- Shin Sheikh Gumi Ne Ya Raba Tsakani?
Daga Nasir S. Gwangwazo,
Tun bayan da al’amuran tsaro suka ta’azzara a tsakanin jihohin Kaduna da Neja, gwamnatocin jihohin biyu suka hada kai wajen tafiya akan matsaya guda tare da aiki tare, don shawo kan matsayar. Daya daga cikin manufa ko dabara da suka tsaya akai ita ce ta kin amincewa da tsarin nan na tattaunawa da masu garkuwa da mutane, duk da cewa, tuni wasu jihohin suka amince da hakan kuma suke aiki da hakan.
Babban misali anan shine, yadda Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya kafe kai da fata akan lallai sai ya cigaba da tattaunawa da ’yan bindiga, mahara da masu garkuwa da mutane a jiharsa a matsayi wani mataki da yake ganin shine zai iya kawo karshen matsalar tsaron jihar ko kuma maganta ta.
Duk da cewa, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya dawo ya janye matsayarsa daga bisani, amma shi ma jima akan waccan akida ta tattaunawa da masu aikata ta’addanci a jiharsa a matsayin wani mataki da yake ganin zai iya kawo karshen matsalar.
Za a iya cewa, wannan ya biyo bayan ziyarar da malamin addinin Islama din nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya kai wa Gwamna Bello ne, inda ya yi masa huduba, kamar yadda yake yi wa masu garkuwar, yana mai jan hankalinsa da cewa, daukar matakin kin tattaunawa da ’yan ta’addar yankinsa kuskure ne.
Jim kadan bayan ganawar kuwa, sai Gwamna Sani Bello ya sanar da rungumar tsarin tattaunawar. Kwana biyu da faruwar hakan, sai masu garkuwa suka sako fasinjojin motar gwamnati da suka shafe kwanaki da dama da kamawa. Kana kuma, Gwamnatin Jihar ta kara sanar da cewa, tana kan tattaunawa da su, domin tabbatar da cewa, an sako dalibai da ma’aikatan makarantar Kagara.
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP A YAU cewa, a cikin yarjejeniyar da za a cimma tsakanin gwamnatin jihar da masu garkuwar akwai sakin wasu daga cikin ’yan ta’addar da aka kama, duk da cewa, majiyar ba ta tabbatar mana da cewa, za a biya wasu kudin diyya ba. Kodayake bayanai sun nuna cewa, a mafi yawan lokuta hakan na faruwa ko da kuwa ba a sanar ba.
Babban abin dubawa a wannan lamari shine, kasancewar Kaduna da Neja suna kan iyaka guda kuam sun dade suna aiki tare wajen shawo kan matsalar tsaro, shin an raba gari kenan a tsakaninsu ko kuwa za a dawo a cigaba da aiki tare? Idan za a dawo a cigaba da aiki tare, shin akan wane tsari; na kin tattaunawa da ’yan ta’adda kamar yadda Gwamna El-Rufai ya kafe akai ko kuwa shi ma zai bi Yarima ya sha kida ne, ya amince da tsarin tattaunawar?
Bugu da kari, shin yadda alakar Sheikh Gumi da Gwamna El-Rufai ta ke da tsami a siyasance, za a iya dawowa a koma tebirin shawara a yarda da tsarin malamin na tattaunawa a jihar Kaduna tunda dai ta fara bayar da nasara a Neja ko kuwa za a cigaba da jan tunga ne?
Kowa dai ya san yadda wadannan manyan mutane biyu suke da tsananin tsayawa kan ra’ayinsu. Shin wa zai dawo ya bi wani a cikinsu, kuma ta yaya Gwamna Bello zai gyara alakarsa da Gwamna El-Rufai, idan ta yi tsami? Lokaci ne zai tabbatar mana da hakan.