Kalubalen Da Ke Gaban Shugabanni — Jifatu

ALHAJI SABITU YAHAYA MUHAMMAD shine shugaban Rukunin Kanfanin Jifatu. Dan kasuwa ne wanda kullum burinsa bai wuce yadda za a tallafawa al’umma ta hanyar ilimantar da su da taimaka musu ta kowane fanni domin su ma su bada gudunmawa wajen ci-gaban al’umma da kasa bakidaya.

A tattaunawar da ya yi da wakilinmu MUSTAPHA IBRAHIM TELA ya yi kaimi wajen bayyana muhimmancin wannan lokaci na Ramadan da kuma aikin da ya kamata kowa yayi na nagarta wanda ya shafi shugabanni, ‘yan kasuwa, sarakuna,’ yan siyasa da dai sauran al’umma baki daya.

A matsayin ka na mai sharhin al’amurran yau da kullum me za ka ce kan yadda al’amurra ke gudana a yanzu?

Ina neman tsari da shaidan. Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai. Ba shakka shi halin da ake ciki yanzu ko dai yadda abu ke tafiya a wannan kasa duk wanda yake shugaba ya san da halin da kasar ta ke ciki a yanzu indai kana a matsayin shugaba ko kuma kana shugabanci a matakin sama can to kasan ya zama dole ne sai shugaba ko shuagabanni sun tashi sun kalli halin da kasa da `yan kasa suke ciki a yamzu wato a Nijeriya a wannan Nahiya ta Afrika, kuma kullum abin da ake magana yanzu idan ana maganar wata babbar kasa a kowace Nahiya ta duniya to fa ita wannan Nahiyar ake nufi da maganar mu a Nahiyar Afrika in ana maganar Nijeriya to ita kanta Nahiyar ake nufi domin Nijeriya ita ce Afrika wasu za su ce kamar Afrika ta Kudu ce babba, amma ba haka ba ne Nijeriya ce ke da wannan matsayi a wannan Nahiya tamu ta Afrika saboda dalilai masu tarin yawa wanda idan mutum ya bincika da kansa zai gane cikin sauki kuma wannan shi ne abinda ake lissafi da shi a duniya a yau.

To kuwa tunda haka ne yau to ka ga akwai babban kalubale ga shugabannin mu na Nijeriya da su tashi tsaye su yi aiki kada su zama marasa manufa, marasa alkibila wanda basu san abin da ke tafiyar da shi ba a yanzu.

Kada kawai ka dauka kai Shugaban Kasa ne a inda kake ko kana dan majalisa ko kana Gwamna ko kana Sarki ne ko kuma kana rike da mukamin soja ko dan sanda ko sauran mukamai da ake da su. To duk wanda ya samu kansa a daya daga cikin mukaman nan da na lissafa ya zame masa dole ya kalli abin da ya sa aka saka shi a cikin wannan rukuni domin sai da aka yi lissafi aka saka ka a inda aka saka ka ana sa ran za ka bada gudunmawa ne dai-dai da yadda girman kasar ke daraja ka da Nahiyar da kake da Nahiyar baki daya.

Kuma baya ga wannan akwai wata matsala ita ce maganar alfarma, wannan alfarma ta zame mana tamkar kansa, ta zama matsala ta kawo mana matsaloli a wannan kasa kuma kullum maganar mu itace kwaya daya kullum shi ne shugabanni su dai na maganar son rai domin son rai  shi ne ke kawo maganar alfarma wadda itace babbar matsala domin muna dabawa kanmu wuka da kanmu mu kashe kanmu da kanmu mu je mu binne kanmu da kanmu wannan babbar matsala ce ga wannan kasa wadda ya kamata a yi gyara a kai.

 

 A matsayin ka na wanda ya ga jiya ya ga yau a siyasar Nijeriya, wane mataki kake ganin za a dauka domin kawo gyara a kasar nan?

Abin da zai kawo gyara shi ne wanda wasu basa so a yi magana shine nagarta. Wato gaskiya da rikon amana. A yau gaskiya da amana ta yi kadan sosai a tsakanin ‘yan Nijeriya duk da ba za a ce an taru an zama daya ba amma a kididdiga ta masana da a kayi mana nagartar ‘yan Nijeriya ba ta wuce kashi uku cikin 100 ba. Ka ga kenan ta yi kadan ina laifin in ba a samu 100 cikin 100 to a samu 70 cikin 100.

Kuma wannan nagartar in kace a yi ta domin ta zama dole in ana sun ci-gaba in kai Shugaban Kasa ne ko dai a yi kokarin kashe shugabancinka ko a yi kokarin raunata ka. Haka in kai Sarki ne kake shimfida gaskiya da adalci sai a yi kokarin kashe sarautar ka ko kai kanka haka in kai dan kasuwa ne sai a yi kokarin kashe kasuwancin ka ko kai kanka, idan kai dan siayasa ne sai a yi kokarin kasheka ko a yi jana’izar siyasarka. Haka lamarin yake idan kai Malami ne sai a yi kokarin kasheka ko a bata maka suna. To haka dai duk wata daraja da kake da ita idan ka ce dole sai an yi yadda ya kamata to sai an yi kokarin ganin bayanka in dai ka ce sai anyi abu na gaskiya.

To kuma a gaskiya wannan ba zai zame mana abu mai alkhairi da mu da ‘ya’ yanmu da jikokin mu ba dole a canja a yi abu mai kyau duk inda za a bawa mutum wani mukami dole a tabbatar nagari ne to da an yi masa maganar a yi nagarta to ita zai yi akan kansa da kasarsa da abin da ya shafi al’umma bakidaya.

 

Wane kira za ka yi ga ‘yan kasuwa musamman a wannan watan na Ramadan?

Ramadan ai shi jamlatan wahidatan ne wato ma’ana ya hada komai da ake magana namu na mu’amularmu musulmi domin ko wacce mu’amula so a ke yi ta canja daga inda take in mai kyau ne ta kara kyau in mara kyau ce ta yi kyau kuma mu ‘yan kasuwa kada mu dauka cewa wannan watan shine watan da duk bukatarsa za ta biya ta hanyar kara farashin kaya a’a hakan bai dace ba abin da ya kamata mu yi shine abin da ake cewa gaba, a na gasar aikata alkhairi bisa la’akari da yadda wasu abokan zamanmu kirista suke yi na rage farashi a lokutan bukukuwan kirismeti to muma ko da bamu dau komai ba na siyasar da suke sanyawa ta addini to wannan ya kamata mu fisu gasa a wannan fage.

A kashin kaina na rage farashin kaya a lokutan bukata akalla ta azumin watan Ramadan wannan kuma shine kiranmu ga ‘yan kasuwa.

 

Jama’a shaida ne kan rage farashi da kuke yi a lokacin azumi, amma kuma wannan shekarar an samu tashin farashi a kasuwa. Shin wannan rahusar da kuke yi tana nan ko kuwa?

Gaskiya wannan rage farashin yana nan kamar yadda aka saba domin mun kai shekaru goma ko fiye da haka muna yi saboda haka canjin yanayi ba zai sa mu canza daga abin da muka san muhimmacin sa ba. Kuma muna rage kashe daya cikin goma ne duk shekara haka muka yi a wannan kamfanin na Jifatu.

 

Ya batun gudunmawa da wannan kamfani ke bayarwa duk shekara ta musamman a wannan wata na Ramadan ta ‘yanta daurarru daga kurkuku. Ina aka kwana a bana?

Eh ba shakka a na yi kuma wannan shekarar ma da ikon Allah za mu yi abin da ya kamata dai-dai da yadda doka ta tanada, a wadannan jihohi da muka saba kamar nan Kano, Katsina, Bauchi, Kaduna, Zamfara da kuma Jigawa in Allah ya so daga cikin su zamu zabo mu yi wannan aiki na ‘yanta daurarru daga kurkuku.

 

Idan muka koma fagen siyasa, yau shekara biyu da kafuwar wannan Gwamnati. Me za ka ce kan kalubalen da kasa ke fuskanta?

To babban kalubale shine wasu shugabanni sun yadda canji ya zo wasu kuma a cikin su ba su yadda ba ka ga wannan babban kalubale ne da shugabannin kasa suke fuskanta a yau.

A wannan lokaci da duniya ta zama kauye daya to dole ne kowa ya yadda ko baka yadda ba wannan zamanin zamani ne da za a bi gaskiya ko gaskiya ta yi aikin ta, ba makawa wannan karni karni ne na canji kuma mutane masu gaskiya yake bukata masu asali in baka yi ba a yau in an kawo wani, wani zai yi wannan haka yake saboda haka kowa yayi amfani da damar da ya samu wajen aikata gaskiya da abin da ya kamata, yanzu ba a bukatar sakarci ko bambadanci.

Kira na ga shugabanni shine su yi gaskiya kuma su ji tsoron Allah su canja daga abu mara kyau zuwa mai kyau wato daga lalaci zuwa jarumta daga sakaci zuwa tsayuwa tsayin daka. Allah yasa mu dace a dukkan ayyukan na Ibada da yau da kullum.

Exit mobile version