Connect with us

MANYAN LABARAI

TETFund Za Ta Tallafa Wa Manyan Makarantun Kasar Nan Da Dakunan Kwanan Dalibai

Published

on

Hukumar Gidauniyar tallafawa manyan makarantu (TETFund), ta bayana cewa, za ta samar da fiye da dakuna ga dalibai 200,000 a manyan makarantun kasar nan.

Mista Kashim Ibrahim-Imam, shugaban kwamitin amintattun TETFund ya bayyana haka a taron da kwamitin ya shirya don tattauna yadda za a raba tallafin gudanar da bincike a jami’o’in kasar nan a Abuja.

Ibrahim-Imam ya ce, rashin cikakken dakuna kwana a manyan makarantu kasar nan yana matukar damun hukumar, ta kuma dauki aniyar tabbatar da kai tallafi tare da kawo karshen matsalar a fadin kasar nan.

“Na damu matuka da wadandan bangarorin guda biyu haka kuma lamarun na damun dukkan ‘yan kwamitinmu.

“bangaren kuma sun hada da na kimiyya da fasahar sadarwa da kuma na dakuna kwanan dalibai a manyan makarantunmu, haka kuma mastalar dakunan gudanar da binciken kimiyya da samar da manyan dakunan daukan karatu ga dalibai abu ne da gudauiyar za ta tabbata da ta kawo tallafin ta don kawo karshen matsalar.

“A bangaren samar da dakuna kwana, abu ne a bayyane cewa, ana fama da gaggarumar matsala na dakuna kwana ga dalibai a manyan makarantun kasar nan, musamman ganin yadda yawan dalibai ke kara karuwa a duk shekara.

“Mastalar haka take a dukkan manyan makarantu kasar nan, misali a Jami’ar Abuja ana samun gado 1000 ne ga dalibai 3000, haka abin yake a jami’ar Kalaba.

“A zamanin mulkina zan karfafa wa manyan makarantumu su shiga hadaka da bangaren kamfanoni masu zaman kansu ta yadda za a gina dakuna kwanan dalibai ta haka za a rage matsalar da ake fuskanta,” inji shi.

A nasa jawabin, bababan sakataren gidauniyar, Farfesa Suleiman Bogoro, ya ce, gidauniyar ta samar da cibiyoyin bincike 12 a manyan makarantun kasar nan don karfafa bincike da harkar ilimi.
Advertisement

labarai