Tattaunawa Ta Musamman Da Marubucin Littafin ‘Zuciyarka Jagorarka’, Mustapha Abdullahi

‘Zuciyarka Jagorarka’

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake kasancewa daku a filin ku na FASIHAI. Shafi  da ke zakulo muku shahararrun marubuta da mawakan hausa, tare da wakiliyar LEADERSHIP A YAU, SADIYA SIDI SAID, wacce aka fi sani da SIDIYA.

A wannan makon muna tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI, daya  daga cikin marubutanku. Ya nishadantar da ku a cikin littafai da dama, inda kuma shine ya rubuta fitaccen littafin nan mai cike da dimbin ilimi da hikima mai suna ‘Zuciyarka Jagorarka’. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Malam Mustapha, masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihinka?

Masha Allah. Suna na Mustapha.  An Haife ni a unguwar Zango da ke bayan asibitin Murtala cikin birnin Kano. Na fara karatu ne a makarantar Madrasatu Simarul Kur’an dake Fagge. Bayan na gama na tafi BUK Staff School inda na yi karatun firamare, bayan na gama ta,  na shiga makarantar Aminu Kano Community Commercial College,  daga nan na koma bangaren Kimiyya a makarantar Sheikh Bashir El-Rayyah.  Bayan na gama ta, yanzu haka ina jami’ar Bayero (BUK) ina karatun likita.

 

Ya aka yi ka tsinci kanka a harkar rubuce-rubuce?

Saboda ina yawan karance karance, kwatsam sai na tsinci kaina ina rubutu

 

Tsawon wani lokaci ka dauka a harkar rubutu, sannan daga fara rubutunka zuwa yanzu littafi nawa ka rubuta?

Shekara biyar kenan zuwa shidda. Na rubuta littafi guda biyar, na buga biyu

 

Ko za ka iya lissafowa masu karatu su?

  1. Zuciyarka Jagorarka 1, 2.Open The Page, 3. Zuciyarka Jagorarka 2, 4. Lafiya Uwar Jiki sai na 5. Kuotes for Thought

 

Daga cikin jerin gwanen littafanka wanne ne bakandamiyarka, ma’ana wanda ka fi so ka kuma fi jin dadi yayin rubuta shi? Sannan kuma wanne yafi ba ka wahala wurin rubutun shi?

Bakandamiyata shi ne Zuciyarka Jagorarka.  Wanda yafi ban wahala kuwa Open the page

 

A dunkule wasu sakonni wa’yannan littafai guda biyu ke dauke da shi?

Na Hausa su na karawa masu karatu illlmi ne game da yadda jikinsu yake. Na turancin kuma su na zaburar da masu karatu wajen zage damtse wajen neman ilimi

 

Malam Mustapha na da aure ko kuma sai dai niyyar yi?

Ba ni da aure, sai dai niyya.

 

A ganin ka rubutu dace ne da cancanta ko kuwa kowa ma ze iya zama marubuci/marubuciya?

To, wannan tambaya taki na da wahalar amsa. Amma a  tunanina, Kowa zai iya zama marubuci ta hanyar yawan karance karance da cudanya da marubuta da kuma naci. Duk da cewa wasu da baiwar iya rubutun ake haifarsu.

 

Ta fannin kalubalen rubutu me ya fi ci maka tuwo a k’warya, sannan masu karatu za su so jin irin nasarorin da ka samu a harkar rubutu?

Samun lokacin yin rubutu, musamman tun da karatu irin namu na da cin lokaci, sa kuma samun maudu in da za ayi rubutun akansa

 

Me Malam Mustapha yafi so ta bangaren, abun sha da kuma nau’in sutura?

Ina son kankana sosai. Sutura kuma ina son kufta

 

Ka taba wallafa littafi?

Eh, na wallafa littafi, Zuciyarka Jagorarka da kuma ‘Open The Page’.

 

Ya kake ganin kasuwancin wallafa littafai da kuma rubutun yanar gizo, wasu kance rubutun yanar gizo na nema ya k’wace kasuwar littafai, shin ya abun yake?

Eh kwarai kuwa zamani ya zo da dole marubuta su fadada tunaninsu, su rungumi yada rubutunsu a yanar gizo.  Tabbas akwai dubban mutane masu karanta rubutunmu. Kenan mutum zai iya siyar da rubutun sa a wannan kafa

 

A iya wallafa littafai wasu da yawa su ka san malam Mustapha. Kasancewar muna wani karni dake tafiya da zamani, kai ba ka rubuta labaran wasan kwaikwayo ne ko masu dogon zango?

Eh to, ba na rubutun wasan kwaikwayo, haka ma na mai dogon zango, amma ina tunani akai

 

Wani shawara za ka bai wa masu karatu har ma da marubuta ‘yan uwanka?

Marubuta hadin kai,  zurfin tunani, da hikima, sai kuma dagewa wajen neman gogewa da kwarewa a fagen rubutun. Makaranta kuma yin uzuri ga marubuta,  babsu shawara,  nuna musu batutuwan da su ka dace ayi rubutu a kansu

 

Su waye taurarinka cikin marubuta mawallafa da ma na yanar gizo, wanda rayuwar shi/ta ke burge ka?

Ado Ahmad Gidan Dabino,  Tijjani Muhammad Musa,  Fauziyya D Sulaiman,  Adamu Yusuf Indabo,  Khalid Imam,  Badamasi Aliyu, Bello Sagir da sauransu.

 

Wani sako ka ke dauke da shi zuwa ga masoyanka, sannan kamar ga masu neman littafanka, ta wace hanya za su iya samu a saukake, akwai wa’yanda ka sake a yanar gizo ne ko kuma se dai a kasuwa?

Ina yi wa masoyana fatan alkhairi da kuma nuna godiya ga addu’an da su ke yi min. Allah ya bar zumunci.  Game da litattafaina,  na saki Zuciyarka Jagorarka da open the  page a okadabooks na yanar gizo. Haka kuma ana samun littafin Zuciyarka Jagorarka a kasuwa da supermarkets na Kano.  Na turanci kuwa ina sa rai zai shiga kasuwa a wannan shekara insha Allah

 

Mene ne burinka nan gaba kadan game da rubutunka?

Burina shi ne rubutuna ya shiga duk wani lungu da sako inda ake yin hausa domin jama’a su ilimintu, su san yadda jiki yake da yadda za su inganta lafiyar su, da kuma kara tunatar da su muhimmancin karatu da neman ilimi

 

Malam Mustapha, LEADERSHIP A YAU na yi maka fatar alkhairi.

Nagode kwarai. Masha Allah.

Exit mobile version