Da yake a wannan zamani ana samun cututtuka bila’adadin na zahiri da badini, Malaman Addinin Musulunci sun yunkuro haikan domin bayar da gudunmuwa kan yadda za a tallafa wa kiwon lafiyar al’umma. Baya ga cututtukan jiki na zahiri da aka saba gani, har ila yau Malaman sukan yi bincike mai zurfi don gano hakikanin abubuwan da ke janyo lalurorin da ake rasa gane kansu kuma a tsari mai kyau na zamani da Musulunci ya yarda da shi. Domin jin ire-iren wadannan cututtukan da yadda ake magance su, Shugaban Cibiyar Kiwon Lafiya da Hada Magungunan Addinin Musulunci ta Al-Yusra Kuma shugaban Kungiyar Masu Hada Magungunan Musulunci ta Kasa (ISTIFHAN), Dakta Jamil Nasir Bebeji ya ttauna da waklinmu, ABDULRAZAK YAHUZA JERE. Ga yadda hirar ta kasance:
Masu karatu za su ji dadi idan ka fara da bayyana musu asalin kafuwar wannan cibiya kafin jin ire-iren ayyukanta.
A’uzu billahi minasshaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Wasallallahu ala Rasulul karim, Sayyidina Muhammad (SAW). Tunda aka kafa cibiyar nan ta Al-Yusra a shekarar 1998 muke taimaka wa mutane da magunguna. Yau wajen kimanin shekara 19 kenan. Mun fara bude cibiyar a Abuja. Amma kafin nan mun fara ne da wani suna da ba mu yi mata rajista da shi ba wato ‘Markazis Salafiyyah’. Cibiyar mun yi mata duk wata rajista da ake yi, ta kai matsayin ‘Limited’ ma a yanzu. Muna kiyaye dokokin gwamanati ta kowace fuska da kuma kula sosai da hakkokin jama’ar da ke zuwa wurinmu.
Ayyukan da muke yi sun kunshi sassa daban-daban na kiwon lafiya bisa tsarin Addinin Musulunci. Muna mayar da hankali a kan gwaje-gwaje don gano irin ciwon da ke damun mara lafiya kafin mu bashi magani. Mukan yi gwaje-gwaje ta hanyar amfani da bayan gida, fitsari, yawu, majina, duba kalar fatar jiki da sauran su. Haka nan ma mukan bi hanyar addu’o’i kamar yadda ake yi a zamanin manyan malamanmu irin su Ibin Sina da ya rasu kamar shekara dubu daya da ta gabata, da su Arrazi da Ibn Hayyan da sauran su. Yanzu tunda an samu ci gaba kuma Shari’ar Musulunci ta ba mu dama mu dauki ci gaba matukar babu shirka babu sabon Allah a ciki, sai muke amfani da na’urar kwamfuta (Analyser) wadda ana iya ganin hatta hanjin cikin mutum. Na’urar tana nuna duk wata gaba ta jikin mutum domin a bincika a gano irin cutar da ke damun mara lafiya. Muna amfani da na’urar a dukkan rassan wannan cibiyar.
Wadanne rassa ne cibiyar take da su?
Saboda muna samun ci gaba sosai kuma mai ma’ana, mun fara kafa rassa a sassa daban-daban na kasar nan musamman a Arewa. Akwai a Kano da ke Na’ibawa a Road Safety, sannan akwai a Jigawa a Hakimi Street, muna da ita a Nasarawa a nan Mararaba a Abacha Road sai kuma nan Abuja a Garki 2, daidai Masallacin Jumma’a na Almuntada. Wadannan su ne rassanmu.
Akwai ‘yan damfara da suke bude shaguna da cibiyoyi na magani da sunan Al-Yusra kuma tabbas muna dab mu dauki mataki na shari’a a kansu. Mu dai wadannan rassan da na lissafo su uku su ne namu, kuma mu ba mu yawo da magunguna a mota ko a kwando da makamantansu. Duk inda muke muna kafa asibiti ne wanda yake kunsar sashen kwantar da mara lafiya, da ofishin likita, da shagon magani, wuraren karatun Alkur’ani da na rukuya da kuma na hade-haden magunguna. Muna kira ga jama’a su yi hattara da wadannan ‘yan damfaran. Hanyoyinmu na gano cutar mara lafiya nagartattu ne, muna amfani da na’urar kwamfuta da kuma addu’a don gano cutar da ta addabi mutum a jikinsa.
Ta wace siga kuke amfani da addu’o’i don gano cuta?
Ko akwai wani magani da cibiyar ta taba yi wa mara lafiya da take tinkaho da shi?
Akwai abubuwa da yawa. Babbar manufarmu ta kafa wannan cibiya ita ce warkad da mutane. Mutane da dama mun yi musu magani sun samu cikakkiyar lafiya da biyan bukata. Daga ciki ana samun mutumin da ya taba debe tsammanin haihuwa a rayuwarsa. Ya je har Turai hatta dabarar nan ta hada jariri an yi amma duk bai yi ba. Sai bayan ya dawo sai ya ji ni ina bayani a rediyo na karfafa masa gwiwa da kar ya debe tsammani sai ya zo wurinmu. Wasu da yawa bayan mun yi musu magani, zuwa wani lokaci sai su zo mun da naman rago su ce matarsu ta haihu an yi suna. Ka ga wannan akwai ban dadi sosai.
Har ila yau, yanayin yadda muke samun goyon baya ko ta wace fuska daga mutanen da muke mu’amala da su yana mana dadi sosai. Kusan za mu iya cewa mu ne muka bayyanar da wannan ilimin na magungunan musulunci sosai. Akwai magabatanmu kalilan a kan ilimin a Nijeriya amma idan ka kirga daga shekara 25 zuwa 30 da suka gabata, kusan an daina zancensa. Idan ma matsalar Aljannu ne ta kama mutum sai a je a yi bori a yi masa girka. Wasu kuma su je wurin Malami ya yi tofi; amma ba a fitar da abin a ilmance na tsarin zamani ba musamman irin yadda za a fitar da magunguna kala-kala da ‘packaging’ dinsu. Ka ga da muka fitar da abin kuma Allah ya san hanyarsa ce sai abin ya samu karbuwa a ko ina har ma ya kai ga wasu suna amfani da sunanmu suna cutar mutane. Duk mai nemanmu a nan Abuja cibiyarmu tana nan kusa da Masallacin Jumma’a na ‘Yan Izala (Almuntada) a cikin Garki. Ko a neme mu ta wannan layin: 07017790084, kai tsaye ma lambata ce.
Ko za ka zayyano wa masu karatu ire-iren cututtukan da cibiyar ke iya magancewa?
A gaskiya ba alfahari ba, babu wani ciwo da aka taba zuwa wurina neman magani da ban bayar da gudunmawa a kai ba. Abin da ya danganci cututtuka na Aljannu, tsafi (sihiri), kambun-baka ko kambun-ido, rashin samun mijin aure a wurin mace, rashin samun haihuwa ga ma’aurata da sauransu da dama.
Wani dan misali da zan bayar shi ne, a kwanan nan akwai wani babban mutum da ya yi ta yawon neman haihuwa bai samu ba. Ya lissafa mun manyan likitoci (na bature) da ya je wurinsa, wasu na san su, wasu kuma labarinsu nake ji amma bai samu haihuwar ba. Har ta kai ga an yi masa yadda ake daukar maniyyi a hada da kwan mace don a samu haihuwa amma abin duk ya gagara. Da ya zo wurina na bincike shi sai na gano abin da ya hana shi haihuwa wanda duk likitocin da ya je wurinsu din nan suka kasa ganowa. Akwai wasu jijiyoyi da ake iya samun su a marainan namiji kuma su yi mugun boyewa ta yadda ba za a iya ganinsu ba da sauki. Wani jijiyoyin kan fita masa ne a sakamakon wasa da al’aurarsa da hannu don ya biya bukatarsa ta sha’awa lokacin da yake matashi, wani kuma ba haka ba ne. To lokacin da mutum yake wannan wasan da al’aurarsa tunda ya riga ya fita hayyacinsa saboda karfin shafar da yake yi sai ya daddaki wurin da hannu; daga nan sai ya tattara jini ya zama sanadiyyar hana shi samun haihuwa. Amma likitocin da aka je wurinsu sun kasa gano matsalar, sai da ya zo nan na bincike shi na gano abin da ya hana shi haihuwa. Cikin ikon Allah ina fara bashi magani ba a yi wata biyu ba matarsa ta samu ciki. Su wadancan likitocin da sun gano matsalar za su iya magancewa amma tiyata za su yi masa, mu kuma ka ga magani muka bayar. Wannan yana nuna irin karfin da Al-Yusra ta yi wurin bincike kan cututtuka. Ba mu zama a wannan cibiyar da abin da muka sani a baya kurum, a kullum bincike muke kara yi game da cututtuka da magunguna na Musulunci da gargajiya da na baturen har da ma na su ‘Chinese’ da ‘India’, tunda Manzon Allah (SAW) ya umurce mu mu nemi ilimi. Yanzu idan ina hada maka magunguna da abubuwan ‘Chinese’ za ka yi mamaki har ka ga kamar kawai ni ba Bahaushe ba ne Dan Chaina ne. Haka idan na koma ina yi ma da na Indiya za ka ce ni Dan Indiya ne.
Baya ga matsalar rashin haihuwa, muna kuma magance matsalar lalacewar yara. Yanzu ma ga wani yaro can (yana mai nunawa da hannu), dan babban mutum ne da aka kawo mana ya haukace saboda shaye-shaye amma Alhamdulillah ga shi nan ya samu lafiya har ma mun fara fita da shi yana yawo. Har hauka muna ba da taimako a kai. Haka farfadiya, ciwon kai, ciwon ciki da sauransu.
Har ila yau, muna taimaka wa maza da mata ta bangaren gyaruwar aure. Matar da ke son karuwar kirji ko baya, rage tumbi ko rage jiki, kara yawan gashi ko jikinta ya kara kyau (ba tare da amfani da abin da zai jawo mata matsala ba, namu sha ake yi) don birge mijinta duk muna taimakawa. Sannan abin da ya shafi ciwon sanyi kamar a rika ganin farin ruwa yana fita daga gaba ko kurarraji ko kaikayin gaba ko dadewa duka muna taimakawa a kai. Hatta masu ciwon ‘HIB’ da ‘Cancer’ da sauransu muna taimaka musu da yardar Allah (SWT). In dai mutum ya zo wurinmu, insha Allahu za mu taimaka masa ya samu lafiya.