Hon. Ishak Ahmad na daya daga cikin fitattun ‘yan siyasar Jihar Nasara. A wata tattaunawa da ya yi da manema labaru a kwanan nan, ya yi sharhi kan cika shekara biyu da mulkin Gwamnatin Shugaba Buhari da ta Gwamna Al-Makura a karkashin APC. Ya ce akwai dimbin nasarori da kuma gyare-gyare, sai dai a wane sassa ne? Ku karanta hirar ku ji:
Gabatar da kanka ga masu karatu Hon….
Assalamu alaikum warahmtullah. Sunana Hon. Ishak Ahmad Ana. An haife ni a Keffi amma ni dan asalin Karamar Hukumar Kokona ne. Bayan na gama makarantana a Jami’ar Bayero ta Kano na fara aiki da Gwamnatin Jihar Nasarawa a Lafiya. Bayan an yi zabe a 1999 da Allah ya ba Alhaji Abdullahi Adamu Gwamnan Nasarawa, na koma aikin ‘protocol’ na tsawon shekara takwas. Na tsaya takarar danmajalisar jiha a nan Karamar Hukumar Kokona. Bayan shekara hudu na sake yin takarar danmajalisar wakilai a 2011 kuma na ci, kujerar da nake kai har zuwa 2015. A yanzu kuma ina gida ina jiran neman wata takarar cikin ikon Allah a 2019.
APC ta yi bikin cika shekara biyu a kan karagar mulki a ‘yan makwannin da suka gabata, a matsayinka na dan siyasa me za ka ce?
Alhamdulillah. Mu an kammala mulki da mu a lokacin Goodluck Jonathan har kuma Allah ya kawo Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Kowa ya san irin matsayin da cin hanci da rashawa ya kai a kasar nan kuma wannan matsala ce da take hana cigaba a duk inda aka same ta. Shi ya sa ma kafin zuwan Buhari sai da aka shiga yanayin da ba a iya biyan albashi. An samu tashin hankali saboda wahalar da ake ciki. Matsalar tsaro ta addabi mutanen kasa, Boko Haram, ‘Yan Neja-Delta, masu ‘kidnapping’ da dai sauran su. Shugaba Buhari ya zo ya tarar da wadannan masifu wanda zan iya cewa in ba irinsa ne aka samu ba, shawo kansu zai yi wahala. Ba a bin doka, babu ‘discipline’ kowa yana abin da ya ga dama saboda yana tutiyar shi dan wani ne. Amma cikin ikon Allah da Buhari ya zo sai ya ce matukar ba a kawar da cin hanci da rashawa ba babu abin da za a iya samarwa a kasar nan. Shi ya sa ya maida hankali duk wanda aka kama ya yi danasha da kudi a kwato; idan kuma ya cinye a kai shi wurin hukuma.
Boko Haram kowa ya san yadda suke kashe mutane, ban ce an gama da ita duka ba amma dai kowa ya san a cikin kashi 100 an magance 80. Batun taimaka wa matasa kowa ya sani an yi shiri a kai kuma an fara aiwatarwa, sai dai dole a kara da hakuri domin idan kana gida ba za ka san halin da ake ciki kan sha’anin mulki ba. Akwai abubuwa da dama da mutum ba zai sani ba. Kafin hawan Buhari, bai san ainihin halin da ake ciki ba, sai da ya hau ne tukuna ya fahimci yadda abubuwa suka yi mummunan lalacewa wanda zai dauki lokaci kafin a magance. Dole ‘Yan Nijeriya su yi hakuri a bashi dama ya gyara abubuwan kamar yadda ya dace.
Shugaba Buhari ya kuduri aniyar taimaka wa mutane, wato ‘empowerment’ amma fa a sani abin ba zai yiwu ba sai da kudi. A batun mai, Neja-Delta sun haddasa fitina ba a samun sa sosai, galibin man da ake amfani da shi shigo da shi ake daga waje, wannan ya kawo ‘recession’. Shi ya sa Shugaba Buhari ya ce to jama’a mu koma gona. Domin tun wuraren 1950 ko in ce kafin a gano mai da gona aka dogara wanda ba domin sha’anin Gwamnati ba da duk batun karkata wa man ma bai taso ba. Shi ya sa shi Shugaba Buhari da ya zo, sai ya nuna zai gyara sha’anin tattalin arzikin kasar ba sai da mai ba. Kuma kowa ya ga alamun cewa idan ‘yan kasa suka bashi goyon baya da hadin kai, za a samu nasara da ikon Allah.
Idan mun fahimce ka kamar kana nuna gamsuwa kenan da mulkin Shugaba Buhari a shekaru biyun nan?
Alhamdulillah, eh; haka ne. Mun ga abubuwan da ake ciki. Yawancin mutanen da suka yi danasha da kudin kasa ba su son ganin cigaban shi Shugaba Buhari. Suna tsoron a tona musu asiri, a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali har talakawa su fahimci miyagun halayen su wadannan mutanen. Amma duk bakin cikin mutum, Allah zai kare Shugaba Buhari.
Batun rashin lafiyar Buhari ya janyo wasu na ganin zai fi masa kyau ya koma gida ya huta bayan shekara hudu, kai mene ne ra’ayinka kan haka?
Jama’a ya kamata mu lura cewa ciwo daga Allah ne, haka nan lafiya daga Allah ne. A lokacin da Shugaba Buhari ya nemi kujerar nan babu alamun wannan rashin lafiyan a tare da shi. Ya yi kamfen a duk jihohin kasar nan. Kuma a yanzu din ma ba zama ya yi da rashin lafiyar ba, yana asibiti kuma zai samu lafiya da ikon Allah. Kar jama’a su rika yin shisshigi, ya kamata su bari shi da kansa ya yanke hukuncin cewa zai sake takara ko ba zai sake ba. Jama’a mu yi hakuri mu bashi lokaci ya dawo ya cigaba da mulkinsa. Buhari adalin mutum ne, yana da tsoron Allah, babbar damuwarsa taimaka wa talaka amma ba tara abin duniya ba. Idan ba mu manta ba, mulkin da ake yi a kasar nan kafin zuwan sa yana yawo ne a tsakanin wasu tsirarun mutane. Amma a mulkinsa ya ce yana so talaka ya ji dadi ya san cewa ana mulki tare da shi a kasar nan amma ba a bar wasu mutane ‘yan kadan suna abin da suka ga dama ba. Ya roki Allah ya ba shi iko duk alherin da zai kawo ya isa hannun mutanen da ke kasa wanda shi ya sa ake masa kulle-kulle da makirce-makirce. Babban abin da yake bukata a wurinmu addu’a.
Tun kafin jam’iyyar adawa ta zama mai mulki a kasa take mulkin Jihar Nasarawa, a matsayinka na dan asalin jihar kuma dan siyasa, yaya kake kallon salon shugabancin Gwamna Tanko Al-Makura?
Alhamdulillah. Na yi zamani da gwamnati guda uku, na yi ‘protocol’ shekara takwas a Gwamnatin Alhaji Abdullahi Adamu, na yi danmajalisar jiha lokacin Alhaji Aliyu Akwe-Doma sannan da danmajalisar tarayya a zamanin shi Gwamna na yanzu, Tanko Al-Makura. Wannan ya bani damar sanin kusan duk wani abu da ya faru a Gwamnatocin… Abin da zan fada a yanzu, zan fada ne a matsayina na dan asalin Jihar Nasarawa ba domin neman suna ko wani matsayi a wurin Gwamnan ba. Hakika da a ce tun kafuwar Jihar Nasarawa an yi irin yadda Gwamnan yake yi a yanzu tabbas da za mu fi haka. Kafin Al-Makura, idan ka shiga garin Lafiya babu wata alama baro-baro da za ta nuna ma cewa nan ne ‘capital’ na Jihar Nasarawa. Ya yi abubuwa da yawa na raya jihar kamar su hanyoyi, makarantu, gadoji, asibitoci da sauran su. A wannan fannin ya yi kokari fiye da sauran gwamnatocin da suka gabace shi. Sai dai kuma inda yake da gyara shi ne, an gyara makarantu amma babu malamai. Za ka samu a makaranta daya malami yana koyar da azuzuwa shida ko bakwai, ta yaya za a samar da ilimi ingantacce a haka? Asibitoci an gyara amma babu ma’aikata, kamar yadda ya yi wadannan ayyuka na cigaba ya kamata kuma a ce ya dauki ma’aikata aiki. Kuma batun albashin da ake bayarwa on ‘percentage’ ba alheri bane. Ya kamata ya ba ma’aikata albashin da ya yi alkawarin zai ba su don sun taimaka kwarai. Lallai muna kira Gwamna ya duba wadannan abubuwan.
Ba ka ganin wadannan matsalolin da ka lissafa sun samo asali ne saboda matsin tattalin arziki da kasa ta fuskanta?
Idan da akwai wannan matsala haka, lokacin da ya hau mulki ai an yi albashi. In da akwai damuwa a gwamnatin da ya karbe ta, me ya sa ya kara albashi zuwa ‘18,000 minimum wage’ kuma ya biya lafiya klau? Da akwai matsalar kudi a jihar da bai kara kudin ba ai. Watakila shi yana ganin don ya samu ya dawo kujerarsa a wa’adi na biyu ne ya sa ya yi hakan. Da kuma ya dawo yanzu mai yiwuwa hankalinsa ya karkata ne a wasu wuraren da ba wannan ba… amma dai tunda ma’aikata aiki suke yi ya kamata a ba su hakkinsu idan ma akwai wani abu da ke faruwa ya fito fili ya bayyana musu. Duk ayyukan cigaban da yake yi wasu ba su gani saboda akwai abin da ke musu zafi a rai game da shi Gwamnan… kusan kowa a Jihar Nasarawa Gwamnati ya sa wa ido domin ba mu da kamfanoni da jama’a za su raja’a masu. Kodayake, alhamdulillahi mun ji dadi da muka ga Gwamnan ya yi ‘agreement’ da Dangote a kan kafa kamfanin siga wanda zai kawo cigaba ga tattalin arzikin Jihar Nasarawa.. Dole dai a ce Gwamna Al-Makura ne ya fara gyara Jihar Nasarawa a yau har aka san cewa Lafiya ‘capital’ ne na jihar. Sai dai a duba batun yunwar da ake ciki.
Wasu ‘yan siyasa na kuka da Gwamna Al-Makura kan abin da suka kira da bai masu abin da ya dace da su ba, kai wace shawara za ka ba shi?
Yawancin manya da aka yi CPC tun farko da su ba su tare da wannan Gwamnatin yanzu irin su Shakana, Dakta Hassan Lawal, Tanko Wambai da sauran su. Gwamna Al-Makura ya gyara tsakaninsa da su, za su ba shi shawarwari masu kyau.
Kwanan baya mutane a Jihar Nasarawa sun fara neman ka fito takarar Gwamna kuma gashi zakakuran ‘yan siyasa na faman dawowa jam’iyya mai mulki ta APC a jihar, ko hakan yana ba ka tsoro?
Mulki na Allah ne.. (ya karanta ayar Alkur’ani). Allah yana ba da shi ga wanda ya so a lokacin da ya so. Shi Wadada da sauran su ban taba tunanin zuwan su APC zai bani tsoro ba, ba kudi ko ‘power’ yake ba da mulki ba, in da suna badawa da Buhari bai yi ba. Shi kansa Al-Makura da bai hau ba, mun san me ya faru. Mu bar wa Allah kayansa kawai. Wani ba zai ba ni tsoro ba. Duk mai neman takara ya fito ya bayyana wa talakawa abin da ya yi musu. Ni kuwa ku je ku bincika ku ji tun daga kan gyara ‘structures’ da ‘empowerment’ da samar da aikin yi. A shekara hudu kacal masu digiri 64 na samar musu aiki. Na yi bohole 180, na kai wuta kauyuka, har kwalta na yi daga Amba zuwa Kungwal. Wa ya taba yin haka a cikinsu? Abubuwan da muka yi ya sa Bayin Allah ke cewa mu fito. Muna shirin amsa kiran talakawa, insha Allah.