Connect with us

RIGAR 'YANCI

Tilas Gwamnati Ta Zage Damtse Domin Kare Rayuka Da Dukiyoyi – Usman Sharif

Published

on

Mun yi farin ciki da samun labarin ganawar da kafafen yada labarai suka ce an yi a tsakanin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno (rty), babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa, wasu shugabannin hukumomin tsaro na kasa da kuma Gwamnonin arewacin kasar nan, inda suka tattauna game da yanda lamarin tsaro ya tabarbare ya ke kuma kara tabarbarewa a wannan yankin namu na arewacin kasar nan, domin lalubo matakin karshe wajen kawo karshen kashe-kashen da wadanda ake kira da ‘yan bindiga dadi ko kuma a wasu wuraren masu tayar da kayar baya su ke ta yi a kan al’umma musamman a wannan yankin namu na arewacin kaar nan.

Wannan bayanin yana fitowa ne daga bakin dan kasuwar nan mai zaman kansa, Alhaji Usman Abubakar Sharif Usmaniyya, a lokacin da ya ke bayyana takaicinsa a bisa tabarbarewar harkokin tsaro a yankin arewacin kasar nan.

Abubakar Sharif ya ci gaba da bayanin cewa, “Duk da cewan kamar yanda shi mai bai wa shugaban kasan shawara a kan harkokin tsaron ya ce ba za su bayyana abubuwan da suka tattauna a wajen taron na su ba dalla-dalla, Sai dai kamar yanda ya ce mutane za su gani a kas ne. To ko ba komai mun ji dadin yanda a wannan karon gwamnatin ta nuna cewa da gaske take yi a wajen kokarin kawo karshen wannan mummunan yanayin.

Lamarin tsaro a sashen arewacin kasar nan ya lalace ta yanda kawo yanzun mu dai ba za mu iya cewa akwai wani ci gaba da aka samu ba wajen magance matsalolin tsaron, domin ko a satin da ya gabata mun sami labari daga kafafen yada labarai na cewa wadannan miyagun ‘yan bindigar sun kai hari a kan wasu kauyaku da ke cikin Jihar Zamfara, inda aka bayar da labarin sun kashe mutane sun kuma sace wasu mutanan masu yawa tare da kore dabbobin mutane da lalata dukiyoyinsu. Duk da cewa mukan sami labari daga hukumomin tsaron na cewa sun kashe da yawan barayin sun kuma lalata maboyarsu, amma mu sam ba mu gani ba a zahiri, ta kafafen yada labarai wadanda kila ma har su nuna mana hotunan gawarwakin na su da kuma na maboyar na su da aka lalata.

Wani babban abin haushi da takaici ma shi ne kamar yanda muka sami labari da kuma abin da muka gani da ido a faya-fayen bidiyo yana yawo kamar dai a Jihar ta Katsina, a wuraren garin Funtuwa, inda su wadannan barayin da ake cewa ‘yan bindiga suka bullo daga hanyar Funtuwa da ta hadu da Birnin Gwari, a kan Babura masu yawa, sannan kuma kowane babur guda yana dauke ne da mutane uku a bisansa, sannan kowane daya daga cikin mahayan nan yana rike da bindigar AK 47 a hannunsa, suka kuma keta ta cikin jama’an nan suka nufi kauyan da suka yi nufin zuwa domin su kai farmaki, suka kuma isa suka aikata duk barnar da suka yi nufin aikatawa babu wani jami’in tsaron da ya kalubalance su. Duk fa da tulin tarin jami’an tsaro kala-kala da ke cikin garin Funtuwa a wancan lokacin, wanda kuma wannan abin ya faru ne da rana kata, kowa yana kallonsu. Baya ga cewa an sanar da duk wanda ya kamata a sanar an ce har zuwa Abuja duk an sanar da magabatan amma babu wanda ya ce masu kanzal suka je suka karkashe mutane suka sace dukiyoyi suka kuma yi awon gaba da wasu mutanan.

A nan muna ganin lallai akwai gyara a wajen bayar da umurnin nan, domin ana cewa tilas ne a bayar da umurnin nan kafin su jami’an tsaron su iya yin wani abu ko da kuwa a kan idonsu ne abin ya ke aukuwa.

Kuma kamar yanda har kullum ake neman al’umma da su bayar da hadin kai wajen bayar da sanarwa a duk lokacin da suka ga wani abu makamancin wannan, to ba wai al’umma ba sa bayar da sanarwar ce ba, amma a lokuta da yawa al’umma suna ganin ko sun bayar da rahotannin babu wani abu ne da ake yi a kai. Sai dai a nan kuma wani wajen da gizo ya ke saka shi ne batun kayan fadan da jami’an tsaron namu su ke amfani da su a wajen tunkarar wadancan makiyan, domin sau tari za ka taras kayan fadan da su ke a hannun abokanan gaban namu watau ‘yan bindigan sun ma fi na jami’an tsaron namu inganci da nagarta, wanda hakan ke nuna cewa tilas ne fa gwamnati ta tashi tsaye ta kara zage damtse domin ta tsayu da hakkin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Duk da hakan dai, muna yin kira ga jama’a da su ci gaba da hakuri da kuma dagewa wajen taimaka wa jami’an tsaro din da bayanai na sirri. Sai dai a nan shawarar da za mu kara bayarwa ita ce in an tashi bayar da rahotannin a sami manyan jami’an tsaro din ne ba ‘yan kananan su ba domin gujewa fadawa tarkon baragurbi.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: