Shugaban kwamitin kasa da kasa na shirya gasar Olympic ko IOC a takaice Thomas Bach, ya ce yana da imanin cewa, birnin Beijing zai cimma nasarar shirya gasar Olympic ta lokacin hunturun shekarar 2022 cikin nasara.
Bach ya ce shirye shiryen da birnin ke yi, suna gudana ba tare da wata matsala ba. Ya kuma jinjinawa kasar Sin, bisa kokarinta na fitar da harkokin wasanni, da ita kan ta gasar Olympic daga duhun da annobar COVID-19 ta jefa su. Kaza lika ya godewa shugaban kasar Sin Xi Jinping, bisa irin goyon baya da yake baiwa gasar ta Olympics wadda birnin Beijing ke kimtsawa.
Bach ya kara da cewa, Beijing ya cimma nasarar gudanar da shirye shirye masu kayatarwa, bisa hangen nesa na shugaba Xi, wanda shi ne ya gabatar da kudurin jan hankalin Sinawa miliyan 300 su shiga wasannin hunturu. A daya hannun kuma, Bach ya ja hankalin ’yan wasan motsa jiki na Sin, da su yi amfani da wannan dama ta gasar Olympic na lokacin hunturu da Beijing zai karbi bakunci, wajen karfafa kwarewar su.
Daga nan sai ya bayyana birnin Beijing, a matsayin birnin da zai bude wani sabon shafi a tarihi, na karbar bakuncin gasar Olympic ta lokacin zafi da kuma lokacin hunturu. (Saminu)