Abba Ibrahim Wada" />

Tattaunawa Ta Yi Nisa Tsakanin Manchester United Da Paulo Dybala

Rahotanni daga kasar Argentina sun bayyana cewa tattaunawa tayi nisa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da kuma dan wasan gaba na Jubentus, Paulo Dybala, a kokarin da dan wasan yakeyi na barin kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
Dan uwan dan wasan kuma wakilinsa ya bayyana cewa tabbas dan wasan zai bar Jubentus a karshen wannan kakar saboda baya jin dadin zaman kungiyar sannan kuma akwai wasu ‘yan wasan da suma zasu bar Jubentus din.
Dybala, mai shekara 25 a duniya ya zura kwallaye 10 ne kawai a wannan kakar a Jubentus kuma kwallaye biyar daga ciki a gasar Siriya A wanda hakan yasa yake ganin akwai bukatar yabar kungiyar domin zuwa inda zai dinga samun damar buga wasa.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Manchester United tun cikin watan Aprilu take tattaunawa da dan wasan domin ganin ya koma kungiyar a kokarin da kociyan kungitar yakeyi na kara karfin bangaren zura kwallo a raga.
Dan wasan dan, ya zura kwallaye 78 cikin wasanni 181 daya bugawa kungiyar Jubentus tun bayan daya koma kungiyar daga kungiyar kwallaon kafa ta Palermo a shekara ta 2015 kuma ya wakilci kasar Argentina a gasar cin kofin duniya.
Har ila yau Manchester United tana dab da kammala siyan dan wasa Daniel James daga kungiyar Swansea City sannan kuma tana cigaba da neman dan wasan baya na Crystal Palace, Aaron Wan-Bissaka, dan kasar Ingila

Exit mobile version