Muhammad Maitela" />

TETFUND Ta Yi Kokari A Ci Gaban Ilimin Yobe Amma Muna Son Kari- Gwamna Buni

Harajin Ilimi

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa hukumar tallafa wa ilimin manyan makarantu ta Nijeriya (TetFund) ta taka muhimmiyar rawa a ci gaban ilimi a jihar Yobe, amma akwai bukatar kara himma a wannan lokacin.

Bugu da kari, Buni ya bayyana cewa a gwamnatin jihar ta bayar da fifiko a matakin farko na ilimi, domin tabbatar da cewa kowane yaro a jihar Yobe ya samu ilimin da ya dace, wanda ya jawo kafa dokar ta baci a harkokin ilimi.

Gwamna Buni ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakoncin tawagar kwamitin amintattu na hukumar TetFund, a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu, a karkashin jagorancin Alhaji Kashim Imam.

Har wala yau kuma, Gwamnan ya yaba kan tallafin da TETFUND ta bai wa manyan makarantu shida a jihar Yobe.

“Mun yi matukar yaba wa kokarin da hukumar TETFUND ta bayar wajen ci gaban ilimi a jihar Yobe, amma kuma duk da hakan muna bukatar karin wasu, musamman makarantunmu irin su Polytechnic Geidam wadda kusan baki daya Boko Haram sun barnata gine-ginenta, wanda mu na iya kokari wajen ganin sake gina makarantar.”

Ta nashi bangaren, shugaban kwamitin amintattu a hukumar TETFUND Alhaji Kashim Imam ya sanar da cewa TEFUND ta kashe naira biliyan 8 a wadannan manyan makarantu a jihar Yobe, wanda hakan kari ne idan an kwatamta da shekarun baya a kudin da suke kashe wa wajen ci gaban ilimi a Yobe.

Alhaji Kashim Imam kuma ya yaba da kokarin Gwamna Mai Mala Buni bisa yadda ya yi namijin kokari wajen ciyar da Yobe gaba a irin wannan mawuyacin hali.

Idan akayi amfani bayanai da fasaha, abin zai yi sauki (tantance tsakanin makiyaya na gari da bata gari). Mu tabbatar an tilastawa dukkan makiyaya samun lambar NIN kamar yadda aka wajabtawa sauran yan kasa,” in ji shi.

“Ta hanyar amfani da fasaha, za ka iya gano bata gari daga cikinsu. Ba dukkan makiyaya bane bata gari, kadan ne daga cikinsu. Tunda dukkansu makiyaya ne, akwai wahalar banbance su.

“Abinda ya fi muhimmanci shi ne karfafawa tattalin arzikin makiyaya Fulani. Suna bukatar tsarin kiwo na zamani, ba mu cika magana kan wannan ba. Kan tsaro kawai muke magana.

“Ba ma magana kan inganta tattalin arzikin rayuwarsu wadda hakan shima ya haifar da kallubalen tsaro.”

Exit mobile version