kuma ga gagarumar gudunmuwar da ta bayar a zahiri, game da yaki da dakile annobar COVID-19 a gida da waje.

Da kuma yadda take kokarin yaki da sauyin yanayi ta hanyar daukar matakan rage hayaki mai dumama yanayi da inganta amfani da makamashi mai tsafta da raya muhalli.

Duk kokarin kasar Sin, ita kadai ba za ta iya sauke nauyin dake wuyan kasashen duniya ba, dole ne kasashe kamar Amurka da kawayenta, su ma su rika yunkurawa suna bada tasu gudunmuwa. Maimakon mayar da hankali kan fito na fito da suka da kakaba haraji ko takunkumai, kamata ya yi Amurka, ta nazarci kasar Sin domin kara fahimtarta, ta kuma daina kallonta a matsayin abokiyar hamayya.

Ba shakka kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka za ta tabbatar da muradun al’ummar duniya baki daya. Yadda rashin jituwa tsakaninsu za ta haifar da mummunar illa, haka kyautata dangantakarsu za ta haifar da gagarumin ci gaba, ba kadai ga kasashen da al’ummarsu ba, har ma da daukacin al’ummun duniya, domin alfanun da za a samu daga hakan, ba zai misaltu ba. Hadin kai tsakanin Sin da Amurka, za ta yi tasiri wajen dakile kalubalen da ake fama da su a duniya kamar na yake-yake da ta’addanci da yunwa da yaduwar cututtuka da sauransu.

Dukkan kasashen biyu na da buri ne iri guda, sai dai dabaru da manufofi sun bambanta, don haka, abu mafi dacewa shi ne, kawar da sabani a tsakaninsu da girmmama juna da manufofinsu da kuma cikakken ’yancinsu, da kaucewa shisshigi cikin harkokinsu na gida, da kuma tabbatar da hadin gwiwa da tuntuba a bangarorin dake bukatar hakan. (Faeza Mustapha)

Exit mobile version