Aminu Aminu Bizi shi ne shugaban Kamfanin hada-hadar kudade ta wayar Salula (Cashless Mobile), wanda Bankin Kasa ya amince da su ci gaba wayar da kan ja’ama’a domin fahimtar tsarin mu’amalla da kudi ta hanyar wayar salula. A tattaunawarsa da Jaridar LEADERSHIP Hausa, ya bayyana irin nasarorin da aka cimma tun lokacin da aka kafa wannan kamfani, sannan kuma ya yi tsokaci kan shirinsa na tallafawa Marayu. Haka kuma Ya yiwa abokan mu’amallar wannan kamfani bushara cewa yanzu haka Jihohin Kaduna, Kano, Jigawa da Bauchi tuni sun amince da bawa wannan kamfani wasu muhimman ayyuka musamman tattara haraji da kuma jagorantar biyan wasu masu ayyukan abinci a Jigawa da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Mene ne makasudin kafa wannan kamfani?
Idan muka koma baya kadan, za mu tuna lokacin da ake amfani da tsarin ban gishiri in baka manda, aka zo batun amfani da wuri; har kuma ka fara tunanin bude Bankuna, zuwa musayar kudi ta hanya kwamfuta.
Saboda haka idan aka dubi Kasa irin Kenya wadda yawan mutanenta ba su wuce jihohi biyu na Nijeriya ba, kuma yanzu haka tana cikin kasashen da a duniya da su ka yi ci gaban da aka daina rungumar kudi a jakukkuna, wanda komai za ka saya sai dai ka mika katin ajiyar ka na Banki a cira ba tare da bata lokacin ba. Saboda haka kamar yadda duniya ta ci gaba an daina rungumar kudi a Kenya ko saniya ka saya sai dai ka biya ta Banki ba tare da wani ya sani ba.
Tun da yanzu al’amarin ya fara daukar Hankalin wasu Jihohi wadanda suka fara aminta da wannan tsari, shin ko zamu iya jin inda aka kwana ta wannan fuska?
Ina tabbatarwa da ma’abota karanta wanann Jarida mai albarka cewar yanzu haka Babban Banki Kasa (CBN) ya amince da wannan Kamfani namu cikin kamfanoni uku da aka sahalewa ci gaba da wayar da kan al’umma wannan sabon tsari domin mu ma hakarmu ta cimma ruwa.
Yanzu Kamfanin Bizi Cashless Mobile shi ne wanda ke aiki ko na ce wakilin Bankin Access a wannan bangare. Ina tabbatar maka tare da yin bushara cewar jihohin Kaduna, Kano, Jigawa, Gombe, Bauchi da Osun duk muna tare kuma har sun bamu wasu ayukan da suka shafi hadahadar kudade.
Shin ranka ya dade mene dalilin da ya sa kamfaninka ya fi mayar da hankali wajen tallafawa marayu?
Duk da cewa ni na tashi da iyaye na amma daga baya duk sun mutu kuma ni ne babba a gidanmu, yawancin kannena mata ne, kuma na duba irin matsalar da ke fuskantar marayu mussamman mata wanda idan ba a yi hankali ba a lokuta da dama shi ke jefa su cikin wani hali maras kyau, hakan tasa na ga da cewar fara neman hanyar tallafa masu ta hanyar daukarsu aiki tare da mayar da su wakilan wannan kamfani a unguwanninsu. Hakan ya zama wani tubali na sake gina rayuwar wadanan marayu da suke gudanar da wannan aiki kuma suke samun abin sawa a bakin salati. Yanzu haka da yawa daga cikin wadannan marayu sun fi karfin abinda da za su ci sai ma taimakawa ‘yan uwa da suke. Mun kaddamar da wannan tsarin tallafawa marayu a Kaduna, Kano da kuma Jigawa.
Ya dangantakar wannan kamfani ta ke da Gwamnatocin Jihohi musamman na arewacin kasar nan?
Muna godiya tare da jinjinawa gwamnonin da muka fara wannan aiki tare, musamman kamar yadda na sha fada wannan tsari na Mobile money shi ne tsarin da gwamnatoci za su fi amfana, kuma ina tabbatar maka da cewa nan da shekara ta 2020 kamar yadda babban Bankin Kasa ya shelanta, matukar matasa da gwamnatocinmu suka rungumi wannan aiki ka’in-da-na’in, ko shakka babu zuwa wancan lokaci za a daina maganar Man fetur a kasar nan, domin sana’a ta isa ko ina kuma mata da maza kowa ya samu abin da zai ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsa.
A bangaren gwamnati misali jihar Kano nan bada jimawa ba zamu kaddamar shirin karbar haraji, ina tabbatar maka da cewa daga lokacin da muka fara wannan aiki jihar Kano idan dai batun kudaden harajinta ne, muna tabbatarwa da gwamnti cewar ta sha kuruminta namanta na jakarta. Domin duk lokacin da mai shago ko kanti ya biya harajinsa cikin mintuna kalilan zaka ji alert kudin ya shiga lalitar Gwamnati ba kira ba abinda zai ci gawayi.
Kamar yadda ake yi wa al’ummar arewacin kasar nan musamman matasa da kallon cima zaune, shin ko wane kira zaka yi gare su domin rungumar wannan shiri?
Al’amarin matasanmu na bani mamaki kasancewar abinda suka fi tinkaho da shi bai wuce babana ne Gwamna, Kwamishina ko kanin babana ne shugaban karamar hukumarmu ba, saboda haka me zan samu shi ne babban abinda ke gaban irin wadannan matasa. Wanda kuma duniya an wuce wannan wurin, ba wanda zai samun wani abu idan bai tashi tsaye ya rungumi neman na kansa ba, dubi wadannan marayun, musamman ‘yan mata da a baya sai saurayi ya zo ya basu sannan suke samu, kuma hakan a lokuta da dama kan jefa su cikin wani hali maras kyau, amma yanzu cikin wadanda muka bawa irin wannan dama ba su ma da lokacin sauraron samari, kullum suna duba ina suka dosa.
Wani abin sha’awa ma shi ne, alheran wannan tsari a fili yake duk lokacin da wadanan wakilan kamfani suka yi mu’amala da wani kwastoma suna da nasu kaso da ake fitar masu. Wannan ne ya bamu damar samun ayyuka a Jigawa wanda muke biyan masu aikin ciyarwa, domin idan ka dubi mutumin dake Karamar hukumar Kirikasamma, a ce sai ya zo Hadeja sannan ya karbi gudunmawar gwamnatin Tarayya na Naira dubu biyar, kudin mota kadai sai ya zuki dubu daya da doriya, amma saboda muke da wakilai a lungu da sako ya sa gwamnati ta aminta da bamu wannan aiki, wadda sai a je har kofar dakinka/ki a biya ki hakkinki. Haka lamarin yake kan maganar albashi, ba jin alert na shigar albashi ne tashin hanakalin ba, a’a tunanin dogon layin da za ka tarar a bakin bankuna wuraren cirar kudin shi ne babban tashin hankali. Amma ta hannun wadannan wakilai na kamfani Cashless Money, kawai sai ka je wurin guda cikin wadancan wakilai ka yi masu transfer na albashin naka da zarar sunga alert su kirga kudin ka su damka maka sai dan alawus dinsu da za a cire masu.
Ganin yadda bude asusun ajiya ke wahalar da mutane musamman na karkara, shin ko akwai wani sauki da wannan tsari ya yiwa masu sha’awar shiga cikin shirin?
Idan kana bukatar bude asusun ajiya da cashless money kawai idan wakilan wannan kamfani suka zo abinda suke bukata shi ne lambarka, ba ruwansu da BBN ko wani ID card, kuma babban amfanin wannan tsari shi ne yadda ko barawo ya ce ka basu lambar ajiyarka idan ka ba shi cikin mintuna talatin za a damke shi. Saboda haka wannan tsarin ya fi duk wani tsari samun kudi cikin sauki matukar mutum zai mai da hankali tare da rike amanar al’ummar da suka aminta da mu’amala da shi.
Mene fatan ka ga al’ummar Kasa wadda duk wannan aiki don ci gaban kasa da al’ummarta kuke yi?
Haka ne fatanmu shi ne jama’a su yi kokarin duba irin ci gaban da duniya ke ciki a halin yanzu, idan dai za a ce kasa irin Kenya za su shiga rukunin kasashen da aka daina rungumar kudi a buhu, sannan kuma a dubi Nijeriya wadda ta jima da sanin ciwon kanta, amma har yanzu al’ummarmu an bar mu a baya, kullum sai ka ga mai kudi ya tara kudi sama da milyan goma a daki, wannan ai ba dabara bace, ko ba barawo akwai ibtila’in gobara da makamantan haka, amma idan kudinka na Banki ba kira ba abinda zai ci gawayi. Saboda haka muke tabbatarwa da jama’a cewar wannan Kamfani ya shirya tsaf domin ganin nan da shekara 2020 kamar yadda babban Bankin Kasa ke fatan gani, za mu yi duk mai yiwuwa domin ganin mun wayar da kan jama’a sun rungumi wannan shiri. Muna fatan Allah ya karawa shugabanninm kyakkyawan tunanin bujiro da ire-iren wadanann basiru domin amfanin jama’ar kasa.