Sakataren kungiyar matasan Fulani ta FUSADAN, Bala Bayero Fullo ya bayyana cewa hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki ne kawai hanyar magance matsalar taron da kasar nan ke fuskanta, amma ba da karfin bindiga ba.
Bala Bayero Fullo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, jim kadan bayan kammala wani taron bitar wayar wa da jama’a kai game da sanin dalilai da abin da ya kawo matsalolin da suke faruwa a Nijeriya, musamman a bangaren Fulani makiyaya.
Bala Bayero ya ci gaba da cewa, dole ne sai an kira al’umma waje daya, musamman Sarakuna da kuma jami’an tsaro domin lalubo me ke faruwa tun da farko kuma me ya haifar da wannan matsalar da nufin warware ta baki daya.
Ya kara da cewa, ana samun lokutan da ake kama masu mutane, wato Fulani, haka kawai a karbi abin hannunsu, ba su ji ba, ba su gani ba, kuma ba tare da sun yi wa kowa laifi ba, kuma a matsayinsu na ‘yan kasa, dole ya lalubo wannan da nufin magance lamarin, kuma a hukunta wadanda aka samu da laifi.
A game da dalilin da y asa suka kafa wannan kungiya ta matasan Fulani ta FASADAN kuwa, ya bayyana cewa domin wayar wa da Fulani baki daya kai a fannonin Ilimin addini da na Boko, “wanda hakika mun lura akwai bukatar hakan kwarai.
Ya ce, “mu Fulani masu son zaman lafiya ne kodayaushe a kowane irin lokaci, don haka muke fafutukar jama’a su fahimci hakan.”
Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja
Daga Sulaiman Ibrahim Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, alkalin kotun koli...