Balarabe Abdullahi" />

Tausayi Ya Sa Na Ke Kula Da Jiriran Da Aka Yar –Hajiya Uwa Uwar Marayu

Wakilinmu, BALARABE ABDULLAHI ya sami damar zanta wa da HAJIYA UWA YUSUF, wadda aka fi sani da UWAR MARAYU da ta ke Unguwar NDC, kusa da masallacin tsohon ministan aikin gona Alhaji Sani Zangon Daura, matar Wazirin NDC Alhaji Yusufu a garin Kaduna, inda ta fara bayyana wa wakilinmu dalilan rungumar kula da duk wani jariri ko kuma jariri da aka tsinta a kusa ko kuma a inda ta ke. Ga yadda tattaunawar ta da wakilinmu ya kasance,
Yaushe ki ka fara wannan aiki na karban jira – jiran da aka yar?
A gaskiya farar da garaje b azan iya bayyana yawan shekarun da na fara wannan abu ba, amma zan iya cewar na wuce shekara ashirin da fara wannan aiki da na sa kai na.

Kafin ki fara kin nemi izinin mijinki ne?
Lallai ban fara wannan abu ba, said a na bayyana wa mai gida cewar, ina son in an bayar da sanarwar an tsinci jariri ko kuma jaririya, ina so a ba ni in raine shi ko kuma in rain eta, nan ta key a amince ma ni.Kuma day a ke shi ne Wazirn wannan gari [NDC] ,duk lokacin da aka
tsinci wanda aka yar sai a bayyana ma sa, bayan an bayyana wa Sarkin NDC, nan ta ke sai ya ce a kai gidansa, wajen matarsa, wato ni ke nan.Kuma da zarar an kawo ma ni wanda aka tsinta, a lokacin sai in ji kamar ni ne na haife shi ko na haife ta.

To ya batun kula da wanda aka kawo ma ki
To, a nan dole in yi godiya ga mai gida na, na yadda a duk lokacin da aka kawo jariri ko kuma jaririya a gidannan, ya na yin duk abin da ya kamata, na kula da abin da aka kawo ma ni, wato tun daga abincinsa da kuma duk wani batu
da ya shafi lafiyarsu.

To, al’umma fa, ki na samun tallafi daga jama’a kuwa?
To, ba na ce ba na samu ba, amma mafiya yawan lokuta, ni da mai gida na da kuma sauran al’umma mu ke kula da su.

Wasu za su yi tunanin ba ki taba samun haihuwa ba ne, shi ya sa ki ke kula da wadanda ake yar wa, haka ne?
To, ka san jama’a ba ka ra sa su da fadin batutuwan da suke bakinsu, a takaice, zuwa yanzu ina da ‘ya’ya har da jikoki ma su yawan gaske.Kuma kula da wanannan jira – jirai, har da su a ciki.

A kwai maganar da ki ke yi ma su kan wadannan jira – jirai?
Lallai akwai kuwa, domin ni da mai gida na, mun sha tarasu, mu ba su umurnin cewar, ko da bamu da rai, su ci gaba da kula da jiran da mu ka bar su, kuma sun karbi wannan wasiyya da hannu biyu a shekaru da dama da suka wuce.

Yau ga shi mu na tattaunawa da ke, wani karin bayani za ki yi ma na, na wannan jiriri da ke hannunki?
Wannan jiriri, an tsice shi ne a gidan bulo, kusa da gidan madara a nan NDC,an yarda shi, sai wani mai gadi ya fito aikinsa da sassafe, sai ya ji motsi a cikin ciyawa, da ya matsa kusa, sai ya ga jiriri ne ke kwance a cikin ciyawa, ya na kuka, muryasa ba ta fita,da ya dauka, sai ya kai gidan Sarkin NDC, sai Sarki ya ce a kawo ma ni, ana kawo wa sai na karba, na yi ma sa wanka, na sa ma sa tufafin sanyi.

A kwai shawarar da za ki ba iyayen yara kan wannan matsala ta yawaitan yar da jira – jirai ta yawaita?
To, babbar shawarar ita ce, iyaye a kara sa ido kan mururin yara mata,musamman iyaye mata, kuma a san cewar, duk dan adam da Allah ya halitta, a kawai kaddara da za ta iya faruwa da shi.In an dauki wadannan shawarwari, matsalolin za su iya zama tarihi, ko kuma su ragu.
Kuma ina tabbatar ma ka da cewar, duk abin da ya bata ma ni rai, in na gansu a gaba na, na kan sami wani farin ciki a zuciya ta fiye da tunaninka,to ni ke na da ba ni na haife su ba?, me ka ke yin tunanin halin da wadanda suka yar da su suke ciki, matukar suna raye? Farrin ciki ko kuma bakin cikin ina wanda suka Haifa, suka yar ya ke a halin yanzu? Kuma wannan jariri Mahmud, shi ne na tara,dukkansu na yanka ma su rago, sai dai yara hudu sun rasu, yanzu ina da biyar a wannan gida.

Baya ga mai gidan ki, wasu na baki tallafin lura da su kuwa?
Ina samun tallafi wajen wasu mutum biyu, Alhaji Salisu Kura na tallafa ma ni, amma tun da ya bar wannan gari na NDC, ba na samun tallafi daga wajensa, sai baba na Alhaji Sani Zangon Daura, ya dauki yara biyu, ya sa su a makarantan Islamiyya da kuma Makarantar boko mai tsada, kuma ya na aiko ma ni da kayan abinci, domin ciyar da wadannan marayu, Allah ya sa ka ma su da alherinsa, amin.

Wasu matsaloli ke damun ki a halin yanzu, na kula da wadannan yara?
Babban matsala ita ce na karancin kudi da zan rika sayen madara domin ba kananan jira – jirai,amma abincin da mu ke ci a wannan gida, ba mu da matsalarsa dare da kuma rana, sai in ce Allah ya sa ka wa mai gida na da alherinsa.

Wani abu ne ba za ki taba mantawa ba da ya faru da ke, a dalilin wannan abu da ki ka sa kan ki?
Lallai a kwai jaririya da na sa ma ta suna Jamila, kwana daya da kawo ma ni ita, sai na kai ta asibiti, da aka gwada ta, sai aka ce ma ni ta na da cutar Sida, sai wata Nas ta ce ma ni in je in ba wata wannan yarinya, domin zan sha wahalar kula da ita, sai na ce ba zan ba kowa ba,suka yi ma ni bayanin yadda zan rika kula da ita, da yadda zan rika ba ta magani,sai aka kwantar da ita a asibitin Nasin hom, a cikin Kaduna, ba a kula da ita, wata rana ta mimmike ma ni, ta na kuka, ta na duba na, ni ma ina kuka ina dubanta, har dai ta rasu, na goyo ta ,na dawo gida, aka yi ma ta sutura, wannan ita ce, na wahala da ita, da ba zan manta wa ba.Kuma in ban da mai gida na, babu wanda na taba furta ma sa ga cutar da wannan jaririyar ke fama da shi, har sai da ta yi shekara daya da rabi, san nan ta rasu.

Kin taba samun wadda ta yi sallama da ke ta ce jaririya da aka kawo ma ki lokaci ka za na ta ne?
Lallai na samu, wata yarinya, ta taba zuwa gidanmu, lokacin na fita, na je Unguwa, sai ta yi sallama da miji na, ta ce ma sa, jaririya da aka kawo gidan nan a rana ka za, nawa ne, na zo ne in karbe ta, sai mai gida na ya ce ma ta ba na gida, ta je ta dawo, ko kuma ta jira ni, sai ta ce za ta je ta dawo, da ta tafi, har zuwa wannan rana ba ta dawo ba. Mun kuma sami damar zantawa da Wazirin NDC Alhaji Yusufu, mijin Hajiya Uwa, Uwar Marayu, in da ya shaida ma na cewar, babu shakka, ya na ba matarsa duk tallafin da ya kamata, domin ta sami saukin ayyukan kula da jira –jirai da aka tsinta da ta sa wa gaba. Wazirn NDC ya kara da cewar, yadda ya ke sa ido ga wadannan yara biyar da suke tsakar gidansa, ba ya sa ido ga yaran day haifa, domin ya dauke su a matsayin yaransa day a Haifa, ya ce, yak an so ya gansu sun je kusa da shi, musamman in ya na cin abinci, a wasu lokuta ma tare suke ci da yaran.

Exit mobile version