Ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Sergio Basƙuets yace mai tsaron ragar ƙungiyar Ter Stegen ne ya taimakawa ƙungiyar tasamu nasara a wasan da ƙungiyar ta buga da Athletico Bilbao a ranar asabar wasan da Barcelona ta samu nasara daci 2-0.
Ɗan wasa Leonel Messi da Paulinho ne suka zurawa ƙungiyar ƙwallayenta guda biyu a daidai mintina na 36 da 85 da fara wasan a filin wasa na Sam Mames.
Basƙuets yace mai tsaron ragar ne yabawa Barcelona nasara sakamakon hana ci da ya yi a lokacin da ɗan wasan gaba na Bilbao, Aduriz ya tarfa mai tsaron ragar ana tsaka da wasan kuma ya hana ɗan wasan damar buga ƙwallon cikin ragar.
Sannan mai tsaron ragar ya sake hana wata ƙwallo da aduriz ɗin ya sake sakawa da kai inda Ter Stegen ya dawo da ƙwallon bata shiga raga ba. Basƙuets ya ce, dole muyi farin ciki domin munada babban mai tsaron raga kuma mai taimako saboda wannan nasarar da muka samu a yau shine yabamu domin yahana ƙwallaye biyu shiga ragarsa.