Connect with us

SIYASA

Tazarce 2019: Tarnaki 10 Da Ke Gaban Gwamnan Bauchi

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar na fuskantar wasu matsalolin da wasu tilin kalubalen da ka iya za masa karfen kafa a zaben 2019 da ke tafe. wadannan matsalolin walau kai tsaye ta rikicin cikin gida ko kuma ta waje ne.

Za mu dan tsakuro wasu kalilan daga cikin tulin kalubalen da ke gaban gwamna M.A. da fari dai kowa ya sani gwamnan Bauchi ya yi takara ne da wasu har ya samu dalewa bisa karamar mulkin jihar a yau, kafin nan ma, ai akwai zaben fid da gwani na jam’iyya, a zaben fid da gwani na jam’iyya APC akwai wasu da M.A ya kayar da su, wadanda kuma suna kule da wannan abun a cikin ransu, a shirye suke su tashi tsaye domin sake neman wannan kujerar a zaben 2019, misali shi ne Dakta Ibrahim Lame tsohon Ministan ‘yan sandan Nijeriya. sun fafata da M.A tun a zaben fidda gwani, M.A ya kada shi, yanzu haka ya fara fitowa yana bayanin cewar an yi masa ba daidai ba; kuma a shirye yake ya sake neman wannan kujerar ta gwamna, a bisa haka yana fito da wadansu kalamai da ke nuni da cewar an ma yi almundahana a zaben fidda gwani. Bayan shi dukka a zaben fidda gwanin, akwai wani Abdullahi Alando wanda shi ma ya fito a APC aka kada shi a zaben fidda gwani, shi kam ma har kotu ya je yana kalubalantar wannan zaben daga bisani kotu ta yi fatali da karar, bayan su ma ai da sauran wadanda ya kada su, kuma da damansu su zama gwamna ne burinsu. Idan gwamnan bai tashi tsaye ba, zai fuskanci matsaloli daga wadanda ya kayar a zaben 2015 domin za su yi kokarin hana shi sakat.

Na biyu: Rikicin cikin gida, tabbas APC a jihar Bauchi tana fuskantar wani irin rikicin cikin gida a tsakanin gwamnan jihar da kuma ‘yan majalisun dattijai ta tarayya da na wakilai, har ma da wasu ‘yan majalisun jiha (amma su kalilan ne), a gefe guda kuma fa, dukkaninsu ‘ya’yan jam’iyya daya ne. tun bayan lokacin da APC ta kafa gwamnati a jihar Bauchi, M.A da ‘yan majalisun tarayya aka fara kai ruwa-rana wadda wannan kacaniyar ta kai har kusan shekaru uku ana fama. Sai dai, a ‘yan kwanakin baya can an fara ganin kamar gwamnan Bauchi da Kakakin Majalisar tarayya wadda ya fito daga mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro suna kokarin sasantawa, dalili kuwa shi ne, an ga gwamnan Bauchi ya je wajen taron taya Kakakin majalisar tarayya murnan zagayowar ranar haihuwa a Abuja, har ma kuma ya zo ya tura wakilinsa a bikin da aka yi a mazabar Dogara. Idan wannan lamarin ya tabbata da dan saukin matsalar da M.A zai fuskanta a tsakaninsa da wadanda suke masu lakabi da (‘yan Abuja), koda fa Dogara ya shirya da M.A amma fa akwai gagarumar matsala a tsakaninsa da sauran ‘yan majlisun irin su Ahmad Yarima, Salisu Zakari Ningi, Halliru Dauda Jiki, a majalisar jihar Bauchi kuma ga irin su Muhammad Aminu Tukur da irin su Maryam Garba Bagel da ke kalubalantar gwamna akan abubuwan da suke gani kuskure ne, kuma dukkaninsu zabbabun shuwagabani ne a halin yanzu kuma a cikin jam’iyya daya. wannan matsalar ta cikin gida, idan ba a shawo kanta ba akwai matsalar da gwamnan Bauchi zai fuskanta a 2019.

Matsalar cikin gidan nan, akwai matsalar da ita kanta APC take fuskanta a tsakanin shuwagabanin jam’iyyar, domin a kwanakin baya wasu bangare sun balle suka ce sun tsige shugaban jam’iyyar APC Uba Ahmad Nana daga shugabancinsa na jam’yyar, wannan yana nuni da cewar ita kanta jam’iyyar akwai wadanda suke bayan gwamna da kuma wadanda sai a slow, amma dai, an jiyo wai suna kokarin sasantawa, domin gwamnati ta sanya kwamitin da zai sulhutansu, koma hakan ta faru, abun da ke a zahirance dai akwai matsala, matsalar da idan ba a samu saukinta ba za ta iya zama wa M.A barazana kasantuwarsa gwamna a karkashin APC, bayan nan, APC a matakan kananan hukumomi su ma dai akwai matsalolin cikin gida, misali yanzu haka shugaban APC na Ganjuwa an tsigeshi, to irin wadannan matsaloli za su iya haifarwa gwamnan rashin samun kuri’u sosai musamman daga yankunan karkara.

Na uku : Zaben cike gurbin shugabanin APC a jihar Bauchi, ai kuwa, wannan lamarin ya sake farraka APC a jihar Bauchi, domin tun lokacin da aka zo domin gudanar da zaben Gundumomi na APC a jihar Bauchi wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka fito karara suka nuna cewar an yi musu rashin adalci, lamarin da a yanzu haka ke nema farraka APC. Bayan da aka yi zaben Gundumomi, ko ma kafin a yi, wasu ‘ya’yan jam’iyyar sun bayyana cewar gwamnati mai ci ta yi iyu-wa-yi-madauki, inda ta saye uwar jam’iyyar a matakin jihar domin musguna wa wadanda take da banbancin fahimtar siyasa ko ra’ayi da su, (dukkaninsu kuma ‘ya’yan jam’iyyar ne). misani, ‘yan tawagar bangaren Kakakin Majalisar tarayya, sun fito fili suka bayyana cewar uwar jam’iyyar ta yi son-kai inda taki saida musu fom din da zai basu zarafin neman sa’a a zaben fidda jagororin APC a Gundumomi 212 na jihar. Lamarin nan ya kawo hayani mai karfin gaske wanda har zuwa yanzu ana nan ana kan tafkawa, domin su bangaren su Aminu Tukur, Kaftin Bala Jibrin, Maryam Bagel da sauransu sun ma yi taron manema labaru suka shaida cewar ba fa za su taba amincewa da wannan kitimurmurar da aka tafka da sunan zabe ba. Sun yi zargin ma cewar ba a yi zaben ba a kowace gudunma a cikin Bauchi, har suka ayyana bin dukkanin matakan da suka dace domin nuna wa uwar jam’iyyar ta kasa cewar an yi musu zalumci, har kawo yanzu a matakin da ake kenan.

Duk a kan wannan, wani abun mamaki, Sani Shehu (Sanin Malam) wanda daga jikin gwamnatin ya fito, domin gabanin ya shigo neman tsayawa takarar shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi shi mai rikon mukamine a gwamnatin M.A hakan ya sanya ya yi murabus domin neman sa’a, amma abun mamaki bayan zaben Gundumomi sai ga shi ya bayyana cewar rashi adalci da aka tafka Allah kadai ya sani. Daga karshe ma dai yanzu haka ya garzaya kotu domin kalubalantar wannan zaben.

Bayan shi fa, Sanata Nazif Gamawa shi ma dan jam’iyyar APC ne, ya yi ta bayanin cewar an kitsa rashin adalci kwarai a zaben Gundumomi, ya kuma shaida cewar babu ma inda aka yi zaben.

Wadannan rikicin ya sake kawo mummunar barakar cikin gida na APC wanda hakan ka iya jawo barazana wa zaman lafiyar APC, idan hakan kuma ta faru, ta ci gaba da rurutuwa tabbas gwamnan jihar mai ci a karkashin APC zai fuskaci tirjiya mai tsananin gaskiya daga ‘ya’yan jam’iyyarsa ta APC.

Na hudu: Matsalarsa da talakawan jihar Bauchi, tabbas ko shakka babu, akwai matsalar rashin da kuma jin dadin walwala hade da rashin samun abubuwan more rayuwa kamar yadda jama’an jihar suka tsammata gabanin hawan gwamnatin, domin kuwa, jama’a da dama a cikin karkara ne ko kuma a birni za ka ji suna kokawa da rashin samun ababen more rayuwa sosai a jihar, da kuma nuna halin ko-in-kula da rayuwarsu, wadannan dalilan sun sanya jama’an jihar suke ganin kamar ba za su sake yarda da gwamnatin ba ganin cewar ba su ji dadi sosai ba a karonta na farko, don haka, koda a yanzu za su ji dadin mulkin za su dauka ana son a sake musu wani abu mai kama da yaudara ne domin a sake samun kuri’unsu a zaben 2019. Irin wadannan matsalolin na rashin samun ababen more rayuwa sosai, ya samu asali ne daga matsatsin rashin babu da gwamnatin ta yi ta kuka a shekarun baya, dakuma matsalar nan ta fadarsa da ‘yan majalisun tarayya wadanda suna da gagarumar rawar takawa wajen ci gaban rayuwar jama’a, fadar da suke yi ta sanyo toshewar wasu ababen ci gaba da dama. ba mu ce, gwamnatin ba ta yi komai ba, illa dai jama’an garin ba su gamsuwa da salon tafiyar, wanda hakan ke iya zama wa gwamnatin Bauchi barazana a zaben 2019 domin jama’a za su iya yin kememe da rukurunsu, domin ko a 2015 jama’a sun bi guguwar daBuhari ya dibo ne suka zabi mafiya yawa daga cikin zabbunmu a yau.

Na biyar: Rashin yin zaben Kananan hukumomi: Gwamnatin Bauchi tun zuwan wannan gwamnatin ta M.A ba a yi zaben shuwagabanin kananan hukumomi ba; wannan dalilin ya sanya ‘yan kananan hukumomi da kuma jama’an karkara suke tsaka da fushin gwamnatin M.A wanda suke cewa akan wannan batun za su nuna amsa kasawarsa ta hanyar kin bashi kuri’u a zaben da ke tafe. Dalili kuwa, kananan hukumomi suna da gagarumar rawar takawa wajen kawo gwamnati, amma ba su samu shuwagabanin da za su jagoranci inganta musu rayuwarsu ba; rashin zaben shuwagabannin ka iya jawo a samu nakasu na sake wa kananan hukumomin hakkokinsu da suka dace gwamnati ta musu, wadannan baraza ne sosai a kan gwamnati mai ci.

Na shida: Gwamnan Bauchi zai fuskacin wata ‘yar matsala daga masu neman tsayawa takarar gwamna a zaben 2019, domin alamu suna nuni da cewar wasu da dama za su fito neman kujerar gwamnan a kuma jam’iyyu mabanbanta, wanda hakan ka iya zama wa gwamna mai ci barazanar samun kuru’u masu tilin yawa. Har kuma, fitowar masu neman kujerar da dama ka iya rage masa masoya ko mabiya musamman ma ‘yan siyasa.

Na Bakwai: Jam’iyyun Adawa da suka kunno kai, la-shakka jam’iyyun adawa, irin su PDP, NNPP da sauran jam’iyyu masu nunfashi za su kawo wa M.A cikas, domin kuwa tuni suka fara tutiya suna masu shelanta cewar gwamnati mai ci ta gaza kasau wajen kawo wa jama’an jihar aiyukan ci gaba da ka iya basu zarafin mallakar zukatan jama’an jihar musamman talakawa. Matsalolin da jam’iyyu za su kawo wa gwamnati mai ci, tabbas sai ya ja damara ya iya ketare adawarsu musamman ganin cewar suna da ababen fada a kan gwamnatin.

Na takwas: Rashin kammala aiyukan da aka faru tun shekaru uku da hawan gwamnan M.A, gwamnatin jihar ta bayar da aiyuka da daman gaske tun a kasafin kudin bara har aka zo ta bana, amma kuma aiyukan da aka tsara za a yi kamar na titina har yanzu sai fama ake yi, wadannan rashin kammala aiyukan da aka faru ka iya zama wa gwamnati mai ci barazana wajen sake samun kuri’un talakawarsa.

Na Tara: Rashin samar da wasu muhimman aiyukan da suka shafi rayuwar talaka kai tsaye, domin talakawa kan yi korafi sosai.

Na Goma: Rashin biyan kudin giratuti na tsoffin ma’aikatan da suka yi hidima wajen ci gaban kasa. Wannan matsalar, zai baiwa ‘yan adawa damar fita fili su kalubalance gwamnatin M.A kan rashin biyan kudin giratuti duk da samu tallafin Bailout da kuma Paris Club daga gwamnatin tarayya.

Nasarorin Da Gwamnan Ya Samu Wadanda Za Su Iya Rage Masa Kalubale:

Biyan Albashi: Gwamna mai ci ya yi kokari sosai wajen tabbatar da cewar a kowace wata yana iya yinsa wajen biyan kudin albashin jihar, wannan ya taimaka masa wajen rage wasu damuwowin, wanda har a kan haka ne shugaban kasa ya yaba masa kan wannan kokarin.

Na biyu: A zaharin gaskiya dole ne kowani mutum ya cire wa gwamnan jihar Bauchi tuta a bangaren inganta ilimi, domin M.A Abubakar ya yi namijin kokari sosai wajen kyautata sha’anin koyo da kuma koyarwa a jiharsa ta Bauchi. idan muka dubi tarihi, gwamnan jihar Bauchi ya zo gwamnatin nan a lokacin da dalibai ‘yan jihar ba su samun wata sakamakon jarabawar mai ma’ana, domin kashi uku 3.5 ne kawai suke cin jarabawa kammala sakandari a gabanin ya amshi mulki, a lokacinda ya samu zarafin hawa mulki a shekara ta 2016 kashi 17.6 suka ci jarabawarsu na WAEC da NECO, haka a 2017 ma adadin ya karu, wannan yana nuni da kokarin gwamnati.

A bangaren inganta ilimi a manyan makarantu kuwa, babu shakka gwamnatin ta yi kokari sosai wajen inganta kwalejin ilimin kimiyya da fasaha mallakinta wato ATAP, domin a halinda ake ciki gwamnati ta gyara makarantar nan fiye da dukkanin tuninin mutum idan aka kwatanta da gwamnatin baya, haka kuma a yanzu haka, gwamnati ta baiwa ‘yan asalin jihar Bauchi damar zuwa domin yin karatu a wasu kwasa-kwasai kyauta a wannan kwalejin, wannan na nuni da cewar gwamnatin ta samu nasara a bangaren ilimi, domin ta samar wa duk mai sha’awar yin karatu hanyoyin da zai bi domin cin gajiyarta. Da ma sauran fannonin ilimi da gwamnatin ta maida hankali a kai.

Na uku: Babin shimfida titina, zan ce an samu nasara na bayar da aiyukan yin titina a fadin jiharBauchi amma fa ba zan ce an yi titina ba; dalili kuwa shi ne yau shekaru uku ana faman yin titinan nan har yau ba kai ga kammala su ba; sai dai idan gwamnati ta gamasu za a samu ci gaban kuma zai zama mata gagarumar nasara, amma wasu an kai ga kammalawa wasu kuma ana kokarin yin hakan, sai dai da yawa daga cikin aiyukan ba ma dauko hanyar kammalawa ba.

Na hudu: Samar da aiyukan yi, babu yabo babu fallasa a nan domin kuwa gwamnati ta tashi tsaye wajen koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai, da kuma samar wa matasa sana’o’i.

Na biyar: Fannin lafiya, gwamnatin Bauchi ta samu nasara a fannin lafiya, domin kuwa hatta a kasafin kudin bara da na bana sa’anin lafiya abu ne mai samun kaso mai tsoka, wanda ta wannan hanyar an yi amfani da wanann damar wajen kyautata lafiyar jama’an jihar.

Na shida: Sashin gona, za a iya cewa da hadin guiwar shirye-shirye gwamnatin tarayya, jihar Bauchita samu nasara musamman wajen baiwa manoma bashin aikin gona. A kwanan ne, aka kaddamar da batun saida wa manoman jihar Bauchi Tiraktoci guda 500, idan hakan suka tabbata suka zo jihar to tabbas hakan zai kawo wa jihar Bauchi ci gaba mai ma’ana a sashin gona da albarkatun kasa.

Na Bakwai: Wanzar da zaman lafiya, gwamna mai ci ya toshe kunnensa ya kuma yi kunnen uwar shegu ga dukkanin masu kawo masa tsegumi da nufin sanya shi ya kawo tashin-tashina ko rudani a jihar. Musamman wajen yin daidaito wajen tafiyar da harkokin mulki ga kiristoci da musulmai, bangarorin addini da sauransu.

Wadannan su ne kadan daga cikin nasarori da kuma kalubalen da suke gaban gwaman jihar Bauchi Muhammad Abudllahi Abubakar a zaben 2019 da ke harararmu.

Tabbas idan gwamnan jihar Bauchi bai yi hankali ba, wadannan kalubalen za su iya za masa mummunar barazana da ka iya hanasa samun nasara a zaben 2019 da ke harararmu.

 
Advertisement

labarai